Connect with us

MANYAN LABARAI

A Karon Farko El-Zakzaky Ya Bayyana A Bainar Jama’a

Published

on


A jiya Asabar 13 ga Janair, 2018, ne hukumar tsaro ta DSS da ta bai wa jagoran kungiyar ’yan uwa Musulmai, wacce a ka fi kira da Shi’a a Nijeriya, wato Sheikh Ibraheem Zakzaky, damar yin hira da manema labarai tun bayan kama shi da sojoji su ka yi inda daga bisani kuma su ka mika shi ga hannun DSS din wadda har zuwa yanzu Zakzaky na tsare a hannunta.

A lokacin da Malam Zakzaky ke ganawa da manema labaran, ya bayyana cewar ya na samun sauki a jikinsa sakamakon bayar da dama ga likitansa ya duba shi biyo bayan tsananin da jikinsa ya yi wadda har rabin jikin malamin ya daina aiki.

A ’yan kwanakin nan dai malamin ya yi fama da matsanancin rashin lafiya a sakamakon hawa da jininsa ya yi, wadda ya ke haurawa fiye da kimar da likitoci ke da bukata, hakan na faruwa ne sakamakon matsalolin da malamin ke ciki.

A ganawar tasa, Sheikh Al-Zakzaky, ya gode wa ’yan Nijeriya bisa addu’o’in da su ka yi ta yi ma sa da kuma wacce su ke ci gaba da yi  ma sa. Ya bayyana cewar ya samu lalurar shanyewar barin jikinsa tun a ranar Juma’a 5 ga Junairun 2018 biyo bayan tsananin da jikinsa ya yi, inda ya ce, jikinsa ya yi matukar tsanani ne a ranar Litinin din da ta gabata, amma yanzu ya na samun sauki.

Ta bakin Sheikh Zakzaky “jikina ya tsananta a ranar Litinin din nan, amma jami’an tsaro sun ba ni dama likitana (nawa na kaina) ya duba ni, kafin nan likitan su jami’an tsaron ne ke duba lafiyata, amma sun ba ni dama nawa likitan ya duba ni. Alhamdullahi Ina godiya ga Allah; yanzu Ina cigaba da samun sauki.”

 

Ga wani barin yadda ganawarsa ta kasance da ‘yan jarida:

 

’Yan jarida: Barka da rana? Ko za ka iya ganawa da mu?

Sheikh Zakzaky: Idan sun amince kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha).

 

’Yan Jarida: Wane hali ka ke ciki?

‘Sheikh Zakzaky: Na samu shanyewar barin jiki a ranar Juma’a 5 ga watan Janairun bana. Jikin ya yi tsanani ranar Litinin, amma daga baya jikin na samun sauki.

 

‘Yan jarida: Yaya ka ke ji yanzu haka?

Sheikh Zakzaky: Ina cigaba da samun sauki. Jami’an tsaro sun bari na gana da likitana na kaina. Da can likitansu ne ke duba ni, amma yanzu nawa likitan ya duba ni. Ina godiya ga Allah. Ina cigaba da samun sauki.

 

’Yan jarida: Ka na da wani abu da za ka kara cewa?

Sheikh Zakzaky: Ina godiya ga addu’o’inku.

 

‘Yan jarida: Mun gode

Sheikh Zakzaky: Na gode.

 

Wannan ganawar Zakzaky da manema labarai ta zo babu zato babu tsammani ga ’yan Nijeriya, sai dai wasu na ganin hakan na zuwa ne a bisa dalilai biyu. Dalilin farko shi ne jerin zanga-zangar neman a sake Zakzaky na tsawon kwanaki biyar wadda mabiyansa su ka yi ta yi a cikin birnin tarayyya Abuja tun ranar Litinin din da ta gaba. Wannan zanga-zangar ta bijiro da abubuwa da yawa a tsakanin ’yan sandan Nijeriya da kuma mabiyan malamin.

Dalili na biyu da manazarta ke gani kuma shi ne domin karyata jita-jitar da wasu kafafen sadarwar zamani su ka yada na cewar Sheikh Zakzaky ya mutu a hannun DSS.

Shi dai jagoran ’yan uwa Musulmai wanda a ka fi sani da Shi’a ya kansace a tsare ne tun bayan wani rikici da ya afku a tsakanin mabiyansa da sojojin Nijeriya a cibiyarsa da ya ke koyarwa, wato Hussainiyya, da ke Zariya a watan Disamban 2015. Tun wannan lokacin ne kuma jami’an tsaro su ke ci gaba da tsare shi bayan da sojoji su ka kama shi a gidansa da ke Gyallesu biyo bayan fafatawa a tsakanin sojoji da mabiyansa.

Idan dai ba ku mance ba, wata kotun Nijeriya ta bayyar da umurnin a saki malamin da kuma umurnin a biya shi diyya da shi da mai dakinsa, Malama Zeenatudden Ibraheem, amma har zuwa yau DSS ba su sake shi ba.

Kotun dai ta bukaci a saki Zakzaky kasa da kwanaki 45 ba tare da wani sharadi ba.

Alkalin kotun Kolawale Gabriel shi ne ya yanke hukuncin da cewar  tsarewar da hukumomi ke cigaba da yi wa Zakzaky tun watan Disamban 2015 haramtacciya ce kuma ba ta da hujja a karkashin dokokin kasar Nijeriya.

Haka ma ya umarci hukumomin da su biya shi da matarsa kudi Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa na tsare sun da a ka yi a haramcen hanya.

Lamarin tsare shehin malamin dai ya jima ya na daukar hankali tun bayan kama shi da jami’an tsaron su ka yi. Shi dai Zakzaky ya jima ya na da’awarsa da kuma cigaba da koyarwar, lamarin da kuma ke tsananta ma sa mabiya da kuma masu kushe da’awarsa.

A gefe guda kuma dai, cikin jerin zanga-zangar da mabiyan malamin su ka yi ta yi a birnin tarayya Abuja na tsawon kwana biyar da cewar a sake shi domin ya je ya gana da likita. Haka kuma wasu sun ce za su cigaba da fadi-tashi har sai an sako shi, domin cigaba da tsare shi da a ke yi ba bisa ka’ida ba ne.

LEADERSHIP A Yau LAHADI ta labarto cewar, yanzu haka dai wannan ganawar Zakzaky da manema labarai ita ce ta zama zancen da ta dauke hankulan jama’ar Nijeriya, domin kuwa jama’a da dama sun jima su na ta sake-saken abubuwa daban-daban a kan lafiyarsa da kuma yanayin da ya ke ciki.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai