Connect with us

TATTAUNAWA

Kujerar Gwamnan Kano A shekara ta 2019 ta Matasa ce —Baba Yawale

Published

on


Alhaji Abubakar Yawale dan takarar gwamna ma fi karancin shekaru, matashi dan gwagwarmaya, wanda suka jagoranci ta tawagar matasan da suka jajirce wajen tallata kyawawan manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari tun lokacin takararsa ta farko. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Baba Yawale ya bayyana takaicinsa bisa yadda wasu gwamnoni suka mayar da matasa gugar yasa, sannan kuma matashin ya tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamnan Kano a shekarar zabe mai zuwa. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Bari mu fara da jin sunan wanda muke tare da shi?

Alhamdulillahi ni dai sunana Abubakar Yawale wanda aka fi sani da Baba Yawale, na fara karatu firamare a Makarantar Sheikh Gwani Dan Zarga daga nan na wuce zuwa Golden Secondary School, sannan kuma na halarci makarantar horar da Malamai ta Gwamnatin Tarayya FCE a Kano inda na karanta ilimin lissafi da kididdiga (Accound anda Auditing).

 

Yi wa mai karatu tambihi kan gwargwarmayar siyasa da aka fafata a baya zuwa wannan lokaci?

Alhadulillahi ni na fara siyasa tun ina karamin yaro musamman yadda na ke da sha’awar siyasar, sannan a lokacin jam’iyyun DPN da UNCP na bayar da gudunmawa, Sai kuma lokacin wannan Jamhuriyyar da muke tun daga shekara ta 1998  na tsunduma dumudumu cikin harkokin siyasa. Kuma alhamdulillahi na yi tafiya da ‘yan takarkaru daban daban wanda na hudimtawa amma babu wani sakamako mai kyau da ya biyo baya. Kamar yadda muka fahimci suna hidimtawa ‘yan uwansu a siyance, idan anyi zabe su kan dauki mutanen da suke sha’awa don mu’aimilla dasu ta a gwamnatance ko a siyasance bayan ka gama yi masu wahaka.

 

A baya sunanka ya yi nisa wajen jagorancin al’amuran da suka shafi harkokin takarar Muhammadu Buhari, shin kenan ana iya cewa har yanzu akidar taku guda ce?

Ina tabbatar maka da cewa ni tare na ke da shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma shi na ke yi, shi kuma shi zan yi a shekara ta 2019. Kamar yadda aka sani ina daya daga cikin mutanen da suka fara yin kira Shugaba Muhammadu Buhari takara a shekara ta 2015 da kuma 2019 domin sake zama dan takara domin mutanen kasa su sake sahalle masa don ci gaba a zangon na biyu, wannan kuma ba don komai sai don a iya fahimtata shekara hudun nan ta yi masa kadan, kuma yana da kyakkyawan shiri na mayar da kasarnan ta dawo cikin hayyacinta domin fita daga cikin ukubar da ake ciki, shekara  dayan data rage tayi masa kadan saboda haka muke rokonsa da ya yi hakuri ya amsa wannan kira na al’ummar Najeriya domin ci gaba zuwa shekara ta 2023.

 

Mu dawo nan Gida Kano kiranye kiranye sun fara yawaita na cewa matasa irin su Baba Yawale ya kamata su fito takara a shekara ta 2019, shin ko me zaka ce kan haka?

Da farko a mataki na kasa ina ganin ba laifi bane idan mai girma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba, amma a matakin jihohi ya kamata a barwa matasa a basu dama suma su fito su nuna irin ta su kwarewar  da gogewa, idan ka kalli kasar nan kusan kashi 80% cikin dari na jama’ar Kasar nan matasa ne, suke tafiyar da al’amura na rayuwa sune a Kasuwa sune a wuraren ayyuka, sannan kuma sune dai ke fama da matsalar rashin aikin yi duk wata matsala da ka sani yanzu matasa ke sahun gaba wajen dandanar ukubar rayuwa. Wannan tasa ni ina matashi Allah ya bamu damar wadda mutane ke ta kiran na fito wannan takara kuma ace na zauna na watsawa matasan kasa a ido? Ai hakan bai dace ba.

Sakamakon danniya dana ga anayi a Jihar Kano mutane su zabeka kaki yi masu abinda suke bukata,  Jama’a sun yi ka alokacin da kake neman kuri’unsu amma daga baya ka juya masu baya, akan wannan tsari na ga ba daidani bane mutanen da suka zabeka sune kuma wadanda dandana rashin adalcinka, domin alkawari ka dauka tare da rantsuwa da alkur’ani idan kai Musulmi ne, shi kuma kirista ke rantsewa da Bible, banga dalilin da zai sa ace mu matasa mu kasa fitowa  domin bayar da tamu gudunmawar ba,  bayan Allah ya yi mana duk abinda mutum yake bukata, saboda haka dole yanzu lokaci ya yi da zamu fito mu nunawa duniya cewa azo ayi tafiyar nan damu, kasancewar kundin tsarin mulkin kasa ya bamu irin wannan dama ta tsayawa takara ya bamu dama mu fito a zabemu.

 

Kowane dan takara nada abubuwan da yake ganin idan Allah ya bashi wannan dama zai aiwatarwa jihar tasa, shin shi Baba Yawale wadanne abubuwa zai sa agaba idan ya zama Gwamnan Kano?

Kudurin da nake dashi ga al’ummar Kano da farko yi masu aiki a inda ya kamata da kuma gabatar masu da tsarin aikace aikace, ni ina da sha’awar wani abu da na ga wani Gwamna ya yiwa jiharsa kuma abin ya burgeni kwarai, daukar yara aiki kai su kasashen waje domin karin karatu da kuma samawa matasa ayyukanyi, ina da kyakkyawan fatan baiwa sarakuna dama amatsayinsu na iyayen kasa, duk abinda za kayi aduniya kashin bayanka Sarakuna ne, Za mu tabbatar da shigo da su cikin wannan tsari domin kaucewa mulkin mallaka da ake yi mana yanzu.

Duk wanda yasan arewa an san muna da tsari muna da shugabanci muna da ilimin rubutu da karatu haka Nasara suka iske al’ummar Arewacin Kasar nan, sannan muna saita yaran mu yadda zasu inganta rayuwarsu, saboda haka domin amfana da irin wadannan hikimomi na ke fatan shigo da sarakuna cikin Gwamnatinmu idan Allah ya tabbatar mana da ita.

Sannan kuma ina da kyakkyawa burin tallafawa mata kasancewa sune masu zabe sanann kuma sune masu rauni. Zaka tarar sunyi zabe amma abin mamaki dazarar anzo gabatar da wasu tsare tsare sai abarsu abaya, to ni ba zan bar wannan al’amari haka ba.

Sai kuma shirin da nake dashi na bujiro da abubuwan da zasu taba zukata da ruhin talakawan Jihar Kano, wanda na tabbata zai zama nasara da ci gaba a tsakanin al’ummar Jihar Kano, Sai sake fasalin shugabancin Jam’iyya domin itace uwar kowa ba zan bari a ci gaba kama karya ba, dole a mutunta shugabanci kuma idan mun samu wannan dama zamu tabbatar da cewa an dai na juya akalar jam’iyya daga wani wuri, jam’iyya ta kowa ce sannan kuma ita ya kamata ayiwa hidima. Duk abinda Jam’iyya ta kawo matukar na ci gaban Jihar Kano ne zamu tabbatar da ganin an aiwatar da shi, idan kuwa muka fahimci bashi da wani alfanu ko shakka za mu yi duk mau yiwuwa domin daidaita shi.

Siyasa ta lalace an tsaya ana yin abinda bashi ya kamata ayi ba matukar Allah ya bamu da ma bazan yarda da wannan ba, muyi abinda yake na gaskiya domin tafiya da al’umma wuri guda. Batun harkar lafiya na cikin abubuwan da na ke fatan baiwa muhimmancin gaske, ba zai yiwu ace asibitin Gwamnatin ace wai magani saye akeyi ba, ya kamata a bada magani kyauta wajen haihuwa ya zama komai kyauta  ne, dole a yiwa mata wannan domin duk wanda ka gani a duniya ta hanyar haihuwa aka sa me shi, dole mu kula da wannan domin ganin mun tallafa. Sai kuma  batun kasuwanni ba zamu yarda a ci gaha  da yiwa jama’a cunkushe ba, an matse kasuwa anyi abinda bai kamata ba, a gabatar masu da wani  abu da sunan taimako daga baya kuma  a wahalar da kananan ‘yan kasuwa, idan Allah ya bamu gwamnati ba za’ayi wannan ba.

 

Kamar yadda akwanakin baya ‘yan kasuwa suka gamu da ibtila’in gobara, kenan idan Allah ya baka wannan dama ‘yan kasuwa kowa zai samu tallafi gwargwadon iko?

Kamar yadda sauran Jihohin irin Borno, Yobe, Taraba da Adamawa abinda mutanen suka sani shi ne aikin gwamnati, amma mutanen Kano abinda suka yarda dashi kasuwanci, gobara ibtila’i ne daga Allah wajibi ne Gwamnati ta taimakawa wadannan mutanen, sannan a tsakanin ‘yan kasuwar akwai wanda yafi wani fuskanta asara mai yawa,  amma ba azo kana da jarin  Miliyoyin Naira azo adan tsakura ma wani abu ace kaje ka ja jari ba,  Magana ta gaskiya ni ba zanyi haka ba zanyi abinda ya kamata gwargwadon iko kowa ya amfana.

 

Jihar Kano da kake neman sahallewar al’umma domin zabar ka amatsayin Gwamna jihace da Jam’iyya APC ke rajin yin maslaha tsakanin masu irin wannan bukata, shin ko Ya kake kallon wannan tsari?

Ni zabe na fito kuma ban fito don neman wani Compromise  ba na fito takara a jam’iyyar APC ne kuma tare da mai girma Gwamna  na ke takara, kuma ina rokon Allah domin a wajen sa nake nema shi zai bani sannanina neman sahallewar mutanen Kano  domin su zabeni, idan su ka zabe ni amatsayina na matasahi zan kawo ci gaban da gwamnatin baya bata zo dashi ba, sannan zan duba aikace aikacen gwamnatin baya na alhairi in dora akai, zan kuma aje duk wani aiki da na tabbatar bashi da wani alfanu ga Jama’a domin kaucewa almubazzaranci da dukiyar Kanawa, Fatana Nasarar Jihar Kano da ci gaba Najeriya.

 

Ko ya baba Yawale yake Kallom makomar matasan da wasu ‘yan siyasa ke

amfani da su wajen biyan bukatar Kansu?

Babbar matsalar itace shaye shaye ba kuma komai ya ja haka ba sai rashin aikin yi, ina tabbatar maka da cewa mu zamu bari ayi amfani da matasa ta wata muguwar hanya ba, so muke musauya akalar siyasa ta koma siyasa mai tsafta kamar yadda kasashen da suka ci gaba ke gudanar da tsarin siyasar su ta yau da kullum.

 

Ya kake kallon irin rawar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na

Jihar Kano ya kamata ace ya taka musamman ganin gogaggen farfesa ne?

Kamar yadda aka sani a baya farfesa Jega ya gudanar da zabe na 2011 mutanen Najeriya basu gamsu da wannan zaben ba, ya zo ya yi na  2015 jama’a kowa ya yaba da yadda zaben ya gudana, saboda haka wannan lokacin muna kyautata zaton samun nagartaccen zabe da yardar Allah.

Saboda haka ina kira da babbar murya jam’a su tabbatar da zabar wanda suka tabbatar da sahihancin sa, kowa ya karkade kuri’arsa domin fitowa ranar zabe a zabemu muna fatan cikawa jama’a alkawarin da muka dauka, sannan kuma muna kara kira ga Jama’a a kara yiwa mai girma shugaban kasa addu’ar samun nasarar zaben mai zuwa.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai