Connect with us

TATTAUNAWA

Za A Samar Da Sabuwar Kungiyar ‘Yan Fansho Da Za Ta Hada Ma’aikatu

Published

on


A tattaunawarsu da Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki shugaban kungiyar ‘yan fansho ta jami’o’in Nijerya Dakta Ayuba Audu Kura Ya tabo batun gwagwarmayar da suka yi kafin kafuwar wannan kungiya, da kuma taimakon da kungiyar ke yi ga mambobinta. Sannan ya yi albishir da cewa za su kafa wata sabuwar kungiyar ‘yan fansho da za ta hada ma’aikatu masu yawa:

Masu karatunmu za su so su ji tare da wa muke?

Kuna tare da Dakta Ayuba Audu Kura, shugaban ‘yan fansho na jami’o’in NijEriya.

 

Me za ka bayyanawa jama’a dangane da yadda kungiyar ‘yan fansho take da matsayinta a yanzu a Nijeriya?

To, Alhamdu lillahi, kungiyarmu ta ‘yan fansho wato Federal Unibersity Pension Association a takaice FUFA, sai mu ce mun ci nasara, domin abin da ya sa na ce mun ci nasara, mun samu hamayya daga wasu kungiyoyi na ‘yan fenso na Nijeriya, wanda ma ba na Unibersity ba, wadanda suka kai mu kotu suke zargin mu. suke mana karya, kuma har da cewa kada gwamnati ta bar mu mu tsaya da kafarmu, muka yi iya kokarinmu muka yi rijista, bayan mun yi rijista, a ciki aka je aka hure wa wasu kunne, aka ce kar su yarda a ce har yanzu mu ne muke lura da Unibersity.

Amma duk wannan abubuwan da suke yi, yanzu wajen shekara takwas, amma ba a kai mu kasa ba, an buga nan, an buga can, ba inda aka kai mu kasa. An yi mana karya, aka kai mu wajen EFCC har sau uku cewa kungiyarmu ta barayi ce, mun ci kudi mun ci mene ne saboda haka bai kamata a bar mu muna lura da Unibersity ba, suka yi iya bincikensu ba su ganmu da komai ba, aka zo wajen State SSS duk aka yi wadannan, kai har ta kai taimakon da mu muka yi musu, muka yi ruwa muka yi tsaki muka nemi bashin miliyoyi wajen bankuna saboda a taimaki ‘yan fansho kuma an yarda an taimake mu, a lokacin nan Ahmadu Bello ta yarda tana tsaya mana, amma duk da haka a cikinmu wasu suka karbi bashi din amma ‘yan hamayya komai suka fada wa ma’aikatar tsaro cewa karya muke yi, kudin da muka karba ba wai an karbo su da sunan wasu ba, a’a sunan ‘yan kungiyar ne, saboda haka kudin da muka karbo da aka biya ai ba a sa kudi cikin aljihun banki da muka karbi bashi.

Amma aljihunmu muke sa wa, aka koma ribar da aka sa ma ya yi yawa, haka abubuwa masu yawa amma da yardar Allah mun gama, kwanan nan muka gama biyan bashi na karshe, wanda ni na rantse musu ba zan sake yi ba, to amma Allah na tuba, wannan bashin da muke karba ba wai ina karba don kai na ba ne, ina karba ne don in taimaki ‘yan fansho, ‘yan fenshon yanzu ba dukkan mu ba ne za mu iya zuwa banki a ba mu bashi ba, sai an kankare da wasu abubuwa.

To wasu in ba don bashin nan da kungiyar ta tsaya musu ba, wani bashi da lafiya, wani gidansa ya rushe, wani yana son ya gyara motarsa da duk wasu abubuwa na rayuwa. Kamar yadda ake ba wasu bashi to ana cewa kada a ba fenshon bashi domin ransa ya kusa tafiya, to mu kuwa muka ce a’a mutuwa a ina? Bayan wannan, wannan bashin da zai dauka na daya ban ce ‘yan uwansa su tsaya mai ba, ba mu ce Unibersity su tsaya mai ba, dan kudin din da ake cire mini naira dari, naira ishirin, naira talatin, in wata ya yi an kawo kudin nan sai mu tambayi banki cikin mu wanene bai biya ba?

Kodayake ita gwamnati take biya amma wani yakan mutu, to ka ga wadanda suka mutu din nan wallahi a cikin kudin muke biya. In ka ga abin da muka biya a kan wasu ‘yan fansho da suka rasu za ka yi mamaki, taimakonsu kawai mu ke yi, bashin da muka dauka 2016 da 2015 ya kamata mu gama shi 2017 a farkon watan Janairu, amma saboda rikicin mutanen mu su je nan bashin nan aka yi ta dadewa har wata tara, to interest din fa wa zai biya? Amma dai haka muka yi hakuri, mun gama biyan bashin nan December 2017, ni yanzu  ‘I am a free man’ ba zan sake daukar bashin ba, amma in ya zama dole zan sake, saboda haka mun samu ci gaba,

 

Bayan wannan gwagwarmaya da aka yi, mene ne ya biyo baya?

Bayan wannan ariyas da muke bi na 33% to an biya mu na wata goma sha biyu shekarun baya, karshen wannan shekarar kuma an biya mu na wata shida, to muna fata sabuwar shekarar nan da muka shiga mai yiwuwa a ba mu duka, a ba mu a bin da muka ga ya kamata,

 

Ya ya  dangantakarku take da sauran kungiyoyin ‘yan fansho wadanda ba na jami’a ba?

Muna da kyakkyawar dangantaka, a halinzu ma zan yi wani albishir na cewa, muna cikin tafiyar nan akwai kungiyoyi da yawa na ‘yan fanshona sai muka lura cewa akwai wasu ma’aikatu wandanda kusan tafiyarsu daya ne saboda haka sai muka ce me zai sa ba za mu hada ba? Da Unibersity da Research da Federal College of Education da Teaching Hospital da Institute kamar Port Authority su Abiation da sauransu, ana kiranmu parastatal, to ita parastatal tana da ‘yan nata matsalolin da suka samu, yadda za mu yi aikinmu ya bambanta da na wasu, tsarin albashin ya bambanta da na wasu, condition na serbice na mu ya bambanta da na wasu, sai muka ce to mu tunda parastatal ne bari mu hada kanmu, to in fact sun ji dadin abindda Unibersity ta yi musu sai suka ce su suna son su shiga, sai muka ce to mun yarda za ku shiga amma ya kamata mu hada wata kungiya wadda za ta rike kowa kuma muka gayawa federal gobernment ga yadda muke so ba zai zama da matsala ba, to yanzu mun yi nisa kuma ba zan gaya maka sunan ba amma nan ba da dadewa ba kafin wannan watan ya kare ko February za ka ji mun yi taro, mun ba ta wani suna, to idan har muka ba ta suna muka fara aiki to Nigerian Unibersity Pensioner ta mutu, domin ita ba ta da madafa, ita ke daukar local gobernment, ta dauka state ta dauka wannan, wane ne naka a ciki?

Kowanne ya tsaya a kan shi wa za su tsaya? Babu, mu kuma muna da Unibersity, muna da Research muna da Institute muna da Abiation then other parastatal, wanda dama gwamnati ne ta kirkiro su ba wai cibil serbice ba ba wai state ba, to muna kokari za a wadannan, to yanzun gaskiya ba mu da matsala.

 

A matsayinka na shugaban kungiyar ‘yan fansho na jami’o’in Nijeriya kuma shugaban kungiyar ‘yan fansho na jami’ar Ahmadu Bello wane darasi ko wane abu ita jami’ar Ahmadu Bello take koyo daga sauran jami’o’i?

To, gaskiya kusan in ce Federal Unibersity Pension Association in ba ta koyi wani darasi a wajen Ahmadu Bello ba, to ba za su taba koya ba, mene ne dalili? Sun fara wannan Association tun 2000, da suka ga wahala ta kama wahala, su nemi nan su nemi nan, suka kafa kungiya din, amma kungiyar nan ba ta je ko’ina ba, tana nan haka, ba registration ba constitution ba wani takamaiman agenda na aikinsu to sai da na koma ABU a 2005 aka ce mini gashi gashi, to da suna gina Union na pensioner suka ga suna cutar su, suka kafa wata union wai NUPA aka ga wato fita daga abinda ake gudu ba, domin ita NUPA ta hada da state da pribate, mu ka ce a’a, to su kuma da suka kafa nasu purely Unibersity, ABU da ta yi joining a 2006, ni na fara zuwa taron a Awka, sai na ce musu, “Kun yi rigista?” Su ka ce, “A’a” “Kuna da Constitution?” “A’a” “To meye abin da zai nuna cewa ku kungiya ce?”

Sai na ce to ni ba zan iya magana a inda ba su da lasisi ba, don ni ba matsoraci ba ne, don ni ko waye zan yi mai magana, to in aka ce ina license din ka? To daga nan ne muka sa kafa, ABU kusan in ce ni na yi rijista da kudina na kaina, akwai kudin Union na ABU, muka yi kokari muka amince fa wannan muka koya masu yadda za a yi tafiya saboda gaskiya mun koya masu abubuwan da ya kamata su yi, karamin rancen yadda ya ke, ai ABU ta fara, suka ce ya za a ba ‘yan fansho? Mu ka ce ku gayawa Bice Chancellor na ku, waye ke biyan ku? Shi, to in an karbi bashi din ba sai ku sa hannu a debe a baka a debe a ba wanda ka ji bashi akwai laifi? Sai na ce to amma ku tabbata kada ku ce su biya maku idan wani ya mutu ku je wajen yaransa, dan ko kunje za a ce an an ce kada a basu, saboda haka sai Ku rage kwadai, dan union fee din nan Ku ajiye, duk abinda za a ce ba za su kai mutum goma ba wadanda suka mutu a wata, ko sun kai goma abin da za su biya ba mai yawa ba ne, da wuya ya kai dubu dari gobernment Unibersity ba yarda za a ce su zauna ba su da wannan kudin, kuma sun koya, har da bice chancellor ma sukan zo su yi magana, lokacin da ake biyan ariyas, nan ABU ita ce ta rubuta abin da yake biya yau, su ka rubuta ga yadda za a biya, sun rubuta nasu, mun yi rejecting abin da ABU ta ce a biya mutane, muka ce muma muna da ilimi, ga abin da circular ya fada, za ka ba mu abin da bai taka kara ya karya ba? Muka yi ta fada, suka ce to za a dinga kasafi biyu, da na ‘yan fansho da na ABU, anan ma’aikatar fansho na federal suka-duba-suka-duba, wanda ABU ta kawo shi ne ma fi kyau, wallahi all unibersities na ta ne ma fi kyau, aka zo yadda za a biya wata-wata, muna da yaronmu Hakim Baba Ahmed, yana general office na secretary to the gobernment, na ce,”To Baba, mu fa yanzu…” Kinkibau ya ce, “To ya za a yi a San yadda za a bi?” Ya ce, “Ran ka ya dade, a bani kwana biyu.”

Zariya suna da masu ilimin da za su yi, muka zo muka shirya table din nan, table ne mai kyau, suka zo suka ce ai an gama, da ba don haka ba, za a zo ne a nemi consultant na karya sai su kawo nan haka-nan haka sai su kawo wani ‘age’ haka, is rubbish, is a straight forward mathematics wanda na kuma yi na basu, suka gani suka ce baba sun gode, har kudi suka so su bani, na ce a’a, in har kun yarda kun biya pensioner suka ce, to ni na gode, to gaskiya some of the Unibersities sun nema taimako ga ABU har ya zama haka, ABU suka ce ai fenshon yanzu, wai taron da aka zauna ana ta yi ma BC namu Abdullahi godiya, muka ce Baba ba don kai ba, ya ce to ai ba damuwa an ta yaba ma shugabanni, to ka ji abubuwan da sun koya da kuma zaman lafiya.

 

A matsayinka na wanda ya ga jiya ya ga yau a jami’a, kuma ka tafi da shugabannin jami’a a matsayinka na shugaban ‘uan fansho na jami’o’in Nijeriya, ya za ka bayyana gudummuwar da kowanne shugaba ya bayar a lokacin da kake shugabancin wannan kungiya?

E to gaskiya, saboda goyon bayan da Ahmadu Bello su ka yi, su kuma sauran jami’o’i suka ji suma suka shiga goyon bayan shugabannin su, ba zan ce ba su taimake mu ba, dan wani lokaci ba su da kudi, wallahi duka bice chancellor din nan wanda na yi aiki da shi, ba wanda bai taimake ni ba, indan muna da matsala haka zan je, dan union din namu bai taka kara ya karya ba, muna da rikici kaza- muna da rikici kaza dan Allah a taimaka mana, in kuma mun ga abinda za su yi ba daidai ba, za mu ce a’a, ga yadda ake yi ga yadda ake tafiya a zamanin mu, kai ma in ka yi haka zai zame maka alheri, kuma ba BC da za a dauka a gabanmu ba mu je gidansa mun gaya mai gaskiya ba, run da ya ke mu a Unibersity mun San masoya mun san makiya, mun san ‘yan adawa mun San ‘yan tada wuta. Wasu a agenda ba abinda suke yi sai tada hankali, haka nan su nasu ya ke, to za mu ce ranka ya dade in ka zo za ka yi hakuri da hakannan, ba mu ce ka ki wani ba, ba mu ce ka so wani fiye da wani ba, amma ka bi daidai ka gama lafiya, kuma haka yawancinsu sun gama lafiya.

 

A daidai wannan lokaci akwai jan daga tsakanin kungiyar ASUU da kungiyar ma’aikatan jami’a, akan batun ariyas, ya kake kallon wannan dambarwa?

E to wannan dambarwan, a wata hanya su ASUU suna da nasu, wadanda ba malamai ba suna da nasu, to sai dai shi dan boko ya fi wanda ba dan boko na koyarwa ilimi a Unibersity, mu ASUU sun san abin da a takarda, da aka tambaye su kun ce a biya ku kudi na kaza-kudi na kaza, yaya za mu fahimce shi a takarda? Ni ma an biya mu amma na yi fushi, me ye na yi fushi? Namu kudin ba wai ba a bamu ba, amma da aka zo abin da ya kamata a bari a biya  wadanda suka gama digiri-digiri nasu domin sun sha wahala, to kudin ba a riga an basu ba, bari a ba su, mu da za a biya mu saboda yawan ‘yan makaranta, sai aka ce mu yi hakuri dama mu iyaye muna rike da mutane, saboda haka a cikin kudin nan ina da kudi kusan miliyan biyu da wani abu, amma kasan abin da aka yi min? Aka bani dubu dari da saba’in da bakwai dari bakwai da kaza-kaza wai namu nanan an biya mune, amma ma ka ga za su ba superbision, first graduate training dole a biya su da wuri sun kashe kudin su, na ce to shi kenan tunda yara ba karewa za su yi ba, to ku kun gama training, in an zo biya na biyu za a biya mu kudinmu, saboda haka to amma su non – academic problem din su basu tsaya sun tsara abin kowa da abinda ya ke da shi ba, to amma namu a anan Faculty of Education, department na …… Ba zan yi gasa da nan Faculty of Education ba, dan akwai malamin da zai koyar da yara dubu wannan ba shakka, to a namu department za a biya mutum ne saboda yawan edcess work load a kai the highest, saboda wani lokaci mukan dauku yara fiye da yadda ake, to ni kuma tausayi ne ba don wani abu ba, kuma wasu course na mu suna ba mutane sha’awa, to ba yadda za a yi mutum ka kore shi, in ka kore shi yau ka hana shi, wataran za ka same shi a wani gari zai ce baba na so in yi amfani da abu kaza saboda ya taimake ni yau ga ka a yau, to ka ji dalili, to suma suka ce suna kaza suna ober time, suna iya kawo takarda su nuna cewa suna ober time? To ka ji dalili, da aka zo bada kudi sai aka ba academic kaso biyu su kuma aka basu kaso guda, kuma laifinsu ne, wa ya ke so? Duk da shi a takarda, kuma bari in gaya maka wani abin da ba ka sani ba, dukka Unibersity, Allah ya ba ABU basira, da malaman ABU da shugaban ABU duk abin da Ahmadu Bello za ta yi akwai kanshin gaskiya a ciki, ko da kadan ne, ni na san unibersity, ko ta wajen pensioner na su na san wadannan sun fito wajen gaskiya, wadannan sun fito wajen karya, domin akwai alawan da muke ba junanmu, to wanda ya fito wajen karya zai nemi nashi da yawa, wallahi tallahi in ba gwamnati ta tsaya ba, yadda wasu unibersities su ka cuci gwamnati Allah kadai ya sani, amma ABU sai an tambayeka da-me-da-me ka koyar? Mutum nawa ka koyar wannan shekarar? Waccen shekarar mutum nawa? To ina takardar? Ga shi, da federal gobernment ta duba, aka ce to bari a yi bincike, da aka zo ABU dukka aka fidda, suka ce kai-kai-kai? Sai aka hana wasu, shi ya sa ma wasu ba a basu ba, aka ce ai department kaza a basu kaza, a dalilin me? Anmadu Bello da ku ke ganinta mu muke fita mu ji abubuwan da ke ciki, mu muke ganin abinda ke faruwa, gaskiya Ahmadu Bello Allah ya kafata fa manufa na gari.

 

Ya kake ganin wannan dambarwa za ta kawo karshe dan ganin cewa al’amurran koyo da koyarwa sun ci gaba kamar yadda saba a jami’ar?

E to, mu dai muna roko su non-academy su zauna da gwamnati, su gaya masu gaskiya, in dama ober time da suke cewa akwai aringizo a ciki, to a dawo daidai, a ce ok, wannan mutum ya yi ober time din sa, wannan mutum ya yi ober time dinsa, wannan mutum ya yi ober time kaza, to amma yana da wuya duka wadanda suka ce za su je su yi ober time bai wuce sakatori na edamination ba, sune lokacin da za a ce ana samun lokaci amma da ma aiki in kana yi kana tashi karfe hudu ne ko? OK ober time ne ka yi, lokacin edam mun ysaya a wurin, shikenan, amma a yi shi a rufe muma a bamu abu kaza kamar wasu Unibersities, ai wannan department a basu miliyan kaza wannan department a basu miliyan kaza a dalilin me? Kuma da aka zo rabo din wadanda suka yi obertime su fada, gaskiya tsakani da Allah, waye ke obertime? Mutum biyu ne; na sama da na kasa; misali kamar HOD, shi HOD is an academician shi za mu ce zai iya bata lokaci, amma kada ka manta sakatarori ba dukkansu ba, wanda suna tare da Head of Department din kusan in ce sune mai yawa sukan tsaya su yi aiki, to amma sukan tsaya su yi aikin nan ba a rubuta kaza-kaza-kaza ga time da official hour ya kare, ga time da ober time ya fara kuma ga time da obertime ya fara kuma ga time da ya kare, ga yawan awa din ga yawan kwanaki, amma yanzu dai ita gwamnati ina roka dai ita gwamnati ta dan kara masu wani abu saboda hankalinsu ya kwanta, indai akwai kudin a kashin gaskiya a dan sammasu, kuma in an zo rabawa su manyan su yi hankali, dan ina ji, kamar yadda na ke ji su suke creating problem, sai a kwashe kudi a ba wasu a ba wasu.

 

To ashe Dakta zargin da wasu su ke yi na cewa ita gwamnati ce ba ta bada wata formula na tsarin yadda za a yi rabon kudin ba ashe ba haka ba ne?

A’a ba haka ba ne ba, a’a, kudin me? Da ma basu a ciki, academic ne suka nemi abin, da suka kai suka samu sai suka ce wai su ma a basu, a baku me? Na daya basu da edcess work load, in ka ce kana da edcess work load, wa ka koyar? Obertime, akan me aka yi obertime din, ba kan edam bane? To shikenan, to basu tsaya sun tsara nasu daidiba, suka ce to za su basu ba ba za su bayar ba, amma kudin da za a bayar a bisa ga abinda muka nema a cikin kudin aka cire aka basu, dan su ba a ce masu ga ainahin abinda za a basu ba, mu mun nemi biliyoyi sai aka zo aka ce to ku za a baku kashi biyu ku za a baku kashi daya, yo ka ji yadda aka yi abubuwa, to amma daga baya yanzu bansan ko me suke yi ba, amma dai muna fata a daidaita a dawo a cigaba da aiki.

 

Dakta a matsayinka na shugaban kungiyar ‘yan fansho ta Nijeriya, kuma shugaban kungiyar ‘yan fansho na jami’ar Ahmadu Bello, wane sako ka ke da shi ga shugaban jami’a na wannan lokaci?

Sakona shi ne mu ci gba da hada kanmu, kuma mu yi watsi da dukkan wadada ke kokarin tarwatsa mu.Ana gab

 


Advertisement
Click to comment

labarai