Connect with us

LABARAI

Kungiyar ’Yan Arewa Ta Otto Ta Cika Shekara Biyu Da Kafuwa

Published

on


Alhaji Bala Muhammed ya yi bayani akan makasudin kafa kungiyar yan Arewa ta otto kamar haka yace lallai babu shakka makasudinmu da kafa wannan kungiyar ‘yan Arewa ta otto shine domin samarwa alummanmu hadin kai da ci gaba ta hanyar taimakon kai da kai da tallafwa mabukata daga cikin alumman yankin.

Shugaban ya yi wannan furuci ne ayayin da ‘ya’yan kungiyar suke gudanar da bukin cika shekara biyu da kafuwa ayankin yace ‘’mun kafa wanna kungiyar da mutane guda goma kacal acikin watan Octoba shekara ta dubu biyu da goma sha biyar mun yi hakan ne da nufin samar da hadin kan alummar arewa mazauna yankin otto da taimakon juna tsakaninmu.

Shugaban kungiyar Alhaji BalaMuhammed ya ci gaba da bayanin ce wa“A yanzu haka akwai mata zaurawa da suka rasa mazajensu sun mutu sun barsu da yara kanana don haka yana acikin manufar kungiyar tana shirin tallafa musu tare da daukan musu nauyin karatun wadannan yara marayu dake gabansu sannan muna aikin gayya wanda aka sani abangaren gyara amakabartu da kuma masallatai da sauran haka kuma acikin abinda muka sa agaba shi ne shirin sayen mutar daukan gawa ko marasa lafiya zuwa wurin magani (asibiti).

Sai ya karkare da bayanin dalilin shirya bukin cika kungiyar shekara biyu da suka kafata Dalilin shirya wannan bikin shine domin mu bayyanawa jama’a irin nasarori da ci gaba da muka samu acikin wadannan shekaru biyun kuma muna da niyyar fadadata zuwa sassa daban daban anan jihar legos da kewayanta domin ganin lokaci ya yi da ya kamata alummarmu su farka daga barci domin su yi wa kansu abinda zai samar musu ci gaba da zaman lafiya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai