Connect with us

MAKALAR YAU

2019: Muna Bukatar Ta-zarce Tare Da Buhari – el-Rufa’i

Published

on


Gwamnonin Arewa bakwai sun hallara a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, inda bayan sun yi Sallar Jumma’a tare da Shugaba Buhari batun siyasa ya taso.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i ya bayyana wa manema labaru a fadar shugaban kasa cewa su Gwamnoni suna bukatar Shugaba Buhari ya sake tsayawa takarar neman wa’adi na biyu a zaben badi idan Allah ya kai mu.

Gwamnan ya kuma nunar da cewa galibinsu suna kan kuejrunsu ne a wa’adi na farko, don haka suna bukatar wa’adi na biyu ga kawunansu sannan suna son haka ga shugaban kasa.

Wanda ya bayyana cewa a kullu-yaumin Shugaba Buhari yana kara samun koshin lafiya, el’Rufa’i ya ce, “Mun yi amanna da shugaban kasa, muna so ya cigaba da shugabancin kasar nan a kyakkyawar turba. Mutane za su iya yada (abin da na fada) game da (zaben) 2019, ba za mu nemi afuwa ba kan haka.”

Da aka tambaye shi ko ba ya ganin ya yi riga-malam-masallaci kan abin da ya fada kuma mutane za su ga rashin dacewar abin? Gwamnan ya amsa da cewa, “Ko abin da mutane za su fada ya dace ko bai dace ba, ba shi ne muradi ba. Kowa yana da ‘yancin fadar ra’ayinsa amma a matsayin Gwamnoni, galibinmu a nan baya ga Gwamnan Yobe, muna wa’adin mulki na farko ne. Muna bukatar cigaba (tazarce) da kwanciyar hankali kuma shi shugaban kasa muna bukatar ya cigaba.

“Kamar yadda jagoranmu, Gwamnan Kano ya ce; haduwa kawai muka yi a nan (ba tare da wani ya san wani zai zo ba), mun je mun yi sallah kuma muka yanke shawarar taya shugaban kasa murna sannan mun gamsu cewa a duk lokacin da muka gan shi; yana kara samun koshin lafiya”.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da batun neman Shugaba Buhari ya tsaya takarar neman wa’adi na biyu ke fita daga bakin Gwamnonin ba, sun bayyana hakan a lokuta daban-daban a shekarar da ta gabata.

A nashi jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sun hallara a fadar shugaban kasa ne domin kai masa gaisuwar ban-girma. inda ya kara da cewa “Mu bakwai muka zo amma kowa shi kadai ya zo ba domin wani dalili ba, amma bayan mun yi sallah sai muka yanke shawarar mu kai gaisuwa ga shugaban kasa. Haduwa kawai aka yi a masallaci kuma wasu suka zo daga baya suka same mu shi ne muka yanke shawarar gaishe shi”, in ji shi.

Gwamnonin da suka ziyarci fadar shugaban kasan dai sun hada da Gwamnan Neja, Muhammed Abubakar da Gwamnan Yobe, Ibrahim Gaidam, da Gwamnan Kogi, Yahaya Bello da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow da kuma Gwamnan Filato, Simon Lalong.

Batun siyasar zabukan 2019 dai na kara nuna inda kowa a tsakanin ‘yan adawa da masu mulki ke fafe gorarsa don kar ya sha ruwansa da daci.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai