Connect with us

LABARAI

Rigima Kan ‘Ya’ya: Matar Dan Atiku Ta Yi Nasara A Kotu

Published

on


Kotun majistare da ke yankin Tinubu a Jihar Legas ta raba takaddamar da ke tsakanin dan gidan tsohon mataimakim shugaban kasa, Aminu Atiku Abukar da matarshi Ummi Fatima Bolori, wanda ta samu sa’a  a kanshi.

Kotun dai ta ba matar wannan damar ce saboda Aminu ya kasa zuwa kotun don ya kare kan shi, dangane da ‘ya’yansu biyu, dan shekara tara da kuma mai shekaru bakwai, don haka suka ba ta damar cigaba da kula da ‘ya’yan nasu.

Kotun wadda majistara Kike Ayeye ta jagoranta, a hukuncin da ta yanke ta ba Ummi Fatima Bolori cikakkiyar damar  cigaba da kulawa da su, amma dai ba’a bayyana sunan ‘ya’yan ba. Kotu ta bata  damar ta sa su makarantar da taga tafi dacewa da ilminsu.

Kotun har ila yau ta bada dama ga mahaifin nasu ya ziyarce su duk lokaci da yaso, hakanan kuma idan an yi hutu yana iya zuwa ya dauke su suyi hutu da shi. Akwai kuma maganar Naira 250,000 kudaden da zai rika biya duk wata ladar kulawa da su ‘ya’yan nasu, za kuma a fara bada kudin tun daga watan Janairun na wannan shekarar ta 2018. Sai kuma maganar inshorar lafiya ta yaran biyu duk da zai dauki nauyi.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai