Connect with us

Uncategorized

Matasan Zamani: Ma’anar Bunkasa Harkar Gona

Published

on


A tashin farko, zai yi kyau mu fahimci ma’anar ko abinda ake nufi da inganta ko bunkasa Harkar Noma, “Agricultural Edtension” tukuna, gabanin kutsawa cikin bayani.

“Gabatar da kyawawan shawarwari gami da ba da tallafi ga Manoman da kuma iyalansu, ta hanyar amfani da hanyoyi iri-iri na ilmantarwa da ake da su: za a sanar da manoman sabbin hanyoyi da dabaru na noman zamani. Za a zaburar da su hanyoyin da za su bi don inganta kayan amfanin gonar da suke samarwa tare da samun karin kudin shiga. Wanda hakan zai matukar ciccida tare da inganta yanayin rayuwarsu, ilminsu da ma habaka matsayin manoman a cikin al’umma”.

Shirin inganta harkar noma da masana’antu cikin wannan kasa an fara shi ne tun a Shekarar 1962, inda aka kira shi da, “National Debelopment Plan 1962-1968.

Daga cikin abubuwan da ake son cimmawa karkashin wancan shiri na Shekarar 1966 sun hada da;

i- Gabatarwa da manoman namu yadda dabaru da hanyoyin noma na zamani suke a yau.

ii- Neman manoman da su hada hannu da karfe wuri guda don cicciba harkar noman zuwa ga mataki na gaba.

iii- Samar da kayan aikin gonar na zamani tare da bunkasa harkokin gonar fiye da yadda aka saba yi.

An ci buri matuka a wancan shiri na farko na inganta harkar noma da masana’antu da ma sauran dangogin tattalin arziki a wannan kasa. Cikin shirin, an yi hasashen za a kashe zunzurutun kudi har kimanin Dalar Amurka Bilyan guda da Milyan Dari Tara ($1, 900, 000, 000). Za a kashe kudaden ne wajen bunkasa abin da manomanmu ke samarwa da kuma yin amfani da kudaden wajen habaka sauran dangogin da za su ciyar da al’umar wannan kasa gaba.

Wadannan su ne jerin manufofi da tsare-tsaren inganta ko habaka Harkar Noma da gwamnatocin da suka shude kawo na-yanzu suka gabatar;

i-National Accelerated Food Production Programme (NAFPP, 1972)

ii-Riber Basin-Debelopment Authorities (RBDAs, 1973)

iii-Agricultural Debelopment Projects (ADP, 1975)

ib-Operation Feed the Nation (OFN, 1976)

b-Guaranteed Minimum Price Scheme (1975-80)

bi-Re-organisation of the Marketing Boards (1977)

bii-Land Use Act (1978)

biii-Agricultural Credit Guarantee Scheme (1978)

id-Green Rebolution (April, 1980)

d-Accelerated Debelopment Area Project (ADAP, 1982)

di-Multi-state Agricultural Debelopment Project (1986)

dii-Nigeria Agricultural Insurance Scheme (NAIS, 1987)

diii-Directorate of Food, Roads and Rural Infrastructure (1986)

dib-National Fadama Debelopment Project (NFDP, 1992) (Fadama 1, 11, 111)

db-National Special Programme for Food Security (NSPFS, 2003)

dbi-Agricultural Policy for Nigeria (1988)

dbii-The Nigerian Agricultural Policy (2001)

dbiii-Agriculture Transformation Agenda (ATA, 2011-2016)

did-Agricultural Promotion Policy (APP, 2016-2020)

 

(Za a cigaba a Mako maizuwa In Sha Allah)


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai