Connect with us

LABARAI

Cutar Lassa: An Rufe Makarantun Jihar Ebonyi

Published

on


Gwamnatin jihar Ebonyi ta bada umarnin rufe duk makaran tun Jihar sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa, wasu ma’aikatan asibitin Irrua dake Abakaliki tare da wasu jama’ar yankin sun kamu da cutar.

Kwayar cutar zazzabin na Lassa na janyo zubar jini ga wanda ya kamu da ita, kuma beraye ne ke yada ta ga bil’adama ta hanyar kashi ko fitsarinsu da kan taba kwanuka ko abinci.

Kwamishinan Ilimi na jihar  Farfessa John Eke ya sanar da rufe makarantun jihar kamar yadda ya samu rahoton wata uwa da danta sun kamu da cutar a jiya Laraba, sannan ya ukaci iyaye da su kiyaye tsaftace muhallinsu da lura da lafiyar yaransu don kaucewar yaduwar cutar.

John Eke, ya kara da cewa, makarantun za su cigaba da zama a rufe har zuwa ranar Juma’ a makon gobe.


Advertisement
Click to comment

labarai