Connect with us

LABARAI

Dokta  Shamsudeen Ya Zama Garkuwan Makarantar Zazzau

Published

on


A ranar Juma’ar da ta gabata, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya nada Dokta Shamsudeen Aliyu Mai Yasin matsayin Garkuwan Makarantan Zazzau.

A jawabinsa jim kadan bayan kammala nadin, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya umarci Garkuawan makarantan Zazzau da ya ci gaba da kyawawan halinsa da ya sa a gaba na ciyar da ilimi gaba, kamar yadda mahaifinsa Marigayi Shekh Aliyu Mai Yasin ya yi a tsawon rayuwarsa.

Mai martaba Sarkin Zazzau, ya kuma  tabbatar wa  Garkuwan cewar adar Zazzau za ta kasance a bude a gare shi, ta yadda zai sami kwarin gwiwar ci gaba da tallafa wa ilimi, kamar yadda ya saba shekaru da dama da suka gabata a masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya.

Kammala nadin ke da wuya, sai Garkuwan Dokta Shamsuddeen Aliyu Mai Yasin ya yi mubayi’a ga mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris da ke alamta Dokta Shamsuddeen Garkuwan makarantan Zazzau nuna gamsuwarsa da wannan nadi da mai martaba Sarkin Zazzau ya yi masa. Daga nan sai Garkuwan ya hau doki tare da ‘yan’uwa da abokan arzik na kusa da kuma na nesa, zuwa  gidan Garkuwan, domin saduwa da wasu al’umma da suka yi dafifi a gidansa, domin tarbarsa tare  da yi masa jinjina  kuma yi masa mubayi’a da shi ke nuna al’umma na tare da shi a wannan nadi da mai martaba Sarkin Zazzau ya yi masa.

A zantawarsa da wakilinmu bayan al’umma sun kammala yi masa mubayi’a, Garkuwan ya nuna matukar godiyarsa ga mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, na wannan nadi da ya yi masa, na.

Ya ci gaba da cewar, wannan dama da mai martaba Sarkin Zazzau ya ba shi, ya siffanta shi da wani kaimi da aka yi masa, da zai kara Yunkura wa, wajen ciyar da ilimi gaba, kamar yadda ya saba.

A dai bayaninsa ga wakilinmu, ya nuna jin dadinsa ga al’umma da kuma sauran manyan mutane da suka bayar da kowace irin gudummawa kafin da kuma lokutan wannan nadi da Alah ya tabbatar da shi.

An haifi Dokta Shamsuddeen Aliyu Mai yasin  Tudun wada Zariya, ya fara makarantar Allo a gaban mahaifinsa Marigayi Shekh Aliyu Mai Yasin, daga nan sai aka sa shi makarantar firamare ta Nurul Hudda,Tudun wadan Zariya, ya na kammala firamre sai ya sami shiga makarantar sakandare ta Alhuda-huda ta Zariya, daga nan bayan ya kammala, sai ya sami shiga Jami’ar Neelai wadda ke Sudan, bayan ya kammala sai ya sake shiga jami’ar African International Unibersity da ke Sudan, bayan ya kammala sai kuma ya sake samun shiga Jami’ar Bayero ta kano, yana kammala wa sai ya sake shiga Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato.

Shi dai Garkuwan, yana da digiri na uku kan magunguna, sai digirn girmamawa na Dokta da  Jamai’ar Jami’atul Islamiyya ta Katar ta ba shi  kan haddar Alkur’ani mai girma, sai digirinsa na biyu da ya samu a Jmi’ar Ghana, sai kuma difiloma kan kimiyyar hada magani, da kuma digiri kan  hada magani da ya samu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Mukaman da Garkuwan Makarantan Zazzau ke kai sun hada da shugaban  na kasa na kunguyar ilimantar da Musulmi da mataimakin shugaban kungiyar tallafa wa da sana’o’in dogaro da kai da shugaban hukumomin gudanarwa  na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Gwambe wanda ya kafa makarantun Farofesa Ango Abdullahi da kuma wasu makarantu da ya bude a jihar Katsina da Kogi da Kano da kuma jihar Zamfara.

Wannan nadin sarauta ta Garkuwan Makarantan Zazzau da mai martaba Sarkin Zazzau ya yi wa Dokta Shamsuddeen Aliyu Mai Yasin ya sami halartar mutane da suka fito daga sassan Nijeriya daban-daban.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai