Connect with us

BIDIYO

TAURARIN NISHADI: Jakadancin NOUN: Jaruman Da Aka Zakulo Sun Dukufa

Published

on


Hakika a duk lokacin da aka ba da wani aiki ga wanda ya cancanta, tabbas za a bai wa mara da kunya, kuma a samu cimma nasara kan burin da aka tasa a gaba. Shi ya sa a irin haka masu iya magana kan ce “Aiki ga mai kare ka” ko kuma a ce “Ko wace kwarya da abokiyar burminta”.

Taurarin Fina-Finan Hausa da Jami’ar Karatu daga Gida (NOUN) ta zakulo domin zama jakadunta a cikin al’umma sun zagara da aiki.

Taurarun, Mansura Isah da Samirahh Ahmad da Umar Gombe wadanda aka zabe su bisa cancanta, sun dukufa ga bayyana wa mutane muhimmancin yin karatu a jami’ar a duk inda suke ba tare da wata matsala ba.

Wani abin burgewa shi ne jakadun sun shiga kasuwanni sun yi hotuna kuma sun wayar da kan mutane game da mahimmancin karatu, musamman wannan karatu da suka karbi aikin yada shi.

Taurarin jakadun cikin hikima da fasaha da gwanancewa sun nuna wa jama’a cewa, batun karatu fa ba lallai sai an shiga aji an zauna ba, don haka Jami’ar NOUN ta ba da dama ga kowa ya yi karatu duk a inda yake, walau a kasuwa ko a banki ko a gida, hatta dan Su (mai kamun kifi) zai iya yin karatunsa na digiri a bakin rafi.

Haka zalika Jakadun sun himmatu wajen jaddada wa al’ummar kasa cewa mutumin da yake son cimma muradinsa na karatu a jami’a zai iya samun haka cikin sauki a kwas din da yake so a ko ina yake.

Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, shi karatu yana da wasu abubuwa da shi kadai ya tara, na farko dai komai ana tsufa da yinsa idan yiwuwar hakan ta tashi, amma ban da karatu.

Na biyu kuma shi karatu ba’a jin kunyar yin sa, domin shi ba kaya ne da za ka ce an tara maka saboda nauyinsa tsufa ya hana ka daga shi ba. Sannan kuma, ba wai zai rika binka kowa yana kallonka tsofai-tsofai da kai ba, ballantana wasu su rika yi maka dariya kana jin kunya ba, wannan karatun kuwa ko wane iri ne haka abin yake.

Babbar hikimar da tasa wannan Jami’a ta fito da shirin ba da ilmin ko a ina kake shi ne, da yawa akwai mutanen da ba kunya ce take hana su zuwa ajin Makaranta ba, sannan kuma ba rashin halin yin karatun ba ne, sai dai harkokin da suke yi na yau da kullum su ne ke hana su shiga aji don yin karatu.

Amma wannan tsari sai ya zo da yadda za ka yi karatunka ba tare da takura ba, domin babu abin tinkaho a halin yanzu fiye da ilimi, da shi ne duk wata kasa a duniya ta ke jin ta isa daga dan yatsa take takama. Daukar littafi ka karanta musamman na makaranta, yana sanya nutsuwa ga dalibi, domin ya san ya san wannan aikin kadai shi ne a gabansa.

Da yawa akwai masu son yin karatu su kuma ba rashin hali bane suna da halin yin karatun, amma wata larura ta hana su, misalin wadanda suke da wata cuta da ba za su iya shiga jama’a ba saboda za a rika kyamar su, to mafi sauki sai su yi rijista da wannan jami’a suna zaune za ta rika ba su ilmi ba tare da sun je ko ina ba, a cikin gida ne ko wurin sana’o’insu.

Wannan kadan kena daga cikin fa’idar jakadancin da wadannan taurarin suke yi wa wannan Jami’a.

Shigar taurarin fina-finan Hausa cikin wannan aiki na jakadancin babbar jami’a irin wannan ya kara fayyace yadda masana’antar take kara samun bunkasa daga nishadi zuwa sauran sassa masu alfanu na rayuwa.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai