Connect with us

TATTAUNAWA

Ba Hana Kiwo Ne Mafita A Nijeriya Ba, In Ji Shaikh Dahiru Bauchi

Published

on


Babban Malamin addinin Islama, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnatin tarayya a karkashin Muhammadu Buhari da ta tashi tsaye wajen kokarin shawo kan rikicin da yake addabar wasu yankunan kasar nan na rikicin Fulani Makiyaya da kuma Manoma. Yana mai bayyana cewar tashi tsaye domin shawo kan rikicin ne kawai mafita ba wai yunkurin hana Fulani kiwo ba.

Dahiru Bauchi wadda ya bayyana hakan a jiya sa’ilin ganawarsa da manema labaru a gidansa da ke Bauchi, ya ci gaba da cewa, tun usuli shi makiyayi ya saba yawo ne, don haka maganar hana shi yawun kiwo ba zai haifar da komai ba, illa wani tashin tashinan.

A don haka ne Dahiru Bauchi ya ce hanya daya tilau dai shine kawai gwamnatin tarayya ta tabbatar da samar wa makiyaya muhallan da suka dace domin yin kiwo da kuma mashayar dabbobi domin kaurace wa tashin hankali.

Ta bakinsa “Abubuwan da suke faruwa a wasu jihohi a Nijeriya na take dokoki da hakkoki, mu a shari’armu na musulunci mutumin da yake gari yana da dabbobi ya zamana an nemi wurin da za a yi kiwo aka rasa, an nemi wajen da za a ke shayar da ruwan aka rasa, sai a ba shi shawara yake sayo abinci irin su harawa da sauran abubuwan da suke bukata. Idan kuma ya zamana ba a samu wajen kiwo ba, ba a kuma samu an sayo an kawo musu ba, sai a ba shi shawara ya kaura daga wannan garin ya koma wata garin da ake samun abubuwan kiwo domin su dabbobi basu zama sai sun samu wajen kiwo suna garari, sai kuma sun sha ruwa”. ta bakinsa.

Ya daura da cewa “Idan kuma mutum ya ce shi babu wadda zai sanya ya kaura daga garin nan sai, a ce a’a hukuma tana baka shawara ko ka saida dabbobinka, domin su dabbobi dole ne sai sun ci abinci, babu yadda za a ajiye dabbobi babu abinci. Idan mutum ba zai iya kaura don dabbobi ba, to sai ya saida su ya ajiye kudinsa a daki. Idan kuma mutum yaki yin hakan dukka, sai gwamnati ta kwace dabbobin ta saida alabashi ta bashi kudinsa domin ba zai iyu a bar dabbobi babu ci babu sha ba”. In ji Shehen.

Ya kuma ci gaba da cewa “Abun da yake faruwa a wasu jahohin da suka hana a yi kiwo, wannan ko kadan ba zai iyu ba; dabbobi suna da rai kamar mutane, hana musu kiwo ba zai iyu ba”. in ji Shi.

Ya ce, dole ne kuma gwamnatin tarayya da shiga cikin lamarin domin kawo karshen matsalolin nan “dole ne gwamnatin tarayya ta shawo kan irin wadannan matsalolin, ta yadda kowa za ta yi shi ne dole ne ta ware filayen kiwo wadda shi wannan wajen, wajen kiwo ne kawai babu wadda zai yi noma a wajen babu wadda zai kuma yi gida a wajen, filaye ne kawai na kiwo da kuma shayarwa. Sannan kuma a yi burtali inda shano za su fita su yi kiwo da inda za su dawo, domin dole ne a yi musu hanya wa shano. Wannan burtalin da za a yi musu din ba za a yi noma ko gina gida a kansa ba. dole ne kuma a yi makiyaya domin a samu ruwan sha, dole ne a samar da yadda za a ke samun zirga-zirgan dabbobi”. In ji Dahiru Bauchi.

Bai fa tsaya haka nan ba, ya ci gaba da bayani kan wannan rikicin da ke ci gaba da hauhawa a kasar nan “tilas ne a yi kiwon dabbobi. Abu kadai da zai raba wannan fadan shi ne a yi wajen kiwo, amma idan gwamnatin tarayya ta yi shiru ta bari ana fada irin hakan, fadan ba zai taba karewa ba. domin su masu shano ba za su zuba shanonsu a cikin teku ba, kuma ba za su maida shanonsu wasu abubuwan da ba su cin abinci ba, dole ne kuma ita gwamnati ta mutunta dokarta, domin a cikin dokar gwamnati kowa yana da ‘yancin ya yi arziki irin tasa wacce ta dace da shi”.

Dahiru Bauchi ya ce ba fa makiyayi shi kadai ne mai kiwo ba “ita kiwo ta shahara ne da bafulatani amma ba wai Bafulatani kadai ne mai kiwo ba, dukkanin wadda yake da dabbobi to mai kiwo ne, domin dole ne zai basu abinci. Don haka ne muke bayar da shawara wa gwamnati da ta yanki wasu wuri da filaye ta baiwa masu kiwo. Masu wuraren nan ko sun yarda ko kuma basu yarda ba, ita gwamnati sai ta yi wa masu kiwon nan haka, domin a samu wajen kiwo da kuma wajen mashayin dabbobi”. In ji Bauchi.

Ya ce bawai yana magana don shi bafulatani ba, ya ce babbar damuwarsa a samu wanzuwan adalci a tsakani “Ni da na ke maganar nan ni Bafulatani ne ta ko’ina nan kuwa, amma bawai ina magana don ni bafulatani bane, a’a ina magana ne akan ilimin addini yadda ya ajiye rayuka kowanne da yadda Allah ya ajiye shi”.

Dahiru Bauchi ya dai jaddada ya kuma nanata cewar gwamnati ta samar da filayen kiwo wadanda babu wani abun da za a yi da wadannan filayen sai kiwo da kuma shayar da dabbobi, a cewarsa yin hakan zai yi matukar kawo sauki da kuma shawo kan rikicin yawan mace-mace da ake samu a fadin Nijeriya “Don haka ne ya kamata a duba a yi adalci kowa a ba shi hakkinsa, kada a tsaya duba cewar su wadannan kabila kaza ne ko kuma mutanen yanki kaza ne, shi mai iko (shugaba kenan) yana duba kasarsa ne da idon rahama don yin adalci ga kowani bangare”. A cewarsa.

Ya kuma karkata da cewar dole ne kuma fa ake sara ana kuma duba bakin gatari domin kula da masu haifar da rikicin don shafa wa wasu bangare bakin fenti “Kuma a rinka lura a yi adalci, wadansu mutane su dauki nau’in unifom na wadansu mutane su dauki bindigogi suna kashe mutane ana cewa Fulani ne wannan dole ne a duba a yi hukunci na gaskiya akansa”. In Shi.

Malam Dahiru Bauchi ya ce batun samar da filayen kiwo da mashaya ga makiyaya abu ne wadda ya dace gwamnati ta yi amfani da ikonta da kuma karfinta, yana mai cewar ba wai jiran ra’ayin wasu ko kuma amincewar wasu gwamnati ya kamata ta tsaya yi ba, ya ce koda wasu sun ki yin hakan da gayar bukatar gwamnati ta tabbatar da samar da wannan yanayin cikin kankanin lokaci domin yin adalci wa kowani bangare.

Ta bakinsa “maganar sanya dokar hana kiwo ba fa zai iyu ba, don haka dukkanin wadda ya yi hakan bai neman zaman lafiya, don haka ne muke kira ga kowa da a tsaya a bi doka domin a samu zaman lafiya, kuma kowa ya tsaya ya rike matsayarsa don ganin ba a samu shiga hakkin wasu bangarori ba”. A cewarsa

Ta bakin Shehun ya ce wannan rikicin bawai na addini bane, rikici ne kawai yake faruwa na son zuciya da wasu ke da shi “Musulunci addinin zaman lafiya ne, Kiristanci kuma addinin tausayi ne, ta yaya mai addinin tausayi ya yi fada da mai addinin zaman lafiya? Idan ka ga an yi hakan to wani dai ya bar layin addininsa. Dukkanin abun da ya fi muni a cikin addini bayan Tsafi babu kamar kisan dan adam. Su aure da ake yi, su idda, su kulle duk ana kiyaye ran dan adam ne. babu abun da ya fi muni kamar kashe jama’ar musulmai ko sauran bangaren jama’an musulmai bayan tsafi”. Ta bakin Shi.

Ya ce, dukkanin gwamnan da ba zai iya rayuwa da Fulani ba, to ya ajiye gwaman kawai ya fi masa “Amma a sallama wasu jahohin Nijeriya a hanun wasu bangarori kamar babu gwamnati wannan ya kamata a janye wannan. dukkanin mutumin da ba zai bari a yi kiwo a jiharsa ba, to ya ajiye gwamnan jihar kawai ya tafi can sahara inda babu mutane babu dabbobi, babu mutane yaje ya yi gwamnansa a can. Amma duk inda za ka zauna a garin da ke da jama’a kuma jama’an da sukea da dukiya dole ne a baiwa kowa hakkinsa”. In ji shi.

Daga nan kuma Dahiru Bauchi ya yi kira ga janibobin jama’a da su tabbatar da zaman lafiya a tsakani domin a cewarsa tashin hankali bai daga cikin addinin musulunci ko kuma na kiristiyaniti. Don haka ya ce da bukatar dukkanin sashin jama’an kasar Nijeriya da su dawo cikin hayyacinsu domin zaman lafiya, ya kuma yi kira ga dukkanin bangarorin jama’an musulmi da na kirista da cewar su zauna lafiya da juna a Nijeriya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai