Connect with us

LABARAI

Ta Kwara Wa Saurayinta Ruwan Zafi A Dalilin Sulhunta Ta Da Kawayenta

Published

on


Wata budurwa ‘yar makaranta Odinke SylbeSter mai dalibta a makarantar koyon aikin jinya ta garin Kalaba jihar Kurosriba ta kwara wa saurayinta tafasasshen ruwa wanda ya ke shi ne shugaban kungiyar daliban wannan makarantar koyon jinyar Ethoti Uno.

Wannan lamarin ya faru ne a lokacin da shi Ethoti ya je ma ta a matsayin mai sulhunta tsakaninta da wasu abokanta daliban makarantar samun horon sanin makamar aiki da ke a karamar hukumar Biase.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, shugaban makarantar Adat Adat Obona ya ce, shi dai wannan shugaban daliban ya halarci inda a ke ba su horo kan sanin makamar aiki kuma ba don ko me ba ya kai shi illa kawai saboda a matsayinsa shugaban daliban da ya samu labarin takun saka da ke tsakanin ita Odinke da abokiyarta, Ono Obonno, da sauran abokan tarayyarta na aiki domin ya shiga tsakani ya ga ya sulhuntasu abu na biyu kuma ya na so ne ya ja mu su kunne game da batun yin amfani da kayan maye.

Amma bai san cewa ta shirya ma sa wata mugunta ba, inda ta tafasa ruwa hade da garin barkono da gishiri a ciki babu wanda ya sani kawai ta je ta dauko wannan ruwan ta zo ta watsa ma sa daga sama har kasa jikinsa gaba daya ya sabule sakamakon ruwan zafin.

A yanzu haka an kai shi ,asibiti ita kuma wacce a e zargin, kamar yadda mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta ce, ta na hannun ’yan sanda kuma su na kokarin yin binceke a kanta.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai