Connect with us

BIDIYO

Yadda Gobara Ta Lashe Gidan Jarumi Tijjani Asase

Published

on


…Kungiyar Jarumai Mata Ta Nuna Alhininta

Shahararen jarumin nan na fina-finan Hausa, Tijanni Asase ya hadu da iftila’in gobara inda wuta ta cinye gidansa kurmus.

Bincikenmu ya nunar da cewa babu abin da maigidan da iyalansa suka tsira da shi, komai ya kone kurmus! amma Allah ya sa iyalinsa sun tsira da ransu, wato matarsa da ya’yansa uku.

Shafin Taurarin Nishadi ya tuntubi Jarumin don jin abin da ya haddasa gobarar, ga kuma abin da ya fada:

“Ranar Asabar da misalin karfe 2 na dare, matata tana kwance suna barci sai aka kawo wuta, sai gun canjin wuta ya kama sai dakinta ya fara kamawa da wuta, daga nan dakin yara shi ma ya kama da wuta duk suna barci. Sai da dakina ya kama ta saman silin zafi ya farka da matar gidan, sai ta rude ta tashi yara ta bude kofar waje ta dakina suna budewa talabijin ta fashe suka firgita suka yi waje ba kaya ajikinsu sai a makota aka basu”.

Jarumi Asase, ya cigaba da cewa a lokacin da gobarar ta tashi ba ya nan, ya kuma bayyana wurin da yake, inda ya ce “ni kuma muna gun aiki sai da safe aka gaya min na zo. Amma har na zo wutar ba ta gama ci ba, babu abin da muka mora a gidan da ni da matata da yarana guda uku, Fatima Zainab da Hafsatu”, a ta bakinsa.

Domin nuna alhini da kuma jaje ga jarumin, a ranar Talatar da ta gabata ‘yan fim mata a karkashin Kungiyar Jarumai Mata na Arewa (Northern Nigeria Female Actresses) sun ziyarci gidan da al’amarin ya faru inda suka jajanta masa da kan wanan abin alhini da ya sameshi.

Cikin wadanda suka sami halarta har da mataimakiyar shugabar kungiyar, Halisa Muhammad, da sakatariyar tsare-tsare, Mansurah Isah, da sakatariyar kudi, Sadiya Gyale. Sauran sun hada da sakatariyar kungiyar Sakna Gadaz, da sauran wasu da ba sa garin Kano, irin su shugabar kungiyar, Wasila Ismail da mataimakiyarta ta biyu, wato Rahma Hassan duk sun yi masu jaje da addu’ar Allah yak are nagaba, ya mayar da fiye da abin da aka rasa.

Har ila yau, mambobi da dama na kungiyar da dama, su ma ba a bar su a baya ba inda suka taru suka yi masa addu’a a gidan da ya konen inda suka roki Allah ya mayar masa da dubunsu.

Jarumin ya nuna jindadinsa tare da godiya ga ‘ya’yan kungiyar jaruman ta hanyar fadin, “Na gode sosai, Allah ya bar zumunci”.

Jarumai da dama maza da mata abokan sana’arsa na cigaba da yi masa jaje ta fuskoki daban-daban, wasu a gida, wasu ta waya, wasu kuma ta hanyoyin sadarwa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai