Connect with us

RA'AYI

Raggo Ba Ya Aikin Soja Da Aikin Jarida

Published

on


‘Yan jarida sune kunnuwan gari masu jiyo labarai gami da yada wa jama’a su ji. ’Yan jarida suna daf da yin kafada-kafada da Malamai da kuma Likitoci duba da yawa aikin su yake ilimantarwa, fadakarwa gami da wa’azantarwa.

Aikin Jarida aiki ne mai matukar muhim manci ga masu yin aikin da kuma Jama’ar da ake aikin domin su. Dimbin Jama’a basa aminta ko gamsuwa da duk wani labarin da Jama’a za su fadi masu ta hanyar baki da baki.

Sun fi yin na’am ko yadda da duk irin labarin da suka ji a kafar yada labarai ta Yan jarida. Ko wane irin labari zasuji suna gamsuwa dashi. Hakan ya sa labarin da yafito daga kafar Yan jaridar yake zama raba gar dama.

Domin kuwa da zaran wani yazo cikin Jama’a yana bada labari kamin su gamsu da labarin zasu tambashi ina yasamo labarin? Da zaran ya ce ‘ya ji ko ya gani a wata kafar yada labarai ne’ to Jama’ar zasu aminta da labarin. Hakan ne yasa Yan’ Jarida suka samu aminta da yadda gamida

daukaka ga Jama’a.

Duba da ganin aduk inda Dan jarida ya je ko a wurin wani taro ko inda ake bin layi kamin a isa inda ake bukata isa. Za ka ga da zaran Dan jarida ya iso wurin Jama’a suna martaba shi sosai da

sosai ta hanyar bashi damar fara yin gaba. Duk irin yana yin da ake ciki walau na Sanyi/Zafi/Iska/Ruwan sama kai ko da Yaki ake yi Dan jarida yana sadau kar da ransa domin ya samoma Jama’a labari.

Ta hakan Yan jarida da dama sukan rasa rayukan su. To ! Amma hakan bai sa Yan jarida yin kasa a Gwuiwa wajen nemo labari ba. Yan jarida sukan kasu kashi-kashi, akwai wadanda suka karanci aiki a Makaranta matakai daban-daban.Akwai kuma wadanda basu karance aikin ba.

Amma kuma sunada matukar gogewa sosai akan aikin. Wanda wasu har suna yin kafada-kafada da wadanda suka karanci aikin.Yan’ Jarida sukan tsaya a tsakiya wato basu wancan bangaren basu wannan bangaren.Sukan bugi Jaki su bugi Taiki! Ma’ana sukanji daga bakin Jama’a su kumaji daga bangaren Gwamnati ko Jagororin Jama’a. Domin ka manta gaskiya da adalci. Haka Yan jarida ke tafiyar da aikin su bisa ga dokoki ko sharuddan aikin nasu. Akwai hukumomi da suke kulawa ko bin diddigi ko sanya ido akan aikin Yan jaridar. Gudun fada tarko ko fushun irin

wadancan Hukumomin yasa dimbin Yan jarida sukanyi taka tsan-tsan wajen kiyaye dokokin.

Duk da na san akwai ‘yan jaridar da sun rigaya sun san dokokin kuma suna bin su sau da kafa.

Idan ma suka ga wani zai taka dokar daga cikin su zasu nusantar dashi ko tsawa ta mashi.Domin ya kiyaye ya kuma kara tsaftace aikin gamida kara nemar ma aikin martaba ga Jama’ar da ake aikin domin su. Sai dai kash! Gaduk kan alamu wannan tsari da Yan jaridar suka biyo tiryan-tiryan shekaru da dama. Wasu ‘yan jaridar na yun kurin sauka daga kan ita waccan hanya da sahihan yan jarida suka biyo tun farko. Wadancan yan jaridar sukan yi aikin sune tsakani da Allah basa kwadayin abin Duniya su kanyi aikin su batare da nuna bam-bancin Addini/Yare/ Kabila/Jinsi ko Siyasa ba.

To sai da mafi yawan Yan jaridar yanzu lamarin ba haka yake a wurin su ba. ‘Yan jarida suna nuna fifiko a wani bangare.

  1. ’Yan Jarida sukan yi Ubangida a siyasa, hakan ya sa suke nuna akidar su a fili.
  2. Sukan sayar da labari misali in su samo labarin da ya shafi wani dan siyasa, ko wani mai hannu da shuni kuma idon suka saki labarin ba zai ji dadi ba sai su je su gaya masa ko gwada masa labarin inda zai basu kudi domin suki

sakin labarin.

  1. Suna nuna fifiko ko bangaranci idan har sun ci karo da labarin da ya shafi addininsu ko Yanki ko Al’adunsu ko Yare ko Jam’iyya ko Ubangidan su ba za su saki labarin ba.
  2. Kazalika ko hira suka yi da wani to in har bai basu Burawun Embulof ba wato na Goro to zaiyi wuya su saki labarin.
  3. Sukan buga da sakin labarin da bai da sahihanci wato labarin kanzon Kurege.
  4. Sukan buga gundarun labarin da ya sha bamban da kanun labarin.
  5. Sukan fi bada dama ga wanda yake kare muradun su ko na Ogansu, damar yawan zantawa dashi don burinsu ya cika.

To! Sai dai, ina so mai karatu ya sani ba wai duka ‘yan jarida ne suka kauce ma

hanyar ba. Da akwai dan sauran na gari a cikin aikin. Sai dai abin mamaki da daure kai! Duk wadannan kura-kurai gami da sakin layi da taka dokar aikin Jarida da wasu ‘yan jaridar ke yi. Da sanin su Hukumomin dake kulawa da aikin Jaridar hakan yake faruwa? Ko kuwa Hukumomin sun durkushe ne? Ko kuma suma sun saki layi suna yi wa dokar ta su hawan kawara? Domin inda Hukumomin suna yin hukuncin ba sani ba sabo ga duk wanda aka samu da aikata laifi. Hukuncin zai iya zama darasi ko izina ga wasu dake yunkurin gurbata aikin na Jarida.

Daga karshe ina fatan hukumomin za su tashi tsaye akan aikin su. Su kuma Hukumomi da

kamfanonin yada labaran ya kamata su yi kokari wajen ganin sun tsaftace aikinsu ta hanyar daukar wadanda suka dace suka kuma cancanta a dauka aikin. Domin in har aka zura ido ana ci gaba da tafiya a haka, to mutunci da kiman aikin Jarida zai zube kasa warwas! Wanda in har

hakan ta afku zaiyi wuyar gaske amaido da martabar aikin cikin ‘yan Shekaru. Domin don gobe ake wanke tukunya!

Daga Haruna Muhammad Katsina,

Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a,

07039205659


Advertisement
Click to comment

labarai