Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Sajen Lado’  

Published

on


Suna: Sajen lado

Tsara labari: Abdulyasar Aminu Abubakar

Furodusa: Aminu kileba baba sharu

Bada umarni: Yahaya Sa’eed

Kamfani: Ajipapa Film Production

Jarumai: Rabi’u Rikadawa, Baba Labaran, M. Inuwa, Alasan Kwalli, Shu’aibu Idris Lilisko, Fati Shu’uma, Jamila I Tahir, Abdullahi Ajipapa, Fa’iza Jibrin, Alh. Garba Dansanda.

 

A farkon labarin an nuna Lado (Rabi’u Rikadawa) a fadar garinsu suna tare da Maigari da sauran mutanan fada Maigari yana fadamusu an aiko daga birni cewar a bada mutum guda daya wanda ya yi karatu za’a bashi takardar aikin dansanda maigari ya zabi wani matashi acikin mutanan fadar akan shi ya je domin shine ya yi boko a lokacin Lado ya yi caraf yace shi ne zai je domin yana son aikin duk da bai yi boko ba maigari ya amince aka tura shi birnin domin ya yi aikin, Lado yana zuwa birni ya fara saba dokar asalin aikin dansanda saboda rashin karatu da ya yi ya sami wani dansanda mai irin halinsa cin hanci da rashawa suka dinga yi tare har mutane suke tare wa a hanya suna cajarsu kudi babu ji babu ga ba tare da laifin komai ba. har wataran asirinsu ya tonu D.P.O ya gane halin da ake ciki ya hadasu yaba su takardar sallamarsu daga aiki ya koresu Lado ya dawo kauyensu amma bai sanar musu da abinda ya faru a birni ba, sai ya yi amfani da uniform dinsa na Dansanda har ya bude dakin da yake kama mai laifi ya din ga yiwa mutanan garin sojan gona ya dinga horar da mutanan garin duk abinda mutum ya yi komai kankantar laifi sai ya ci tararsa ko kuma ya kama shi ya garkame ya sami dama daga gurin maigari saboda karyace-karyacen da ya ke yi musu maigari har ya amice masa.

A gefe guda kuma akwai wata budurwar dan maigari Maryam(Fati Shu’uma) wadda Lado ya matsantawa cewar yana son ta ita kuma tana ta yi masa wayo domin bata sonsa kwata-kwata ita dan maigari take so kuma ko’a gidansu mahaifiyarta bata goyon bayan ta yi soyyaya da Lado domin duk sun fara fahimtar halinsa, kawayen Maryam ma basa son tarayyarta da Lado hakan tasa wataran sun tare da ita suna bata shawara akan tara bu da Lado yaron Lado ya ji su ya je ya sanarwa da Lado shi kuma ya tura har gidansu kawayen aka taho da su ya garkame a dakin da ya ke ajiye masu laifi idan ya kamo har sai da ta kai Maryam ta daga wa Lado hankali sannan ya yarda ya sakarmata kawayenta sannan a karshe ta yi fushin zuciya ta rabu da shi ta cigaba da soyyayarta da tsohon saurayinta dan maigari.

A karshe lado acikin mutanan da ya ke kawowa ya garkame har ta kai ya saka an dakko masa wani matashi a garin horo da duka da suka hadu shi da yaransa suna yi wa wannan matashi har ta kai ga ya rasa ransa wannan abun ne ya fara daga hankalin mutanan gari harta kai asirin Lado ya tonu a garin kowa ya ji, a lokacin Maigari ya aika birni ‘yan sanda suka zo suka cafke Lado da yaransa a lokacin da ya ke yunkurin zuwa ya jefar da gawar matashin da suka kashe.

 

Abubuwan Birgewa:

1- Kyamarar daukar hoto ta fita a fim din babu laifi.

2- Jaruman sun yi kokari wurin isar da sakon.

3- An nuna illar aikata sojan gona

 

Kurakurai:

1- Wanda a ka nuna a matsayin iyayen Lado kwata-kwata sun yi kankanta domin saura kadan su yi sa’aninsa ma.

2- Sautin fim din bai fita yanda ya kamata ba don wasu hotunan ma muryoyin jaruman tana gocewa ana fara jin maganarsu kafin aga sun yi abun a aikace.

3- Shin tabargazar da Lado yadin ga yi a garin har ta kai ya bude dakin da ya ke saka masu laifi duk garin arasa wanda zai yi kararsa gurin hukuma? ko kuma duk garin ba su da ilimi na boko?

4- ‘Yan matan da Lado ya saka aka dakko ya kulle shin basu da iyayene domin mai kallo ya ga babu wadda mahaifanta suka bi bayanta.

5- Mahaifin Lado wana irin mahaifine da yake biye masa yake aikata shirme tunda ba’a nuna galgalma bane a fim din

6- Da wacce takarda Lado ya sami aikin dan sanda tunda ba’a nuna ya yi boko ba? kawai mai kallo ya ga yafara aiki.

7- Mahaifiyar Maryam ta yi kankanta ace ta fito a matsayin ita ta haife ta domin a gaske bai ci a ce ta haifi wannan ba.

8- A ina Lado ya sami mashin aka ganshi yazo gidansu Maryam zance tunda a farkon fim din ba’a nuna yana da mashin ba kuma a gurin aikinsa duka duka bai yi dadewarda har za’ace ya mallaki wannan babban mashin din ba.

9- A yanda aka nuna yanayin garinsu Lado ba kauye ba ne na kayau shin wana irin maigarine da har Lado zai din ga zuwa fadarsa yana zumbuda wannan karyace karyacen da shirmen amma kuma bai dauki wani mataki ba har sai da ta kai Lado ya yi kisa.

 

Karkarewa:

Akwai sako a fim din amma labarin ya yi kashi – kashi bai tafi kai tsaye ba sannan labarine na barkwanci amma wasu abubuwan da Jaruman suka din ga yi a maimakon ya bada dariya sai ya dinga bada haushi. Wallahu a’alamu!

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai