Connect with us

WASANNI

Wasan Nijeriya Da Ingila Ya Tabbata

Published

on


Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ingila, FA ta bayyana cewa ta amince da tayin da Nijeriya ta yi mata na buga wani wasan sada zumunci domin tunkarar wasan cin kofin duniya.

Tawagar kwallon kafar ta Ingila za ta buga wasan sada zumunta da ta Nijeriya a shirin da take yi na fafatawa a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.

Ingila na fatan yin wasa da Super Eagles ta Nijeriya ne a filin wasa na Wembley dake birnin Landan a ranar 2 ga watan Yuni na wannan shekarar da ake ciki

Haka kuma tawagar ta Ingila za ta yi wasan sada zumunta da tawagar ‘yanwasan kasar Costa Rica a Elland Road ranar 7 ga watan Yuni, sannan ta wuce zuwa kasar Rasha domin fara wasanni.

Ingila wadda mai koyarwa Gareth Southgate ke horar wa tana rukuni na bakwai da ya kunshi kasashen Tunisia da Panama da kuma kasar Belgium.

Nigeria kuwa tana rukuni na hudu da ke dauke da kasashen Argentina da Iceland da kuma Croatia.

Mai koyar da’yanwasan Najeriya, Gernot Rohr, ya bayyana cewa wasa da kasar Ingila zai taimakawa ‘yanwasansa da gofewa da kuma sannan yadda zasu tunkari manyan kasashe a kasar Rasha.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai