Connect with us

LABARAI

Sarkin Itatuwan Bauchi Ya Yi Tir Da Ayyukan Masu Sare Itatuwa

Published

on


Sarkin Itatuwan Bauchi, Alhaji Abubakar Sadik Ladan Abdullahi ya yi kira da kakkausar murya ga daukacin jama’a, musamman masu saran itatuwa a dazukan masaurartar Bauchi da su guji yin hakan domin kare mutuncinsu.

Alhaji Abubakar Ladan Abdullahi da yake hira da manema labarai a garin Bauchi kwanakin baya, ya ce yi wa doka karan-tsaye ne a rinka saran itatuwa ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana cewar, saran itatuwa barkatai matsala ce da ke haddasa zaizayar kasa da kwararowar hamada, game da haddasa koma bayan tattalin arzikin fadin kasar Bauchi.

Sarkin Itatuwan na Bauchi ya kuma gode wa gwamnatin Jihar Bauchi da masarautar Bauchi dangane da kokarinsu da jajircewa bisa dashen itatuwa a sassa daban-daban na masarautar da Jihar baki daya domin yin kandagarki ga zaizayar kasa da kwararowar hamada.

Alhaji Abubakar Abdullahi ya kuma nuna jin dadinsa yadda hukumomi ke sa ido kan ayyukan marasa kishin kasa da ke sare itatuwa, tare da yi masu hukunce-hukunce masu tsanani ga wadanda suka aikata aika-aikar.

Ya kuma sake yin kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da suke taimaka wa masarautar da gwamnatin Bauchi da ka da su gajiya da kokarinsu na kare itatuwan da ke dazuka da ke samun barnan marasa kishin kasa.

“Yana kuma da kyau masu sana’ar sayar da itace su hada karfi da karfe da hukumomin gwamnati ta yadda za a rage sarar itatuwa barkatai a dazukan mu ba bisa ka’ida ba”. in ji shi

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai