Connect with us

ADON GARI

Taskira: Tsamiya: Amfaninta, Illolinta, Da Magungunan Da Take Yi

Published

on


Tare da Jummai Ibrahim GSM: 08185137255

Tsamiya na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan da al’ummar Hausawa ke amfani da su sosai a rayuwarsu ta yau da kullum. Tana da amfani mai tarin yawa, haka kuma tana wasu illoli idan aka sha ta ba bisa ka’ida ba.

Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa abubuwan sha, wajen yin magani, da kuma a girke-girke a matsayin abun dandano.

Leadership Hausa A yau Juma’a ta gane matsalolin da Tsamiya ke magancewa:

  1. Cushewar ciki da rashin yin bahaya
  2. Mura da zazzabi
  3. Ciwon ciki
  4. Tashin zuciya ga masu ciki
  5. Tsutsar ciki
  6. Matsolin da suka shafi hanta da madaciya

 

Illolinta kuma sun hada da

  1. Tsamiya za ta iya haifar da illa ga masu ciwon sukari saboda tana rage adadin sikarin da ke cikin jini. Haka ma ga wadanda za a yi wa tiyata, ana so su dakatar da shan tsamiya akalla makonni biyu kafin a yi tiyatar saboda wannan dalili.
  2. Ga ramammu, yawan shan tsamiya na iya kara rama. Ga masu kiba kuwa za ta taimaka masu wajen rage kiba
  3. Ba a son a sha tsamiya da magungunan Ibrofen da Aspirin saboda tana kara adadinsu da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai