Connect with us

TATTAUNAWA

Mu Ke Tallafa Wa Kanmu A Cikin Kungiyarmu —Hajiya Murjanatu

Published

on


Batun sana’ar dogaro da kai a yau za a iya cewar matan aure da ‘yanmata da kuma matasa maza kalu-balen yau ya sa sun rungumi sana’o’i da hannu biyu, a dalilin kamfar ayyukan gwamnati na kananan hukumomi ko na jiha ko kuma na gwamnatin tarayya.

Wakilinmu BALARABE ABDULLAHI da ke Zariya ya yi gamon-katar da

shugabar mata a kungiyar UNGUWAR ALKALI NOMA DA KIWO, da ke birnin Zariya, HAJIYA MURJANU DANJUMA wadda ta amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi ma ta kan yadda suka kafa wannan kungiya ya zuwa aikace-aikacen  da suka sa a gaba da ya shafi samar wa mata da sana’o’in dogaro da kansu ko kuma dogara da sami damar warware wadannan matsaloli da suke fuskanta a tsakaninsu da mazansu. Ga dai yadda tattaunara ta kasance:

Da farko, za mu so jin tarihin kafuwar wannan kungiya?

Lallai mun kafa wannan kungiya shekara goma sha biyar da kafuwarta a nan Unguwar Alkali cikin birnin Zariya. Kuma mun fara tunanin kafa wannan kungiya ne a lokacin mu goma sha uku,amma a halin yanzu mu na da mambobi fiye da dari biyar maza da kuma mata.

 

Wane dalilai ne suka sa kuka hadu tun farko, domin kafa wannan kungiya?

A lokacin da muka fara zaman taro, abin da muka fara tattaunawa shi ne, wasu hanyoyi za mu bi mu tallafa wa kanmu, ba tare damun jira mazanmu ba, da haka muka dora tubalin tafiyarmu ya zuwa yau da za mu iya cewar, duk da wani karfi mu ke da shi ba, amma fa akwai kungiyoyi da suke koyi da wannan kungiya ta mu,na tsare-tsaren da suke sa muke samun nasara.

 

Me kuka fara sa wa a gaba da ku ka fara tafiya da sunan wannan kungiya?

Kamar yadda na fada ma ka a baya, mun kafa wannan kungiya da sunan tallafa wa juna ne da sauran mata da matasa maza, to da muka fara aiwatar da ayyukanmu, sai muka sa batun sana’an dogaro da kai shi ne a gabanmu, kuma mun fara da sa sana’o’in da suka hada da yin man shafawa da turaren da ake fesawa a daki da sabulu da kyandir, da dai sauransu.

 

To a lokacin da ku ka fara, wane hanyoyi ku ka bi, na samun kudaden da kuka sayi kayayyakin koyon sana’o’in da kuka sa a gaba?

Babu ko shakka ba mu nemi taimakon wani mutum ba,sai duk wanda zai shiga kungiyar,a kwai kudin ka’oda da kuma kudaden da mu ke tattara wa a ranar taro, sai kuma mu kanmu shugabanni mu na tatsar kanmu kudade da zarar wasu bukatu sun taso ta kowane bangare. Wato da wadannan kudade muke sayen kayayyakin da muke koyar da sana’o’in da na bayyana ma ka.

 

Ga wadanda za su shiga wannan kungiya, nawa suke biya?

Lallai muna da takardar da muka tanada ga duk wanda zai shiga wannan kungiya, wanda sai mai son shiga kungiya ya cika zai zama dan kungiya, mu ma fa duk wanda ko wadda muka ba wannan takarda ta shiga kungiya ne, mai son shiga kungiyar ba zai ba da ko kwabo ba. A cikin wannan fom wanda ya cika zai bayyana sana’ar da yake so ya koya, daga nan ne sai mutum ya fara zuwa cibiyar koyar da sana’ar ta mu, a fara koya masa wannan sana’a, da ya zaba a fom din da ya cika.

 

Su mazan da suka nuna son koyon sana’a, ya kuke yi da su?

Ga bangaren maza, musamman in sana’ar da suke so dunkin keke ne, mu kan dauke shi, mu kai shi shagon da ake dinkin keke, mu bayyana wa mai shagon cewar, wannan matashi da muka kawo maka, ba mu da kudin da za mu biya, ka ka koya masa dinkin keke, wasu na karbar yaran da muka kai musu ba tare da wani bata lokaci ba ba, wasu kuma su ce sai an biya su kudin da za su koya wa matasan da muka kai wajen koyon sana’ar,in mun ce ba mu da kudin wasu na karban yaran wasu kuma su juya ma na baya,ta haka dai muke yi har muka kawo yau da za mu iya cewar,matasa da yawa sun koyi sana’o’i a wannan kungiya tamu.

Kuma zuwa yanzu, mun sami ma su sana’o’in hannu da yawa da muka yi musu bayanin kungiyarmu, na rashin kudi, da zarar mun kai musu matasa suna daukarsu ba tare da an bata lokaci ba.

 

In matashi da kuma duk wanda ya kammala koyon sana’a, akwai wani tallafin ci gaba sana’a kuke ba su, domin su ci gaba da yin sana’ar da suka koya?

Duk da dazu na shaida ma ka ba mu da kudi, ba kuma samun wani tallafi daga wani ko kuma wasu,amma zan iya tunawa, Mai Shari’a marigayi Malam Saifullahi Muntaka Kumasie,mun je wajensa neman taimako ,kuma ya yi ma na tallafin da za mu taba mantawa das hi ba,kuma ya umurci mai yi ma sa gini, day a je inda mu ka fara ginin cibiyarmu,ya duba inda mu ka tsaya, ya ce zai kammala ma na ginin cibiyarmu da mu ka fara aikin ya tsaya cik.

To duk halin matsin da mu ke ciki,in mun yaye wasu yaranmu,mu na dan bas u wasu ‘yan kudin da zai kais u ina ba,domin su ci gaba yin sana’ar da aka koya ma su a wannan cibiya ta mu.Amma ka ga kamar wasu abubuwa da kayayyakin hada sub a shi da tsada,mu kan ba yaran ko kuma matan tallafi kyauta,domin su ci gaba da yin sana’ar da aka koya ma su, duk kudin da mu ka bas u kyauta ne ba za su dawo ma na da ko da kwabo ba.

 

Game da kiwo da kuma noma da kuke yi, wane tsokaci za ki yi mana kan wadannan abubuwa biyu?

To,bangaren noma da kiwo, mu shugabannin kungiya muke yi, in mun yi noma sai mu sayar, kudin da muka samu, sai mu sa a cikin cibiyarmu haka ma kiwo da zarar mun sayar da dabbobin da muka yi kiwo, abin da muka yi da kudin noma da shi za mu yi wannan kudi.

 

Kuna da wata alaka da wadanda kuka koya musu sana’o’i a shekarun baya?

Lallai ko muna da alaka mai kyau, wasu muna kirarsu su zo cibiyarmu, su koyar da sana’o’in da  muka koya musu ga sabbin da aka dauka, a wasu lokuta ma, in mun je wasu wurare muka hadu da suna girmama mu fiye da yadda kake tunani.

 

Zuwa yanzu, mene ne matsalolin wannan kungiya?

A gaskiya, wannan kungiya tana da matsaloli da yawa, amma muhimmai su ne, rashin ginannen cibiyarmu da za mu rika koyar da sana’o’i, sai kuma matsalar rashin ma su tallafa ma na da kayayyakin aiki da kuma kudi, a takaice wadanna su ne manyan matsalolinmu, da in har aka warware ma na su, za mu kara fadada ayyukan da mu ke yi a nan gaba na samar da sana’o’i ga matasa maza da mata da kuma matan aure a nan karamar hukumar Zariya da duk mai bukatar koyon sana’a a fadin jihar Kaduna.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai