Connect with us

KASASHEN WAJE

Ban Yi Kalaman Batanci Ga Afrika Ba —Shugaba Trump

Published

on


Rahotannin baya-bayan nan sun ce Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta yin amfani da Kalaman cin zarafi wajen suffanta nahiyar Afrika da kuma kasar Haiti.

Sai dai Trump ya jaddada sukar da ya ke yi wa shirin majalisar dattawan kasar, na amincewa da wata dokar shige da fice, da za ta tilasta wa Amurka karbar ‘yan ci rani daga kasashen da ya ce suna fama da talauci.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya, da Kungiyar Tarayyar Afrika, da gwamnatin Haiti, da ma sauran kasashe, suka yi tur da kalaman na wulakanci, da suka bayyana su kai tsaye da cewa na nuna wariya ne, wadanda wasu kafofin yada labarai suka nuna Trump din ya furta, a lokacin da ya jagoranci wani taro kan shige da ficen baki ‘yan ci rani a fadar White House.

Yayin da yake kare kansa a shafinsa na twitter, Trump ya musanta furta kalamai na kamanta ‘yan kasar ta Haiti da kuma al’ummar nahiyar Afrika a matsayin kazamai, a cewarsa ya dai bayyana su ne a matsayin matalauta wadanda gwamnatocinsu ba su da alkibla.

Wasu rahotannin kuma na nuni da yawan mai da wa Shugaban martani game da wadannan kalamai da aka ce ya jefi baki ‘yan cirani daga wasu kasashen da aka ce ya kira su da kwatankwacin ‘Ramin Masai’.

Donald Trump ya bawa ‘yan majalisun Amurka mamaki yayin da ake zaman tattaunawa kan maganar baki a ranar Alhamis, in da aka ba da rahoton ya kira kasar Haiti da wasu kasashen Afirka da “Ramin Masai”.

Kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito ciki har da Jaridar Washington Post da New York Times da kuma gidan talbijin na CNN.

Shugaban ya yi tambayar “Me ya sa ake maganar wadannan mutanen da suka fito daga kasashen da suke kamar Ramukan Masai?”

Trump ya ce, me ya sa Amurka ba za ta dinga kyale mutane masu yawa daga kasashe irinsu Norway su dinga shigo wa Amurka ba, maimakon wasu mutane daban.

A Larabar da ta gabata ne dai Fira Ministar kasar ta Norway ta ziyarci Amurka, tare da ganawa a fadar gwamnati ta White House.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai