Connect with us

MANYAN LABARAI

Sojojin Ruwa Sun Bukaci Ba Su Damar Hukunta Masu Kunnen Kashi

Published

on


Rundunar Sojojin Ruwa ta Nijeriya ta bukaci Majalisar Tarayya da ta samar da Dokokin da za su bayar da dama su rika gurfanar da wadanda suka kama da laifi maimakon hannunta su ga ‘yan uwansu jami’an tsaro domin gudanar da bincike.

Riyal Admiral, Bictor Adedipe, Kwamandan Sansanin Sojojin Ruwa na Gabaschi ne ya bayyana hakan a jawabinsa yayin da Kwamitin Sojojin Ruwa A Majalisar Wakilai ya ziyarci rundunarsu a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba.

Adedipe ya bayyana cewar da yawan masu aikata laifi da suka kama suka kuma hannunta ga jami’an tsaro domin gurfanarwa sukan sake dawowa su sake aikata irin laifin da suka aikata a baya.

Ya bayyana cewar dokokin da Majalisar Tarayya ta samar ne kawai za su baiwa Sojin Ruwan Nijeriya cikakken goyon bayan doka na gurfanar da masu aikata miyagun laifuka. “Muna kamawa tare da tarwatsa haramtattun ma’adinai a kowace rana. A duk lokacin da muka yi kame muka hannunta ga ‘yan uwan mu jami’an tsaro, za ka yi mamakin jin cewar an bayar da belin su.”

Don haka ya ce “Muna rokon Majalisar Tarayya da ta ba mu cikakken goyon bayan doka domin mu rika kamawa tare da gurfanar da wadannan miyagun masu laifi da jami’an mu ke kamawa suna aikata ayyukan assha.”

Da yake jawabi, shugaban kwamitin, Honarabul. Abdussamad Dasuki ya bayyana cewar a nan gaba kadan a watanni masu zuwa Majalisar Tarayya za ta sanya wa Dokar Tsaron Ruwa da Yaki da Fashi a Cikin Ruwa (Anti Piracy) hannu domin baiwa Sojojin Ruwa damar samun albarkatu masu yawa domin samun kayan aiki.

Hon. Dasuki ya bayyana cewar tuni Dokar ta tsallake karatu na farko da na biyu da kuma taron sauraren ra’ayin jama’a don haka nan gaba kadan za a aminta da ita a matsayin doka.

Dan Majalisar wanda ke wakiltar Mazabar Kebbe/Tambuwal a Majalisar Wakilai ya bayyana cewar da ba don sadaukar da kai da kwazon Sojojin Ruwa ba da Nijeriya ba ta kai inda take a yanzu ba.

“Wajibi ne a karfafawa Sojojin Ruwa domin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya. Haka kuma Majalisar Tarayya ta na duba wasu hanyoyi domin kara inganta ayyukan Sojojin Ruwa.” Ya bayyana.

A jawabinsa Kwamando (Commodore) Promise Dappa, Jami’in Mulki na Sansanin wanda ya bayyana nasarori da kalubalen da suka fuskanta a 2017 ya bayyana cewar da yawan laifukan da suke hannuntawa ga jami’an tsaro ba a daukarsu da muhimmanci.

Dappa ya jaddada cewar jami’an tsaron da ke da hurumin doka wajen gurfanar da masu laifi sun fi bayar da kulawa ga shigar da karar masu laifin da suka kama da kansu.

Ya kuma bayyana cewar a cikin watanni shida da suka gabata, sun kama mutane 65 suna hako mai ba bisa ka’ida ba, an kuma kama manyan jiragen ruwa 20, da kwale-kwale 11 da kuma jiragen ruwa na katako 66.

Ya ce sama da haramtattun matatun mai 500 ne aka tarwatsa an kuma karbe sama da ton dubu 20 na gurbataccen mai da kuma ton dubu 20 na haramtaccen gyararren mai wadanda duka aka kama daga barayin mai.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai