Connect with us

SIYASA

Ba Wanda Ya Isa Ya Hana Kwankwaso Zuwa Kano –Tsohon Kakakin Majalisar Kano

Published

on


Daya daga cikin jiga–jigan magoya bayan Injiniya Dakta Rabiu Kwankwaso, kuma tsohon kakakin majalisar Jihar Kano, Honarabul Isyaku Ali Danja ya bayyana cewa babu wani mahaluki da ya isa ya hana madugu uwabn tafiyar Kwankwasiya zuwa Kano.

Tsohon Kakakin na Majalisar Jihar Kano, ya yi wannan bayani ne a wani gagarumin taro da magoya bayan kwankwasiyya suka yi a lugat, domin shirye –shirye na zuwan jagoran kwankwasiyya Birnin Kano. Inda bangarorin magoya baya suke ta musayar yawu akan zuwan tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya.

Majiyarmu ta nakalto Musa Iliyasu Kwankwaso yana cewa basu yarda wani mutum ya zo ya tayar musu da hankali ba, wannan ne ya sa suma magoya bayan Dakta Rabiu Musa Kwankwaso suke ta tallata zuwan jagoran nasu.

Inda suke raba jajayan huluna a fadin kananan hukumomi arbain da hudu dake jihar kano. A wannan ranarma sun raba kimanin jajayan huluna dubu goma sha shida. Wannan taro ya sami halartar manyan jagororin kwankwasiyya na jihar kano musamman tsofafin kwamashinonin jihar na locacin tsohuwar gwamnatin Dr Rabiu Kwankwaso. Kammla wannan taro keda wuya wakilinmu ya sake ganawa da tsohon kakakin majalisar jihar kano honarabul isyaku Ali danja yace wannan ranace ta farin ciki domin wannan taro da mukeyi. Shirye – shirye na zuwan jagoranmu Dr Rabiu Musa Kwankwaso wanda zaikawo ziyara ta siyasa da kuma dukkannin abubuwan da suka faru zai sami dama ya jajanta. Wato a wannan jiha tamu daga nanne wakilinmu ya tanbayeshi, baka ganin magoya bayan Ganduje zasu hanaku wannan taro? Wannan abune da bazaka hana kowa ya fadi albarkacin bakinsa ba. Kuma ina tabbatarma injiniya Dr Rabiu Musa Kwankwaso mutum ne dan jihar kano, kuma wanda yake da asali ajihar kano, mai taimakawa al’ummar jihar Kano dama nigeria baki daya. Saboda haka babu wani daya isa yahana wani zuwa jiharsa kuma kamar mutum irin wannan, kuma matsayinsa na wakili amajalisar kasa wato ta dattawan Nigeria. Don haka babu wani mutum dan Adam a nigeria da zai hana wani zuwa garinsa.


Advertisement
Click to comment

labarai