Connect with us

NAZARI

Aikinmu Kare Rayuka Da Dukiyoyin Al’umma  — ABU CSO

Published

on


Tawagar wakilan jaridar Campus Herald da suka ziyarci Chief Security na jami’ar Ahmada Bello, Kanar Jibrin K. Tukur Mai ritaya, wadanda suka tattauna da shi a kan ayyukan da sashen sikuriti na jami’ar ya fi mayar da hankalinsa a kai, wanda kuma ya shaida musu cewa, babban aikin da sashin yake gudanarwa shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’ummar  ciki da wajen jami’ar. Ganin yadda tattauna wa take da muhimmanci, wadda kuma jama’a da dama za su amfana da ita, ya sa Editanmu Sabo Ahmada Kafin-Maiyaki ya fassara wannan tattauna wa wadda aka yi ta a Jaridar ta CAMPUS HERALD ta watan Satumba zuwa Disamba, daga harshen Ingilishi zuwa Hausa. Ga kuma yadda fassarar ta kasance:

Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

Sunana Kanar Jibrin K. Tukur mai ritaya. Na shiga makarantar koyar da manyan hafsoshin soja (NDA) da ke kaduna a shekara ta 1986. Na fita a matsayin hafsan soja, na kai matsayin Kanar, wanda daga nan ne na yi ritaya don kashin kaina. Na yi aiki a bangarori daban-daban na soja, wadanda suka hada da, 302 Mediun Artillery Regiment da 312 Artillery regiment (ECOMOG) da HK2 Dibision Ibadan da HK82 Dibision Enugu da Defence Intelligence Agency da kuma sashen tsare-tsare da kuma shirye-shirye a shalkwatar rundunar sojojin Nijeriya. Sannan kuma na halarci kwasa-kwasa da dama, haka kuma an tura ni kasahe irin su;  Tarayyar Turai da Amurka da  Parisa da Chana da Pakistan da Indiya da Rasha da sauran wasu kasashe. Haka kuma na yi karatuna a jami’ar Ahmadu Bello, inda na samu digirina na farko, sannan kuma na yi digirina na biyu a jami’ar Kalaba.

 

A matsayinka na Chief Sikuriti na wannan jami’ar, wadanne nasarori ka samu daga hawanka wannan mukami zuwa wannan lokaci?

Na samu nasarori masu yawa zuwana wannan jami’a, kamar  bayar da takardar shaidar mallakar abin hawa a kowane get, domin kawo karshen barayin motoci da suka addabi wannan jami’a a lokutan baya, da samar da katin shaida ga dukkan wanda ya kai shekara 18 yake zaune a jami’ar kuma yake yin aiki a waje da samar da katin shaida ga masu shaguna da yaransu, sannan kuma mun bayar da dama ga jami’an sikuriti da su karo ilimi wanda yakan kai wata 4 zuwa 6, sannan akan bayar da takardar shaida ga duk wanda ya kara karatu. Sannan mun gabatar da wani shiri na musamman da ake yi wa lakabi “WASA” wanda jami’an sikuriti ke gudanar da wasanni iri-iri inda kuma ake gayyato mutane domin su yi nishadantarwa, da kawo farin ciki da annashuwa.

Sanan mun samar da na’ura da ke binciken mutane wadda za ta iya gano in mutum ya dauko wani abin da zai cutar da jama’a ko zai yi barna, za ta tona asirinsa. Baya ga wannan akwai kyamarori a boye a kusurwoyi daban-daban na jami’ar. Sannan kuma shugaban jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Ibrahim Garba ya gyara mana motar zirga-zirga,  yadda jami’anmu ke shiga lungu da sako na jami’ar domin tabbatar da an samu cikakken tsaro.

Sannan mun samar da wayoyin hannu ga jami’anmu domin a samu cikakkiyar sadarwa a tsakani, yadda da zarar wani abu ya taso za a san halin da ake ciki. Misali, daga nan ina iya kiran jami’inmu da ke Kwalejin aikin gona da ke Kaba ko Mando ko Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello ko Kongo da sarauransu.

Sannan kuma, mun samar da sababbin unifom ga jami’anmu. Haka kuma lokacin da muke tirenin mun tsince tsofaffi da marasa lafiya wadanda ba za su iya ci gaba da aikin ba, mun kawo masu jini a jika wadanda za su yi aikin kamar yadda ya kamata.

Sannan daga cikin nasarorin da muka samu shi ne, na yin taransifa, domin yin transifa na sa ma’ikaci ya kara goge wa, saboda haka, mun yi amfani da wannan dama wajen yi wa jami’anmu taransifa yadda za su samu irin waccan kwarewar da ake bukata, musamman a matsayinsu na sikuriti.

A kokarin da muke yin a ci gaba da kare dukiyoyin jama’ar da ke hulda da wannan jami’a, bayan an karbi takardar shaidar mallakar abin hawa daga get din shigo wa, a kowane gurin ajiye motoci mun yi wani karamin get, yadda nan ma in mai mota zai shiga sai an ba shi takardar shaida, yada in ya tashi zai fito da abin hawansa zai bayar da wannan takarda wadda ke tabbatar da cewa, wannan motar ta sa ce. Haka kuma a ci gaba da kokarin kiyaye motocin da ke shigo wannan jami’a mun kafa dokar hana shigowar motocin masu gilas mai duhu. Abin da ya dada karfafa mana gwiwa wajen kafa dokar hana shigowar motocin masu duhun gilas shi ne, lokacin da na fara  aiki,  na shafe wata biyu cur ina kewaya harabar jami’ar a kowace rana tsakanin karfe 11:00nd zuwa karfe 2:00nd a lokacin na gano cewa, ana aikata wasu laifuka cikin irin wadannan motoci da ke da gilas mai duhu.

Haka kuma a kokarin tsafatace tare da tabbatar da ci gaba da rayuwar shuke-shuken da ke cikin wannan jami’a wadanda ke kara kawata ta, mun hana dabbobin makwabta shigo wa harabar wannan jami’a, mun kafa dokar cewar duk dabbar da aka kama a harabar jami’a, za a kama ta, mu rike ta har sai mai ita ya zo ya biya tara, sannan a yi masa gargadi a ba shi.

 

Ka yi ritaya daga aikin soja domin kashin kanka, domin ka ci gaba da wata sabuwar rayuwa, shin yanzu ka samu wannan biyan bukata kuwa?

Dangane da abin da na koya a aikin soja, sai in ce wannan aikin da nake yin a sikuriti kamar wani sabon abu ne, kodayake, suna da dangantaka da juna, domin dukkansu sun doru ne a kan  dole ka bi umarni. Saboda haka ne ma nake kokarin koyar da irin wannan dabi’a ta tabbatar da bin umarni a wannan bangare na sikuriti, sannan in tabbatar da samar da cikakkiyar  da’a a tsakanin sikuriti da kuma tsakaninsu da sauran al’ummar jami’a da samar da ilimi, sannan kuma ina koya musu yadda ya kamata su yi shiga wadda za ta kara musu kwarjini da mutunci a lokacin da suke bakin aikinsu.

 

Tun lokaci da ka fara aiki a wannan ofishi, a matsayinka na shugaban sashin sikuriti, wace gudummawa, wannan sashi ya bayar dangane da tabbatar da doka da oda a cikin harabar wannan jami’a?

Babban aikinmu shi ne, mu tabbatar da ana bin doka a cikin jami’a domin tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar wannan jami’a. Dalibai na da matukar muhimmanci a jami’a, domin dukkan rukunin mutanen da ke jami’ar suna zaune ne saboda dalibai, idan babu dalibai babu jami’a.

Saboda haka a sashin sikuriti akwai wani bangare da ke kula da tabbatar da zaman lafiya da kuma daidaita tsakanin dalibai idan an samu rashin fahimtar juna tsakanin dalibai ko ma’aikata, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da ke zaune a cikin wannan jami’a. Sannan kuma da tabbatar da cewa, an bi dukkan dokin da jami’a ta shimfida.

Tabbar da ID card ga dukkan al’ummar da ke wannan jami’a, wanda kuma yake da matukar muhimmanci.

Adana wasu kayan jama’a na dan wani lokaci, da kuma bai wa masu kaya kayansu lokacin da suka bukata. Mukan kwace kayan da ake zargin na sata ne, har sai an tabbatar da shaida in kuma wanda ake tuhumar bai iya kawo shaida ba, za a ci gaba da ajiye kayan har sai mai shi ya zo ya tabbatar da cewa na sa ne, ta hanyar bayar da cikakkiyar shaidar da za a gamsu da ita.

Sannan idan gobara ta tashi a cikin makaranta ko gidajen ma’aikata, muna da bangare na musamman da ke lura da irin wadannann  matsaloli wanda ke kawo karshenta kashe  gobarar da ta taso a cikin jami’a ko a gidajen ma’aikatan jami’ar.

Muna kuma hana aikata laifuka sannan kuma duk wanda aka kama da laifi, ana tabbatar da cewa, an yi masa hukunci gwargwadon laifin da aka kama shi da shi. Daga cikin ayyukan wannan sashi na sikuriti ke yi shi ne, mukan kasance a guraren taron da dalibai ko ma’aikata ko malaman jami’a suka shirya wa domin bayar da kariya, lokacin da ake yin irin wadannan taruka.

Haka kuma daga cikin aikin wannan sashi na sikuriti shi ne samar da sitika ga motoci da kuma takardar shaidar mallakar abin hawa in an shigo da shi cikin jami’a. Sannan muna kula za zirga-zirgar ababen hawa yadda ba za su cunkushe ba.

Haka kuma bisa hadin gwiwar sahin kula da lafiya na jami’a, muna tabbatar da cewa dukkan abincin da ake kawo wa cikin jami’ar ana sayarwa, mai tsafta ne kuma ba zai haifar da illa ba ga wadanda suka yi amfan dai shi ba.

Muna tabbatar da an samu kyakkyawan yanayin, ydda za gudanar da harkokin karatu da sauran al’amuran rayuwa a cikin wannan jami’a cikin walwala da kwanciyar hankali.

Sannann kuma duk lokacin da wata hatsaniya ta tashi a wajen jami’a, mukan kara daura damarar tabbatar da tsaron al’ummar da ke cikin wannan jami’a, yadda wani abu daga waje ba zai shigo mana cikin jami’ ba. Domin samun nasara aiwatar da dukkan wadannan abubuwa da na ambata, muna da bangarori irin su;  Bangaren masu faturu da masu bincike da masu lura tare da nazari a kan yadda harkoki ke gudana a cikin jami’a da masu tabbatar da doka na musamman da furobost da masu jiran ko-ta-kwana da ofishin da ke raba aiki da masu kula da abin hawa da masu daidaita sabani da ‘yan kwana-kwana da bangaren da ke kula da tirenin  da aikin gadi da sito da sashin kudi da sahin kula da manyan laifuka  da na bayar da ID card da kuma bangare da ke tabbatar da dukkan wadannan abubuwa na tafiya kamar yadda ya kamata.

 

Dalibai na korafin cewa, sikuriti na wulakanta su a get din shigo wa kan dokar sa sutura, ya ya wannan al’amarin yake?

Hukumar wannan jami’a ita ta kafa dokar sa sutura, saboda haka mu kuma babban aikinmu shi ne mu tabbatar an aiwatar da dokar. A kokarin ganin an aiwatar da dokar wani lokaci dalibai kan nuna bijerwarsu, har ta kai ga kalubalantar sikuriti kan mene ne dalilin da zai sa ya matsa musu, musamman dalibai mata wadanda su ne suka fi yawan karya wannan doka, wadanda ke bayyana tsiraicinsu. Saboda mu kuma mukan yi kokarin ganin an tabbatar da bin doka, wannan shi ne, ya sa watakila dalibai za su ga kamar ana ci musu mutunci.

 

ABU ita ce babbar jami’a a yakin sahara, wane albishir kake da shi ga jama’a na cewa duk da wannan girma na ta, akwai zaman lafiya a cikinta?

Gaskiya ne ABU ita tafi kowace jami’a girma a yankin sahara, ta fuskar fadin kasa da yawan jama’a, kuma ita ce kadai jami’ar da ta tattara jama’a daga kowane bangare na kasar nan.

Domin tabbatar da an samu zaman lafiya a wannan jami’a, muna da kusan sikuriti dubu uku wadanda ke kula da wannan jami’a domin tattabar da ci gaba da samun zaman lafiya. Sannan dukkanin wadannan sikuriti mun wadata su da kayan aiki, yadda za su gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata. Kuma kullum muna gargadin dalibai kan su guji dukkan wani abu da ya saba wa dokar wannan jami’a. Da  haka ne zaman lafiya ya tabbata a wannan jami’a.

 

An lura cewa, kullum yawan almajirai da masu tallace-tallace sai karu wa yake yi a wannan jami’a, wane abu kuke yi na ganin cewa, kun kawo karshen irin wadannan abubuwa?

Wannan wani aiki ne da sai an samu hadin kai tsakanin dalibai da sikuriti, domin ta haka ne za a magance wannan matsala, saboda haka ne zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga su dalibai da su sanar da sikuriti duk lokacin da suka ga masu talla ko masu bara a cikin wannan jami’a, don daukar matakin da ya dace.

 

Daliban da ke koyon akin jarida na kuka da sikuriti wajen hana su damar aiwatar da wasu abubuwa da suka shafi karatunsu musamman daukar hotuna lokacin da suke yin tirenin. Ko ka san da wannan?

E, gaskiyar maganar ita ce, ba ma hana dalibai yin duk wani abu da ya shafi harkokin karatunsu amma kamar abin da ya shafi daukar hotuna da makamantansu sai an rubuto takardar neman izini, mu kuma mu duba mu gani sannan mu amince. Saboda haka dukkan wani abu da za a yi amfani da harabar jami’a dole ne a nemi izini, mu kuma mu duba mu gani, in wanda ya kamata a yi ne sai mu amince, har ma muna iya tura jami’anmu su kula da jama’ar gurin.

 

Wadanne kalubale ka fuskanta zuwanka wannan guri?

Babban kalubalen da na fuskanta shi ne na tabbatar da mun kare iyakokin wannan jami’a, wanda saboda haka ne ma ya sa muka samar da hantas tare da ba su kayan aiki domin su tsare mana wadannan iyakoki, saboda a baya mun samu rahoton yadda wasu ke kutso wa daga waje su yi barna.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai