Connect with us

RAHOTANNI

Jihar Kano Ce Jihar Da Ta Yi Nasarar Rungumar Shirin Rage Cinkoso A Gidajen Yarin Kasar Nan

Published

on


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin kwamitin masu ruwa da tsaki kan harkokin rage cinkuso a gidajen yarin kasarnan wanda Ministan  Sharia  Abubakar Malami (SAN) da kuma shugaban kwamitin mai sharia Ishak Bello  alkalin babbar kotun Abuja suka ziyarce shi a

fadar Gwamnatin Kano.

Gwamnan Ganduje ya yiwa bakin nasa lale marhabin tare da nuna farin cikinsa  bisa zabar Kano a matsayin wurin farko da suka ziyarta. Domin tabbatar da ganin gidajen yarinmu an rage cinkoson da ke addabarsu wanda hakan ke cikin kudurin shugaban Kasa Muhammadu

Buhari.

Daga nan sai ya ci gaba da cewa tun zuwan wannan Gwamnati mun yi wa sama da mutum 1,500 ‘yan kurkuku afuwa wadanda suke da kanana laifuka da aka dauresu  sakamakon gazawarsu na biyan tarar da aka yi masu ya ci gaba  da cewa akwai bukatar  gwamnatin tarayya ta yi la’akari  da mayar da gidajen yarin karkashin gwamnatocin jihohi domin samun kulawar data kamata.

Da yake gabatar da jawabinsa Ministan Sharia Abubakar Malami SAN ya godewa Gwamna Ganduje bisa goyon bayan yaki da cinkoson gudajen yarin kasar nan, ya bayyana cewa Jihar Kano ce Jihar farko da ta rungumi wannan shiri ta hanyar yiwa mazauna gidajen yarin da suke jihar Kano afuwa masu yawan gaske, musamman lokacin ziyarar da shugaban Kasa ya kai jihar Kano inda aka yiwa mutum 500 afuwa , yanzu haka kuma akwai karin mutane 368  da aka kammala shirye shiryen sallamarsu daga gidajen yarin na Jihar Kano wanda Gwamnatin Kano ta amince da biya masu tarar sama da Naira Miliyon goma sha shida, wanda jimmala mutum

868 aka yiwa afuwa cikin watanni biyu.

Shugaban Kwamitin wanda kuma shi ne alkalin babbar kotun Abuja ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda Gwamnatin Kano ke saukaka aikin, ya kara da cewa da ace sauran gwmanoni zasu kamanta abinda Gwamna Ganduje ya yi cikin kankanen lokaci kwamitin zai komawa shugaban Kasa da kyakkyawa rahoton kammala aikinsu. Daga nan sai ya bukaci sauran jihohi dasu gaggauta rungumar wannann shirin domin kawar da cinkuson da ke addabar gidajen yarin kasar nan kamar yadda Gwamna Ganduje  ya aiwatar a JIhar Kano.


Advertisement
Click to comment

labarai