Connect with us

LABARAI

Ba Mu Amince Da Siyasar Ubangida Ba A ADP –Kwamba

Published

on


An bayyana cewar jam’iyyar ADP ta ware kashi Ashirin da biyar na rabon mukamai ga kowanne jinsin mata da matasa, domin dukkanin bangarorin na da rawar takawa a siyasance. Shugaban jam’iyyar ADP ta kasa reshen jihar Neja, Kwamared Tanimu Sarki Kwamba ne ya bayyana haka a wani kwarya-kwaryar taro da kungiyar ta shirya laraban makon da ya gabata.

Kwamared Tanimu ya cigaba da cewar hatta masu nakasa ADP ba ta bar su a baya ba, domin su ma an ba su damar yin takara a dukkanin mukaman jam’iyya da ma wani matsayi da suke bukatar nema. Dan haka mun shirya karban dukkanin mukaman siyasa a jihar nan, amma hakan fa ba ta sabuwa sai an dunku mazabu, domin siyasa na mazaba, mu a jam’iyyar mu ba mu da ubangida dan haka da zaran kana da katin zama da jam’iyya kai ma wani abu ne a jam’iyya dan kana da rawar takawa.

Yace a salon siyasar da ADP ta zo da shi, muna da kwamitoci da duk wani abu ya taso suke da alhakin zama dan dubawa, dan haka mu a tsarin jam’iyyar mu ba a kai jam’iyya kotu duk abinda ya taso a cikin gida ake dunke shi, a tsarin mu ba wanda zai kai jam’iyya kotu kan wani rashin fahimta duk abinda ya taso a cikin gida ake dunke shi, kai jam’iyya kotu tamkar mutum ya bar jam’iyya ne.

Muna da kwamitin amintattun jam’iyya BOT wanda a kowanne lokaci suna zama dan tattauna matsalolin da ke tasowa cikin gida domin dunke su, duk jam’iyyar da BOT dinta bai da lokacin zama ko kuma ba a kiran zama wannan ya tashi daga jam’iyyar siyasa zuwa kungiya. ‘Yan kwamitin amintattau na jam’iyya suke zama suna tattauna matsalolin jam’iyya da duk wasu matsaloli da ke tasowa dan samar masu mafita.

Tanimu Sarki Kwamba ya jawo hankalin ‘yayan jam’iyya da cewar duk wani mai bukatar wani a siyasance indai a ADP ne to ya tabbatar ya faro da mazabarsa, domin shugabannin mazabu suke da muhimmanci akan kowa, mun shirya dan ganin an yi siyasa ta gaskiya, kan haka yasa mu ke cewa duk wani dan siyasa da ya gamsu da akidun ADP to kofa a bude ta ke.

Taron dai ya samu halartar Hon. Haruna Usman mataimakin sakataren jam’iyyar ta kasa, sai Hon. Yusuf Kure tsohon shugaban jam’iyyar na riko, da mataimakin shugaban jam’iyyar na ‘ B’ Zone, Hon. Bashir Muhammed Abacha.

Jam’iyyar dai yanzu haka ta ba za komarta wajen farauto ‘yayan jam’iyyar PDP mai adawa da kuma wasu daga cikin ‘yayan APC mai mulki da suke ganin ba su aminta da yadda ake shugabanci a jihar ba.


Advertisement
Click to comment

labarai