Connect with us

LABARAI

Sadaukarwa Babbar Kariya Ce A Rayuwa — Shehu Namadi

Published

on


A cikin makon jiya ne wakilinmu ya sami zantawa da fitaccan dan siyasar nan Alhaji Shehu Namadi Samaru.

Wakilin namu ya sami zantawa da shi ne a yayin da ya halarci taron saukar karatun Alkura’ani da makarantar Arwatul Makarikul Islam ta shirya a Samaru Zariya, inda  bayan ya kammala jawabi na tunatar da wadanda ke da hannu da shuni kan su bayar da gudummawa wajen taimaka wa addini da kuma taimaka wa marasa karfi, sannan ya kara da cewa, sadaukar da dukiya na da matukar muhimmanci, wnda bayan ka yi sadaukar war za ka samu jin dadi a cikin zuciyarka.

Irin wanna nnatsuawar da yake samu c eke kara karfafaf masa gwiwa wajen ganin ya taimaka a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Sadaukarwa babbar kariya ce daga sharrin mutum da na aljani, saboda haka sai ya shawarci wadanda Allah ya hore wa da su dinga daure wa suna bayar da gudummawa. A karshe, ya bayar da gudmmawa mai tsoka ga wannan makaranta,wanda kuma ya bukaci a ci gaba da bayar da taimakon ko da bayan wannan taro ne, domin makarantar na bukatar taimako mai yawa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai