Connect with us

TATTAUNAWA

Ya Kamata Matasa Su Rage Tsattsauran Ra’ayin Addini – Sani Haris

Published

on


Kungiyar Rasulul A’azami Foundation reshen Jihar Bauchi ta gudanar da taron bita ga matasa sama da 80 domin ilmantar da su game da rage nuna tsaurin ra’ayi a cikin  addinin musulunci, musamman game da ra’ayin akida maras kyau da ke sa a cutar da mutane dmin banbancin akida ko ra’ayi wanda ake ganin shi ke taka muhimmiyar rawa wajen bullar rassan kungiyoyi a wasu kasashe na duniya saboda yadda wasu matasa ke daukar makamai suke fada da masu banbancin akidar da ba tasu ba. A saboda haka ne wakilinmu a Bauchi, MUAZU HARDAWA, ya tattauna da MALAM MOHAMMED SANI HARIS, inda ya yi ma sa karin bayani kan wannan taron bita da ya gudana na tsawon kwanaki uku daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a makarantar Sumayya da ke Bauchi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me za ka bayyana game da makasudin wannan taron bita  da kuka gudanar kuma wane sako kuke dauke da shi?

Assalamu alaikum warahmatullah, wasallahu ala nabiyyu Muhammad sallahu alaihi wasallam, hakika wannan kungiya  ta(RAAF) a karkashin sashin kwamitin ilmantarwa karkashin Khadi Elmainari sun yi nazari kan wasu bakin akidu da ke shigowa cikin matasa kuma suke jefa su cikin wani mummunan ra’ayin, don haka mun shirya wannan daura ta kwanaki uku  an zauna anyi tunani kan abubuwa da ke shafar yaran mu wajen gurbata tunani saboda yadda matasa suke zaune basu da abin yi shine suke nemawa kansu abin yi ta kowane hali kuma komai munin sa. Saboda shine ya ke sawa su dauki makami su yaki wani har su kashe saboda tunanin ya saba wa ra’ayinsa ko na wani wanda ya ke goyon baya. Don haka muka ga ya kamata mu fara shirya irin wannan taron bita don mu tare su daga irin wannan matsala don su kaurace wa irin wannan akida ta hanyar shirya su kan hanyar kirki, bama son matasa su shiga akida ta shirme su gane hanyar kirki ita ne ta fi alheri.

Sayyidina Aliyyu  Alaihis salam ya bayyana dan adam shi dan uwanka ne kuna tare a addini a addini ko a halitta, don haka kuna tare, kuma haramun ne ka kashe dan uwanka ko ka illata shi ko aibanta shi ko kafirta shi ka ce ya fita a musulunci wannan bakon abune a musulunci. Shari’ace kawai mai iya hukunci kan mutum bayan dogon nazari kana bin da ya aikata. Abu na biyu kuma shine hana matasa shaye shaye ko mungayyen ayyuka da zinace zinace, domin Manzon Allah SAW yace fiyayyen mutane shine wanda ya fi amfanar da al’ummar sa, shi yasa muka tara su don ilmantar da su mu gamsar da su mu hana su shiga cikin miyagun akidu domin akidar kashewa ko kafirtawa bakuwar akida ce a cikin addinin musulunci. Don haka muna so mutane su kasance masu alfahari da matasa a cikin al’umma wajen nuna misali.

 

Kamar yaya matasan suka dauki wannan koyarwa da yadda kuke son su isar da ita zuwa gaba?

Wannan abu ya samu karbuwa saboda måun yi mamaki mu na zaton mutane 75 zamu ilmantar yanzu sun fi 80, daga Bauchi da Gombe da Dass da Azare da sauran wurare.  Saboda Bahaushe ya ce karamin sani kunkumi ne, don haka muke ba ilmi muhimmanci a kan fannoni masu yawa na ilmi a san komai, har malamai su ba almajiri damar cewa yanzu shima ya zama malami zai iya ilmantar da wani. Kuma idan ka ba mutum ilmin tajwidi ba ilmin fikihu  ba nahawu ba balaga da sauransu to sai ya kasance an shiga cikin illa an kasa gane komai, saboda addinin musulunci yana son kowane ilmi don haka a yanzu sai ka ga matashin da ya karanta ahlari sai ya dauka cewa shi melami ne haka wanda ya karanta ishmawi ko wani littafi alhali ilminsa bai taka kara ya karyaba. A addinin musulunci kurum ake yi wa wannan hawan kawara ga ilmi, kowa yace shi Malam ne alhali bai ilmantu ba. Amma ko a dokar Nijeriya don ka karanta shari’a ba za ka zamo lauya ba sai ka je makarantar lauya ka yi karatu sun gwada ilmin ka  kafin su baka takardar zama lauya ta yadda za ka iya kare mutane a gaban kotu, ya zamo za ka iya fassara dokar Nijeriya har ka amfanar. Mu ilmi a gidan Ahlul baiti muhimmi ne sai mutum ya ilmantu ya bada fatawa dole sai ya san kowane fanni na alkur’ani da hadisi da mandik da duk wani sashe na ilmi a musulunci kafin ya kira kansa malami.

 

Mene ne shawararka ga Musulmi kan abin da ya shafi hadin kai?

Ya tabbata dole mu hada kan mu a matsayin mu na Musulmi, domin ba al’ummar da take zaune kara zube babu hadin kai kamar Musulmi, saboda idan ka duba duk dukiya tana gabas a kasashen musulmi haka ilmi, amma musulmi sune suka fi wulakanta saboda rashin hadin kai, yau a hada wannan kasa yaki gobe a hada waccan kasar kullum sai cinye musulmi ake yi su ma  kowa yakar juna yake yi, kuma Yahudawa da Kiristoci kowa yana bin umarnin manyan sa suna magana da murya guda, idan Fafaroma ya yi magana ba wanda zai kauce, amma mu musulmi mune ke da  matsala bamu da jagoranci a duniya kowa da inda ya sa gabansa, kullum muna cikin musanya da juna a fannin ilmi da zamantakewa na addini da rayuwa a wannan zamani da muke ciki. Ba wanda ke iya magana a matsayin sauran musulmin duniya yau a cinye wannan gobe a cinye wancan duba yadda ake ciki a Isra’ila game da masallacin baitil mukaddis a halin yanzu rashin haduwa a zauna tsintsiya madaurinki daya kowa na cin mutuncin mu saboda yadda kowa ya sanya gabansa inda yake so.

Duba yadda Allah ya arzuta kasashen musulmi da man fetir da albarkatun kasa wanda duniya ke so, amma an wayi gari wahala ta shigo, ra’ayin kafirta juna ya sa kowa cikin cikin matsala, alhali a baya hatta kiristoci idan kirsimeti ta zo sukan kai wa musulmi abinci su ma Musulmi idan sallah ta zo za su kai wa kirista abinci ana zaman tare ba matsala, amma yanzu hatta tsakanin musulmi sai wani ya rungumi bom ya shiga masallaci ya kashe dan uwansa da nufin akidar su ba daya ba ba ya son ganin sa a duniya to yaushe za mu ci gaba.Yau wannan ya kafirta wannan wancan gobe ya kafirta dan uwansa kuma Allah ya yi umarnin ayi riko da igiyar Allah kar a rarraba, saboda yawan rabuwa shi ke sa yau a cinyen wannan musulmi gobe a yaki wancan a cinye shi kullum ana tsangwaman mutane saboda son zuciya.

Don haka a kullum muna kokarine don cirewa matasa wannan akida ta kafirta juna ko kasha juna da makamantan su don su rungumi zaman tare a zauna da juna lafiya a gina al’umma a ciyar musulunci da musulmi da kasa gaba.

 


Advertisement
Click to comment

labarai