Connect with us

MANYAN LABARAI

Yadda Ta Kaya Tsakanin ‘Yanshi’a Da ‘Yansanda A Abuja

Published

on


Tun ranar Litinin 8 ga watan Janairun 2018, mabiyan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suka fara gabatar da wata zanga-zanga a Babban Birnin Tarayya.

Zanga-zangar wacce daruruwa suka gabatar da ita a ranar Litinin ta faro ne daga Sakatariyar Tarayya, inda suke tafiya suna rera taken ‘A saki Zakzaky’. Zanga-zangar tasu ta gamu da turjiya ne yayin da jami’an ‘yan sanda suka fara amfani da barkonon tsohuwa, inda har ya kai ga an watsa su.

Sai dai a ranar Talata 9 ga watan Janairun 2018, mabiyan na El-Zakzaky sun sake fitowa kwankwasu da kwarkwata, inda suka faro wata zanga-zangar daga Kasuwar Wuse dake tsakiyar garin Abuja, sai dai a wannan ranar ma, kafin su karasa shataletalen Berger, jami’an ‘yan sanda sun hallara, inda suka fara antaya barkonon tsohuwa, tare da kame na kamewa daga cikin masu zanga-zangar.

Zanga-zangar ta dau sabon samfuri ne a rana ta uku; ranar Laraba 10 ga watan Janairun 2018, inda ‘yan shi’ar suka faro jerin gwanon nasu daga UTC, suka zagaye manyan titunan dake wannan yankin. Sai dai a wannan rana, mabiyan na El-Zakzaky sun zargi ‘yan sanda da yin amfani da barkonon tsohuwa da harsashi akansu.

Daya daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar, Abdullahi Muhammad ya bayyanawa majiyarmu cewa; “Muna cikin tafiyarmu cikin tsari da natsuwa, inda muke jerin gwanon neman gwamnati ta bi umurnin kotu wurin sako mana jagoranmu. Kafin mu ankara, a daidai kasuwar ‘Area 1’ sai ‘yan sandan suka tare mu, suka fara harba mana barkonon tsohuwa, tare da harsasai masu rai. Mun yi asarar rayukan mutane biyu, tare da masu raunuka da dama.”

Sai dai rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa, ta dakile zanga-zangar ‘yan shi’ar ne saboda jerin ganon nasu barazana ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali. Rundunar ta fadi haka ne a wata takardar manema labarai da ta fitar jim kadan bayan tarwatsa zanga-zangar ta ranar Laraba.

Takardar ta ‘yan sanda ta ci gaba da cewa; “Muna so a fahimci cewa, abubuwan tsaba ka’ida da doka da ‘yan shi’a suka fara tun daga ranar Litinin 8 ga watan Janairun 2018, ya na haifar da fargaba da tsoro a zukatan al’ummar Babban Birnin Tarayya. A wasu lokutan ma suna hana jama’a gudanar da al’amuran rayuwarsu kamar yadda suka saba.” In ji su.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai