Connect with us

ILIMI

Mufti Menk: Hanyoyi 22 Na Tarbiyyantar Da Matasa A Musulunce (2)

Published

on


Fassarar Bello Hamza

 

9: ka zama iyaye da abokin yaran ka matasa:

Mayar da su abokai na nufin ba su dawainiya a aikace-aikacen gida, misali in Amir dan shekara 16 ya iya mota, to ya rinka kai mahaifiyarsa kasuwa duk Asabar, ita kuwa Jasmine ‘yar shekara 15 a bata aikin gyara da kula da fulawan gidan ta haka zasu ga kansu a matsayin bangaren iyalin za kuma su kara mutunta kansu.

 

10: A samar da masallaci a cikin gida

Ka kebe daki ko wani bangare na falo ko tsakar gida ya zama mallacin gidan, ka dora wa manyan yaran  aikin lura da kannensu wajen share masallacin da kiran sallah da kuma tayar da ‘yan gida a lokacin sallan asuba da sauran su.

 

11: Ka guji addinin maza zalla.

Ana nufin kada ka hana mata sallah cikin jam’i, in maza na sallar jam;i ka tabbatar mata na yi a bayan su ka kuma tabbatar cewa, limamin yana karatu ta yadda matan zasu iya jin abin da ya ke fada, in har kuma babu maza a kwadaitar da matan yin sallah tare cikin jam’i tsakaninsu.

 

12: Ka samar da wajen ajiye litattafan addini tare da aiyana mai kula da su.

Ka samar da litattafan adidini tare da bideo da kaset-kaset na bangarori daba-daban na ilimin addinin musulunci, a kuma hada da littafan tarihin gwarazai da mujaddadan addinin musulunci. Ka aiyana daya daga cikin ‘ya’yanka matashi ya zama mai kula da littatafan, shi zai rinka lura da zirga-zirgan litattafai tsakanin mutanen gida da kuma daukar nauyin zuwa sayo sabbin litattafan in bukatar haka ya taso.

 

13: Ka rinka tafiya da su tarukan addinin musulumci.

Maimakon fita cin abinci a otal, ka kebe kudi domin dauka nauyin iyalinka zuwa taron addini ko wata walima in da zasu hadu da tsararrakinsu su kulla abokantaka tsakaninsu. Ya na kyau ka dauki nauyinsu domin halartar taron karshen zangon karatu na ‘yan makarata (IBC) a nan ma zasu hadu da ‘yanuwansu musulmi daga sassa daban-daban yana kuma kara dankon zumunci.

 

14: Ka koma unguwan da musulmi suka fi yawa.

In ‘ya’yanka suna hurda da musulmi da wadanda ba musulmi ba zai taimaka musu fahintar juna, amma kasancewa kusa da masallaci zai fi karfafawa yaran shaukin zuwa sallah cikin jam’i.

 

15 : Taimaka wa matasa hada kungiyar tsaransu.

Yayin da ‘ya’yanka ke hurda da ‘yauwansu musulmai za su samu abokai masu yawa cikin tsararrakinsu, to kada a bari zumuncin ya tsaya a nan, a taimaka musu hada kungiya su rinka haduwa lokaci zuwa lokaci suna ziyartar Malamai da Dattawa a cikin al’umma suna kuma shirya gyaran masallaci da makabartu, ta haka zasu kara fahintar rayuwar duniya da mahimmancin hadin kai tsakanin al’umma.ya na da kyau a samu manya cikin unguwa su zama masu kula da irin harkokin da samarin ke yi domin tabbatar da kauce wa matsala.

 

16: Ka samar da lokacin kallon talabijin, ka kuma lura da abin da suke kallo.

Babban abin da ke saurin dauke hankalin yara shine kale-kalen talabijin da sauraron wakoki, dole iyaye su lura da abubuwan da yaransu ke kallo da kuma tunatar da su kaucewa kallon abubuwan da ke dauke da tsirayci da tashin hankali da kashe-kashe, amma a karfafa su a kan kallon shirye-shiryen addini. A kwai bukatar aiyana rana daya ko biyu da zai zama babu wanda zai kalli talabijin ko fim, ana sa ran wannan ya zama matakin rage kalle-kalle tsakanin iyalinka.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai