Connect with us

LABARAI

Dilolin Miyagun Kwayoyi Na Neman Fin Karfin NDLEA A Kotu — Dr. Abdul

Published

on


Ayyukan hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, a jihar Bauchi na gamuwa da cikas musamman ganin yadda a ke amfani da matasa a hidimomin siyasa ta hanyar bude mu su ofisoshi su na kide-kiden kamfen da shaye-shaye a cikin birane da yankunan karkara, bugu da kari kuma da yadda NDLEA din ke fuskantar koma-baya a kotuna bisa yadda dilolin miyagun kwayoyi ke kalubalantar hukumar.

Wakilinmu, MUAZU HARDAWA, ya tattauna da DOKTA (BAR.) IBRAHIM ABDUL, kwamandan NDLEA na Jihar Bauchi, don jin irin yadda wannan aiki ke gudana. Ga yadda hirar su ta kasance:

Yaya za ka bayyana ma na yadda aikinku ke gudana na dakile tu’ammali da miyagun kyayoyi, musamman tsakanin mata da matasa a Jihar Bauchi?

Gaskiya wannan matsala ta tu’ammali da kyayoyi a tsakanin matan aure ko yara

matasan ‘yan mata babban al’amarine, domin da maza kurum aka sani ke shaye-shaye, amma yanzu idan an samu namiji daya za a iya samun mata hudu musamman a wasu jihohi irin su Kano amma nan Bauchi akwai sauki.

Kuma hakan na faruwane saboda tsananin talauci wanda ke sa matan son yin ayyuka na neman kudi ba tare da sun gajiya ba, ko kuma shiga cikin damuwa tsakanin su da mazaje ko yara ko abokan zama sai a bukaci shan magani don a yi barci ko kawar da damuwa da makamantan su alhali ba a san shan irin magungunan ill ace babba ga rayuwa ba domin ba ana sha ne da umarnin likita ba. Don haka idan an fara sha gobe an ji baya amfani kamar jiya sai a kara yawan kwayar ko kuma a sake maganin da ya fi wanda aka sha jiya karfi da haka har sai mutum ya zama dan kwaya daga nan sai kai wa ga fita daga hayyaci ko aikata abubuwa da suka saba da hankali sai lalacewa.

 

Kasancewar ka masanin doka, shin babu wata doka da ta hana aiki da irin wadannan kwayoyi ne ko sayar da su menene tanadin doka a kai?

Abin da ya haifar da wannan shi ne dokar da ta kafa wannan hukuma bata yi wani tanadin doka don hana sayar da irin wadannan kwayoyiba, saboda magunguna ne da likita ke rubutawa mutane su sha su warke daga cututtuka kamar su tramadol ana rubutawa masu cutar sicle aneamia, idan mutum na tari zai sha maganin tari koflin ko benelin da sauran magungunan tari duk a na sha bisa ka’ida cokali daya ko biyu a warke. Amma sai matasa suka gano idan ansha ya wuce kima a na buguwa a fita a hayyaci don haka sai mutum ya shanye kwalba daya ko biyu ko fiye a lokaci guda sai ya samu buguwa ko gamsuwa kamar ya sha hodar iblis ta koken. Don haka zai iya rashin mutunci ko aikata duk wani laifi domin ya fita a hayyacin sa ji yake shi ya fi kowa kuma ba wanda ya kaishi. Haka idan mutum ya sha kwaya fiye da kima zai fita a hayyacinsa wani lokaci idan mun kama su cewa suke yi ji suke kamar sun zama sarki saboda tambele da fita a hayyaci.

Matasa sun gane idan sun sha ba bisa ka’ida ba suka yi hade-hade  sun kirkiro za su ji kamar sun sha koken,  duk da cewa magungunan suna da illa ta wannan hanya amma suna da fa’ida wajen warkar da cuta haka kuma dokar da ta kirkiro wannan hukuma doka ta 11 da ta 19 da 20 bata hana amfani da magungunan ba kamar su rocha su tramadol su eddol  ba dokar da ta hana aiki da su don nan ba koken saboda rashin kudi, shi ya sa mutane suke kirkiro nasu hanyoyin.  Dokar ta ce idan an kama mutum da koken da heron ko sld da sauransu  ne kawai ga hukunci, amma ba ta yi magana kan irin wadannan magunguna ba,  don haka idan mun kama su muka kai kotu sai ya zamanto idan suna da lauya mai kyau sai ya ce ai babu wata doka da ta hana amfani da irin wadannan magunguna, wasu alkalan kuma sun fi son ganin dokar da ta fito da hani karara kafin su yi hukunci ballantana kuma ga yadda wasu alkalan yau suka kasance cin hanci ya shiga jikin su.

Don haka idan muka gaza bayar da shaidar cewa wadannan magunguna daidai suke da koken wajen illa to dole sai alkali ya salami mutum saboda lauya ya nuna yaya za a ce tramadol daidai yake da koken alkalan suna son ganin komai a fili ba irin su icd da aka hana hana sayar da su ba. Amma wadancan magunguna an musu ka’idar ba a iya sayar da su sai da takardar likita a nan kasar amma ba a hana su kamar yadda aka hana su koken da icd ba. Kuma duk da haka don mu temaki jama’a mukan fita doka mu kama mutum mu ajiye shi mu masa tarbiyya saboda dokar da ta kirkiro NDLEA ta bamu damar mu yi wa irin wadannan mutane tarbiyya.

Don hakan idan na kama mutum sai na ce tarbiyya nake masa. Idan ba haka ba kullum muna kama su kuma kullum suna kaimu kotu yanzu haka akwai kotun da aka kaini ake neman na biya naira milyan dari da hamsin da cewar wai na kama mutum ba bisa ka’ida ba kullum matsalar da mu ke ciki kenan ace mun tauye hakki mun kama mutum ba bisa ka’ida ba don haka sai ko na ce ina yiwa mutum tarbiyya ne kafin na samu sauki, duk inda na je aiki sai an kai ni kotu haka muke ta bugawa tun daga cikin Bauchi unguwar bayan gari zuwa wajen Bauchi na rufe shagunan magani sun fi saba’in kuma haka suke kaini kotu muke ta bugawa duk domin mu taimaki masu tasowa domin ganin basu samu kansu a wannan hanya ta shaye-shaye ba don haka kullum kamasu muke yi mu ajiye haka kullum karar mu suke yi kuma sai an samu sauki mu saki mutum.

Kashi cas’in na masu sayar da magungunan suna kotu daga inda suke beli amma saboda sashi na 150 da 35 na tsarin mulki da 158 duk sun bayar da damar ba da beli duk sai a bayar da belin su to yaya za mu yi da hukuncin kotu. Amma saboda mutane basu sani ba sai su je suna zage-zage suna cewa mun rufe chemis alhali yawan kwaya ko maganin tarin da ke ciki ya fi karfin na magani sai na sayarwa matasa su sha su yi tambele, haka kuma wasu idan sun ga mun kama mun kai kotu sai a sake sai su bayan haka rika zagin mu wasu har masallaci za su je su hau lasifika su ce bama aikin mu yara sun dame su mun kama an yi halin ko in kula an saki mutum alhali ba a san irin halin da muke ciki ba na gaba kura baya siyaki.

Bayan haka kuma tunda na zo wannan ofis ba wani kudi da gwamnatin tarayya ke bayarwa na azo a gani,  ko tallafi daga gwamnatin jiha domin lura da wadanda muke kamawa sai ko mu ke neman abin da za mu ciyar da su a aljifunmu duk domin kar a ce bama aikin mu. Idan an bayar da kudin kuma baya isa don haka ya kamata a ce gwamnatin jiha ta taimake mu domin tunda muka zo gwamnatin jiha bata taba temakon mu ba ko sau daya idan akwai mai ja kan wannan korafi sai ya fada mu ji.

Mutum bai isa ya hana fashi da makami ko aikata manyan laifuka ba sai ya datse hanyar tu’ammali da kayan maye saboda sai sun fita a hayyacin su suke aikata kowane irin laifi.

 

Yaya ka nazarci irin yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa suke bude musu ofisoshi a unguwanni ko kan titi suna shaye shaye da kide kide?

Wannan babban al’amarine saboda duk shugaban da zai tara matasa waje guda ya basu kayan maye su sha su rika sanya kida suna tambele suna damun mutane ba alheri cikin lamarin, kuma a kullum muna samun koke daga mutanen irin wadannan wurare saboda yadda suke damunsu da karar sauti da shaye shaye wani lokaci har tsare hanya suna rashin mutunci ko karbewa mutane kaya da makamanta su abin ba dadi yadda ake fada don haka ba zamu bar mutane su ci gaba da daukar doka a hannun su suna rashin mutunci ba dole muna shiga cikin lamarin saboda akwai dangantaka tsakanin shan kyaya da aikata laifuka.

Kuma masu mulki suna irin wannan abin yaushe za su temaki jama’a don haka kullum sai mun kama su mun danne su mun cire kayan mayen a jikin su ko tabar wiwi ko maganin tari ko makamai wanima idan mun kama shi sai ya hadiye tabar wiwi, don haka idan mun kama su kullum sai yan siyasar sun zo beli amma ni ba ruwana sai su samu ma’aikatan ni bana damuwa da lamarin su tun da ko gidan gwamnati bana zuwa kuma bana neman wani abu wajen su tunda dama ba taimakon mu suke yi ba.

 

Wace hanya kake gani za a bi don rage shaye shaye a tsakanin mata?

Mutane su jawo masu wannan harka ta kwaya kusa da su kada su guje su, domin irin wadannan mata ba kowa ya ke sanin su na sha ba, saboda wasu bacin rai ke sa su irin wannan shaye-shaye wata kishiya aka mata wata an sauyawa mijinta wajen aiki an kaishi nesa ba ta iya barci sai ta sha kwaya saboda sun saba suna tare wasu kuma rashi ke damun su ko talauci ko damuwar kishiya to ta yara ana so a yi babu hali kuma an kasa hakuri da rashin da Allah ya kawo. Wata kuma tsabar fitinar mijinta ko damuwar rashin aure ko damuwar gidan miji duk sune irin matsalolin da wani lokaci matan hatta barci basa iyawa sai sun sha magani daga haka kullum ana kara yawan maganin ko ana sake wanda ya fi karfi da haka har lamarin sai ya zamo jiki idan ba a shaba babu zama lafiya.

 

Shin shan miyagun kwayoyi yana raguwa ne ko yana karuwa a jihar Bauchi?

A gaskiya zan gaya maka babu yaudara tsakanin mu tunda gwamnati ba damuwa ta yi a magance ba don haka lamarin karuwa ya ke yi, muna tubka ana warwarewa saboda yanzu siyasa ake ciki kuma matasa kullum karuwa suke yi babu aikin yi don haka ake amfani da su a na ba su kayan maye suna rashin mutunci, koda ba a fili ba kudin da a ke ba su yawanci an sani wata tsiyar sai sun sha mugun abu su aikata. Don haka su ke rashin mutunci wa juna tare da yin abin da suka ga dama, domin ko an kama su madadin su bar hukuma ta yi aikinta a koyawa yaro sanin darajar kansa da ta jama’a, yanzu hukuma za ta kama yaro da laifi jimawa za ka ji manya sonata kiran a sake shi to ka ga ba cigaba a wannan lamari, domin ko an sake shi zai ci gaba da aikata laifin da ya ke yi ne. Kuma bama samun temako duk wannan aiki mota uku kurum muke da shi don aiki duk wannan shiyya.

Nan iyaye za su kawo yaran su suna son kashe su mu kuma mu rike musu yaran don kada su kashe su, amma babu wani temako da gwamnati ke mana yawanci kamar ni da ke fita wasu kasashe na yi aikin lacca da makamantansu na samu kudi wani lokaci da zarar na dawo na iske babu abinci haka zan cire na saya don ciyar da wadanda muka tsare. Kuma yawancin jihohi wannan hukuma na cikin kwamitin tsaro amma banda Bauchi, suna aiki da ‘yan sanda da soja da sauran jami’an tsaro amma banda hukumar NDLEA. Haka idan gwamnati za ta bayar da tallafin motoci ko kayan aiki ba a bamu sai soja da ‘yan sanda alhali mu ke taka rawar gani wajen mu’amala da manyan masu aikata laifuka.

Mutane su sani muna temakon jama’a ne don haka mutane su bamu goyon baya musamman ganin yadda idan mun fita aiki kauyuka sai mutanen wurin su fito da adda wai za su yake mu alhali muna rike da manyan bindigogin mashingan mai sarrafa kanta. Idan tsautsayi ya ratsa mun ga za su mana illa mun harbi mutum ace mun yi kisa shike nan ma’aikaci ya shiga damuwa iyalansa suma haka. Idan kuma sune suka yi galba a kan mu suka kashe mana mutum iyayensa da iyalensa sun yi asara ko an je an kama mutane kwana kadan an karbe su sun fito sun ci gaba da rayuwa.

Don haka ya kamata mutane su dauke mu a zaman abokan aiki ba abokan gaba ba. Idan mun je wuri a taya mu aiki mu kama mai laifi mu raba su da masu lalata musu yaransu. Kuma duk wanda muka kama idan bamu same shi da laifi ba za mu sake shi, haka kuma duk wanda aka ga mun kama, to muna da tabbacin illar da ya ke wa al’umma domin yawanci masu kishi ke sanar da mu halin da ake ciki. Kuma sai mun je mun bincika mun tabbatar kafin mu kawo hari wajen mu kama mutum. Kuma lokacin da mu ke bincikawa babu wanda ya sani haka muke aiki da basirar da aka koya mana kafin mu kai ga kama mutum don haka muna son mutane su bamu goyon baya da fatar Allah ya temake mu, amin. Na gode.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai