Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ba Su Iya Kwallo Ba – Dabi

Published

on


Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Dabi Hernandez, ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ba ta iya buga kwallo ba domin ba sa kayatar da magoya bayansu.

Dabi, wanda ya shafe shekara da shekaru a kungiyar ta Barcelona kuma ya lashe kofuna masu yawa daga shekara ta 2008 zuwa ta 2011 ya ce kwatakwata Real Madrid ba ta iya buga wasa ba.

Ya ci gaba da cewa sau da dama kungiyar tana siyan ‘yanwasan da suka iya buga kwallo amma saboda kungiyar ba burinta ta kayatar da magoya bayanta ba sai ta lalata ‘yanwasan da buge-buge da zundume zundume.

Ya ce kowa ya san tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona yadda ta iya murza kwallo kuma suna kayatar da yan kallo yadda yakamata.

Ya kara da cewa burin kungiyar shi ne dan wasan baya na kungiyar ko mai tsaron raga ya zunduma kwallo sai ‘yanwasan gaba na kungiyar suyi gudu su dauka wanda bah aka akeyi a Barcelona ba.

Yace a Barcelona idan mai tsaron raga ko dan wasan baya yana yawan zundume zundume magoya baya ihu suke masa saboda bah aka suke son gani ba saboda haka dole ya daina ko kuma ya daina jin dadin kungiyar.

A karshe yace kungiyar tana samun nasara a haka duk da rashin buga wasansu kuma kamar yadda kowa yasani kowacce kungiya tanada nata salon wasan saboda haka ba laifi sukayi ba sai dai yace magoya baya suna son a dinga burgesu ta hanyar buga wasa mai kyau ba kawai samun nasara ba a wasa.

A yanzu Dabi yana hadaddiyar daular larabawa yana buga wasanninsa tun bayan daya bar kungiyar ta Barcelona kuma yana da niyyar zama mai koyar da ‘yanwasa anan gaba.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai