Connect with us

SIYASA

Wasu Matasan ‘Yan Abi Yarima Asha Kida Ne Ba Su San Meye Siyasar Ba — Sadiya Kaduna

Published

on


Tare da Fadila H. Aliyu Kurfi[email protected] tweeter @FadilaKurfi

Shirin rigar “RIGAR ‘YANCI” shiri ne na matasa da yake tattaunawa da jajirtattun matasa akan rayuwarsu da mahangarsu kan siyasa, wane tagomashi matasan zasu samu idan sun dafa ma gwamnati ta hau? Wasu matasa yayin zabe sukan jikkata kawunansu da ‘yan uwansu wasu su rasa rayukansu, to me za su amfana da shi a siyasar  kasancewarsu wanda suka zabure suka hada karfi da karfe don ganin sun dora shuwagabanni kan madafun iko da suke akai.

Hajiya Sadiya Kaduna fitarciyar macece ‘yar kasuwa, sannan kuma marubuciya, wacce ta yi gwagwarmayar kungiyoyin mata marubuta, macece wacce take matukar kishin kasarta da jaharta, duk wani abu na cigaban kasa da matasa tana cikinsa, macece tamkar maza, tana sana’onta bayan rubutu, duk wanda ke harkar soshiyar midiya ta fesbok ina jin yasan da zamanta saboda irin guddumawar da take bayarwa da ilmantar mata.

Barka da zuwa wannan shafi namu na Rigar ‘Yanci Hajiya Sadiya Kaduna.

Yauwa barkanmu dai Haj Fadila

Ko za mu iya jin dan takaitaccen tarihinki?

Farko dai suna na Sadiya Muhammad Abdullahi wacce aka fi sani da Aunty Sadiya Kaduna an haifeni a Tudun Wadan Kaduna na yi karatun makarantar primary school dina a Bantic dake Tudun Wadan Inda na yi secondary a memuna Gwarzo bayan nayi aure na koma Islamic section na yi Sanawiyya a Salamatu institute dake unguwar Ma’azu Kaduna,  nan na yi diploma a bangaren Arabic Alhamdulillahi yanzu ina da aure da yara bakwai masha Allahu.

 

Me ye asalin fara rubuce-rubucenki? Sai kuma zuwa yanzu littafi nawa ki ka rubuta?

Asalin fara rubutu na ada shine, “ ina sha’awar inga ina rubutunne kawai ba don isar da wani sako ba, ban sani ba ko don ni ma a kirani marubuciyar ne oho, sai kuma daga baya ya koma kishin adabi na fara rubutun littafi na farko ne a shekarar 2007 inda na fara da Auran kaddara. Zuwa yanzu littafi nawa sun kai adadin goma shir.Na rubuta littafai guda goma cikinsu sun hada da, Auran Kaddara, Alwashi, Ummu Sulaim, Marainiya, Mufarka Mata, Lobers Delight, Ukuba, Waye Musabbabi, Kula da kaya, Azal. Dukkansu babu wanda bai samu karbuwa ba.

 

Wane hasashe za ki yi game da siyasar Nigeriya da makomarta a na ki ra’ayin?

Alhamdulillahi abin da zance game da siyasarmu ayau shine, “dai dai gwargwardo zan iya cewa siyasa ta yi lafiya sosai a mahangata don gaskiya gara yau da jiya don mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali fiye da baya, an kuma samu cigaba sosai kuma alal hakika aganina a yanzu mun sa mu canji a mahangata mulkin Shugaba Buhari wata babbar ni’imace a gare mu musamman mu ‘yan arewa, amma har yanzu wasu daga cikinmu basu gane ba kuma ba za su gane ba saboda basa son su gane saboda wani ra’ayinsu na daban ina ganin ba za su gane hakanba sai sun sake kuskuren zaben tumun dare sannanne za su gane wautar da suka yi.

 

Meye makomar matasa a mahangarki game da siyasar ta kasar Nigeriya?

Mahanga ta game da matasa shine, “ wasu daga cikinsu suna kokarin yin siyasarsu da tsafta,  wasu kuwa kwamacala suke yi basu san ma mecece siyar ba, kawai yinta suke yi sun zama ‘yan abi yarima asha kida ne. Su gyara siyasarsu don su kasance cikin matasa na gari wadanda su ma nan gaba za ayi alfahari da su irinsu Gamji Dan kwarai kuma su ma za su fi jin dadin rayuwarsu ba hargowa.

 

Shin ko manyan kasar nan masu fada aji na wani yunkuri domin tallafa ma matasan meye makomar mata a siyasar?

Suna yi kam sosai sai dai kinsan ance in danbu yayi yawa baya jin mai, zan yi misali da inda nake gwamnan mu da sauran na kasa da shi suna matukar kokari wajen ganin sun sama ma matasa aikin yi tare da ba al’umma ingantaccen ilimi wanda za ayi alfahari da su nan gaba  kuma suna iyayinsu na ganin sun kasance masu tarbiyya yadda baza ayi kuka da su ba  wajen bangar siyasa, haka matan ma suna bada muhimmiyar gudunmawa asiyasar saboda sune iyayen al’umma su ma gwamnati batabarsu abaya ba tana goyon bayan duk wani shiri da suke yi na kawo cigaba.

 

Wacce gudummuwa matasa za su iya bayarwa wajen cigaban siyasa ko dimukradiyyar kanta idan an ba su dama?

Tabbas matasa su kuwa ke da gudunmawar da za su bada don saboda kwanyarsu na ja  ya kamata adinga sako su a cikin siyasa  don asamu sabbin cigaba, idan ana tafiya da su tamkar ana kara koya masu ne fa ta yanda idan manyan sun kauce sai su matasan su dauka daga ina manyan suka ajijye, mayar da matasa baya gaskiya ba karamin dankwafar da kasar nan gaba daya bane, a tasa matasa gaba domin cimma nasara, manyan nan ya kamata ku dan huta tunda kun yi mun gani ku samo masu kwazo ku tasa su gaba ku koya masu.

 

Kasancewar mata su ne koma baya a harkar siyasa, wace irin rawa kike ganin mata za su taka wurin kawo saukin rayuwa da ci gabanta idan an ba su dama?

Mata a siyasa suna da mahimmaci kasancewar sunfi kowa kusa da al’umma, misali za ku ga mace dubu in aka ce a taro mata baki ga namiji dari ba, in aka ce a taro maza dubu don haka ya kamata su shigo su ma a dama da su sai kana ciki kake da korafi aji, in ko baka ciki koka yi korafi ba mai ji su kuma ‘yan siyasa ya kamata su janyomu don muna da gudummawar da za mu ba da muma musanman mu marubuta wadanda muke isar da sako lungu da sako a saukake a cikin nuni cikin nishadi kuma sakon ya isa har ya yi amfani kuma muna alfahari da hakan.

 

Me sa matan Hausawa ke yin baya a lamarin siyasa, masu aure da mararsa auren?

Bakomai ke sa mata suke ja baya ba gaba daya illa mazan da suke nuna son kansu su komai sune sun kanainaye komai gani suke yi su kadai ne suka iya kuma su za su yi wanda wannan babban kuskure ne don sai angwada akan san na kwarai da jarabawa jirgi ya tashi sama, kuma harda laifin jami’armu idan mace ta yunkuro zata yi wani yunkuri sai a rika kallonta marar kamun kai wanda sam hakan bai dace ba.

 

Zabe ya kusa gabatowa, kowa yasan yanda matasa ke daukar abin da zafi, wace shawara za ki ba matasan?

To! lallai kam zabe ya matso Allah yasa mu ga lokacin lafiya, shawarta ga kowa ba ma matasa kadai ba kowa mu yi karatun tanatsu musan me mu ke yi mu yi tunanin me zai je ya dawo mu yi siyasa mai tsafta wacce zata kai mu tudun muntsira wacce za mu yi alfahari da ita.  Alhamdulillahi ina ma al’ummar kasata fatan alkhairi, ina gaida masoyana ako ina suke ina alfahari da su. Bissalam.

 


Advertisement
Click to comment

labarai