Connect with us

LABARAI

Dalibai 197,050 Ne Suka Rasa Gurbin Karatu A Jami’o’i Bakwai Na Nijeriya

Published

on


Duk da fadin da ake yi na wahalar da ke tattare da samun damar shiga manyan makarantun kasarnan, binciken Jaridar Guardian ya bankado wasu bayanai wadanda suka yi hannun riga da sanarwar da hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun JAMB ta bayar, wanda ke nuni da cewa kashi 75 na daliban da suka cancanci shiga manyan makarantun sun sami guraben karatu a wannan shekarar ta 2017/2018.

Binciken jaridar ya nakalto cewa bakwai kadai daga cikin manyan makarantun sun nuna cewa, dalibai 46, 950, watau kimanin kashi 20 cikin dari suka sami shiga manyan makarantun, daga cikin jimillan dalibai, 244, 000, da suka sami nasarar cinye jarabawar shiga manyan makarantun da hukumar shirya jarabawar ta (POST-UTME), ta shirya.

Sakamakon binciken na majiyar tamu ya nuna, daga cikin dalibai 104,000, da suka cancanci shiga jami’ar Ilorin, dalibai 11,000ne kadai suka sami shiga jami’ar. Ita kuwa Jami’ar Ibadan, dalibai 27,000,ne suka sami cin jarabawar shiga cikinta, amma daibai 3,750, kacal Jami’ar ta dauka daga cikinsu. Daga cikin dalibai 20,000, da suka sami nasarar cinye jarabawar hukumar domin shiga Jami’ar Jihar Lagos, dalibai 4,000,ne kacal Jami’ar ta dauka. Ita ma Jami’ar Ambrose Alli, da ke Ikpoma ta Jihar Ido, dalibai 8000 ne kawai ta yi kokarin dauka daga cikin 15,000 da suka sami nasarar cin jarabawar shiga cikinta. Hakanan, Jami’ar Benin, ta dauki dalibai 10,000 ne daga cikin 21,000 da suka sami nasarar cinye jarabawar shiga Jami’ar. Jami’ar Fatakwal, ta dauki dalibai 6,700 ne daga cikin daliban da suka cancanci shiga cikin na ta su 37,000. Jami’ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin Tarayya da ke Akure, Jihar Ondo,  ta iya samar da guraban dalibai, 3,500, ne kacal daga cikin 20,000 da suke da hakkin shiga cikinta.

Da yake amsa tambaya a kan dalilin hakan, jami’in hulda da jama’a na hukumar shirya jarabawar, Dakta Fabian Benjamin, cewa ya yi,yawancin makarantun da ba su yi aiki da sunayen da hukumar ta aike masu da su ba,suna da wasu matsaloli ne, wasu har ya zuwa yanzun ba su gama cika sharuddan da hukumar ta gindaya masu ne ba, wasu kuwa sabbi ne don haka tilas ne su yi takatsantsan wajen daukan daliban.

To amma, ko me zai kasance da dubun-dubatan daliban da ba su sami guraban daukan na su ba, duk da cancantarsu? Fabian Benjamin, cewa ya yi, “Hukumarmu ba ta da izinin cewa ga abin da zai faru da su, sai dai hakkin su daliban ne su nemi a dauke su a cikin jami’’o’in da kuma manyan makarantun, mu namu sanya ido ne mu ga cewan an dauke su kawai.”

Dangane da kiran da iyaye da dalibai ke yi na a tsawaita lokutan da sakamakon jarabawar na UTME, zai yi aiki zuwa shekaru uku, kamar yadda ‘yan Majalisun tarayya ke bayar da shawara. Sai jami’in ya ce, wannan ba shi ne matsalar ba. Rashin samun damar daliban na shiga manyan makarantun ya dogara ne ga irin zabin da suka yi. Muna kuma yin kokarin magance hakan.

Dangane da wannan matsala ta daukan daliban, wasu manyan makarantun suna baiwa gwamnatin Tarayya shawarar ta kara mayar da hankali a wannan sashen na ilimi mai zurfi, ta hanyan yin kari a kan daukan nauyin sashen, da suka hada da rashin cikakkun kayan aikin koyarwar, karancin Malamai, karancin su kansu Jami’o’in, da makamantan hakan.

A ta bakin jami’in hulda da jama’a na Jami’ar Fatakwal, Williams Wodi, a maimakon gwamnatin Tarayya ta kara gina wasu sabbin jami’o’in,kamata ya yi ta fadada na yanzun da kayan aiki, ta yadda za su iya biyan bukatun daliban. Wodi, ya ce, daga cikin dalibai milyan 1.7, da suka rubuta jarabawar shiga jami’o’in, gabakidayan jami’o’in kasarnan, ba za su iya daukan abin da ya wuce dalibai 570,000, ba. Wanda hakan matsala ce babba, a hakan ma ayyuka sun yi wa malaman yawa, hukumar kula da jami’o’in kuma ta NUC, ta bayar da sanarwar, a yanzun haka an bukatar manyan malamai masu shaidar digirin digirgir, har dubu 32,000, wadanda za su koyar a cikin jami’o’in kasarnan,matukar ana son komai ya ta fi daidai, sai ya kare da tambayar, a ina za mu samo su?

Ayyukan Da Ganduje Ke Yi Na Da Alaka Da Nasarar Da Aka Samu A Zaben Kananan Hukumomi —Garo

An Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da cewa ya yi rawar gani wajen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano.Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo ya bayyana hakan.

Yayi nunu da cewa duba da yanda a wasu jahohin anma shafe shekaru shida wasu 9 ba a gudanarda zaben kananan hukumomi ba, amma anan kano wa’adin zababbun daya kare ba a dauki wani tsawon lokaci ba, aka sanya ranar zabe akayi, duk kuwa da yanayi na karancin kudi da ake fama dashi a kasarnan.

Ya ce “Mun godewa Allah da al’ummar jihar Kano suka fito suka kada kuri’arsu akayi zaben.Cikin kwanciyar hankali da lumana ba tareda wata matsala ba”

Alhaji Mutala Sule Garo ya ce zabe ya tafi daidai  duk da cewa an dan sami tsaiko na raba kayan zabe sakamakon sunzo hukumar zabe a makare, ba a gudanarda zaben a lokacin da ake bukata ba, amma  isowar kayan aka raba a kananan hukumomi 44 jama’a sun tsaya sun yi zabe.

Ya yi kira da cewa a ci gaba da baiwa Gwamnatin Kano goyon baya, zabe ya nuna jama’a sun zabi abinda zai taimakesu, sunji dadin yanda jama’a suka fito sukayi zaben nan, ayyukanda

Gwamnatin Kano take yanada alaka da nasarar da sukayi a zaben da ba a taba ganin irinsa ba wajen nagarta.

Alhaji Murtala Sule Garo yayi kira a wadanda ba su yi nasara ba su zo a hada kai da su domin ci gaban jihar Kano domin idan akayi zabe an gama maganar banbancin jam’iyya al’ummar Kano gaba daya za a sa a gaba dan dorawa akan ayyukan alkhairi da Gwamna Ganduje yake aiwatarwa.

Kwamishinan na kananan hukumomin Alhaji Murtala Sule Garo yayi kira ga dukkan zababbun shugabaninn kananan hukumomin su bada hadin kai ga gwamnati wajen aiwatarda ayyuka tukuru domin bada gudummuwansu ga ci gaban al’ummar jihar Kano.


Advertisement
Click to comment

labarai