Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Bauchi Bata Da Shirin Korar Ma’aikatan Jiharta, In ji Liman Bello

Published

on


Gwamnatin jihar Bauchi bata da wani shiri na korar ma’aikatan jihar wadda wasu ke yadawa na cewar ana shirin korar wasu daga aikinsu, gwamnatin jihar ta ce wannan labarin karya ne kawai ake yadawa a cikin jihar domin tayar wa ma’aikatan da hankalinsu kan aiyukansu, gwamnatin ta ce wannan jita-jita ne kawai marar tushe wacce bata da makama.

Shugaban ma’aikatan jihar Bauchi Alhaji Liman Bello shi ne ya bayyana hakan a ranar Talatar nan jiya kenan lokacin da yake ganawa da wasu ‘yan jarida a ofishinsa ya ce jita-jita ne kawai marar tushe da wasu ke ta yadawa domin jawo wa gwamnatin Bauchin mai ci bakin fenti da kuma neman kusheta daga ma’aikatan jihar da kuma sauran jama’an jihar.

Ya yi bayanin cewar a halin da ake ciki gwamnati mai ci bata shirya ko kuma tashi shirin dakatarwa da izinin aiki ga wasu ma’aikata ko kuma shirin korarsu daga bakin aikinsu ba, ya ce wannan jita-jitan wani yunkuri ne kawai na wasu bata gari masu son ganin sun nuna gwamnati mai ci ta gaza da kuma neman dakufar da ita daga shirinta na ciyar da ma’aikata gaba da kuma kyautata musu rayuwarsu.

Shugaban ma’aikatan ya shawarci dukkanin ma’aikatan jihar da kuma illahirin jama’an jihar da su yi facakali da wancan jita-jitan da wasu ke yadawan a cewarsa gwamnatin jihar bata da masani kan shirin korar kowani ma’aikaci, ya ce a halin yanzu gwamnatinsu ta dukufa ne kawai domin ci gaba da kyautata rayuwar ma’aikata da kuma tabbatar da jin dadinsu da kuma walwalarsu a kowani lokaci ba shirin korar wani ma’aikaci ba.

Dangane da ma’aikata ‘yan kwangila kuwa, Alhaji Liman Bello ya ce gwamnatin ta gama yanke shawar dakatar da su domin kwangilarsu ta kare, ya ce gwamnatin tana nan ta shirye-shiryen samar da aiyukan yi wa matasan jihar da zarar tattalin arzikinsu ya habaka, ya ce shirye shiryen samar da aiyukan yi sun jima da kuma yin nisa.

Da aka tuntubi shugaban kungiyar gwadago ta jihar Bauchi kan wannan batun na korar ma’aikata, Comrade Hashimu Gital ya misalta wannan jita-jitan a matsayin wani batun da bai da tushe ballantana kuma makama yana mai bayyanin cewar a tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da kuma kungiyarsu akwai kyakkyawar fahimta, ya kuma ce gwamnatin jihar ba za ta dauki wani mataki ba face ta yi shawara da su kan dukkanin lamarin da suka shafi ma’aikata don haka suma basu da wata masaniya kan wannan shirin da ake jita-jita a kansa.

Shi ma dai sai kuma ya bukaci ma’aikatan jihar da su yi watsi da jita-jitan su ci gaba da gudanar da aiyukansu cikin kwanciyar hankali da kuma bukatarsu da su ci gaba da mara wa gwamnatin baya a shirinta na ci gaba da kyautata rayuwar su ma’aikatan jihar ta Bauchi.

Kwamared Gital ya jinjina da kokarin gwamnatin jihar na hanzarta amincewa da karin girma ga wasu ma’aikatan da ta yi bayan sun yi jarabawar da suka yi na karin girma a watan Disamban da ta gabata, yana mai bayanin cewar hakan zai yi matukar kara wa ma’aikatan kumajin yin aikinsu yadda ya dace ba tare da taraddadi ba, ya kuma roki gwamnatin ta ci gaba da jan ragamar harkokin ma’aikatanta kamar yadda suka dace.

 


Advertisement
Click to comment

labarai