Connect with us

SIYASA

Takarar Gwamnan Nasarawa Ina Nema Wajen Allah –Mataimakin Gwamna Nasarawa

Published

on


A ranar litinin ne mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Silas Ali Agara ya kaddamar da kanshi gaban shugabannin Jam’iyyar APC ta Jihar, tare da dubban magoya bayanshi, a Babban Birnin Lafia.

Bayan tarbar da Shugabannin Jam’iyyar APC suka yi masa na girmama wa da ban girma. Sun kuma bukaci ya bayyana masu makasudin zuwansa gaban dubban al’umma. Inda anan, mataimakin Gwamnan ya mike ya fara da taken Jam’iyyar APC. Ya bayyana dalillin zuwansa ofishin jam’iyya a wanan lokacin, tare da dubban magoya bayansa, “Na zo ne na gabatar da kaina gaban Shugabannin Jam’iyyar APC ta Jihar Nasarawa. Na tabbatar masu da cewa na amsa kiran da al’umman Jihar Nasarawa suka yi min cewa basu ga wanda ya dace ya gaji gwamna Al-Makura ba face ni.” in ji shi

Ya kara da cewa duk lokacin da al’umma suka bukaci ka yi abu, to sun ga cancntane gareka. Kuma a garinsu ni zan kwatanta ayyukan Gwamna Al-makura saboda ba karamin cigaba alumman Jihar Nasarawa suka samu a wannan Gwamnatin ba.

Mukaddashin Gwamnan ya ce kiran da jama’an Jihar Nasarawa sukayi min cewa sunga cncantata na dacewa na gaji Al-makura a shekarar 2019.

Silas Ali Agara ya ce wannan kiran da jama’a sukayi min baya rasa nassaba da yadda suka kalli dadewa da gogewana a siyasa.

How. Agara ya ce na kasance tare da Gwamna Al-makura tun a 2010 munyi yakin neman zabensa har Allah ya kai mu ga cin Nasarawa. Ya kara da cewa tunda aka kafa Gwamna a shekarar 2011 mike tafiya tare kuma Gwamna bai bambamce kowa cikin abokan tafiyarmu ba.

Ya ce Gwamna Al-makura yana karban shawara daga dukkanin mukarrabansa.

Haka zalika Mataimakin Gwamna ya ce, dukan alumman dake rayuwa a Jihar sun ga rawar da Gwamna Al-makura ta taka.

Ya ce wannanne ya baiwa kowa dama da ya fito ya nime takarar gadan wannan kujerar saboda duk wanda ya gaji Gwamnan zai dasane daga inda Gwamnan ya tsaya.

Da aka tambayeshi baya ganin akwai kalu bale a neman kujerar Gwamna?  Sai ya ce ai babu abin da yake da kyau ace idan ana nemansa a zameshi cikin sauki. Dan haka duk wani kubale mjnriga munshirya mashi saboda mu wajen Allah. Muke nema saboda shike bada mulki ga wanda yake so. Kuma a lokacin da yake so.

Ya kara da cewa duk kudinka duk jama’anka idan Allah ya ce ba kai bane Gwamna babu abin da zaka yi. Sanan ko baka da kowa idan Allah ya ce kaine to babu wanda zai hanaka domi ikon Allah yafi komai.

Silas Ali Agara ya bukaci abokan takararsa da su zaman masu hadin kai muyi siyasa mai tsafta bada gababa. Mukkyaye hakin alumman Jihar Nasarawa. Kada mu nuna bambamci na addini ko na kabila muyi kokari mu samar da cigaba a wannan Jihar.

Ya roki sauran yan takara da mu hada kai duk wanda Allah ya bashi ni na yarda zanbishi saboda nasan Allah ne ya bashi. Kuma idan nine Allah ya bane ina rokon abokan tafiyata su bani goyon baya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai