Connect with us

WASANNI

Karshen Tika-Tika-Tik: Cokuelin Ya Koma Valencia

Published

on


Mai koyar da ‘‘yanwasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya tabbatar da cewa dan wasan kungiyar, Francis Cokuelin ya bar kungiyar ta Arsenal inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Balencia.

Dan wasan, mai shekaru 26 a duniya ya samu kansa cikin halin rashin buga wasanni sakamakon rashin kokari da yake yi wanda hakan ya sa mai koyar da ‘yanwasan kungiyar ya ajiye shi a jiran ko-ta-kwana.

Dan wasan, a wannan kakar, ya buga wasa daya ne wanda aka fara da shi a farko sannan ya shigo bayan hutun rabin lokaci sau shida a gasar firimiya wanda hakan ya sa yake ganin yana bukatar barin kungiyar domin samun buga wasanni.

Mista Wenger ya ce, dan wasan yana bukatar buga wasanni sosai wanda kuma ba zai samu ba a kungiyar a yanzu wanda hakan ya sa kungiyar ta yanke shawarar siyar dashi domin ya cigaba da samun damar buga wasanni.

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia dai takai tayin kudi fam miliyan 12 wanda kuma kungiyar ta Arsenal ta amince da tayin kuma tabawa dan wasan dama domin yaje a gwadalafiyarsa a kungiyar.

Cokuelin, dan asalin kasar faransa wanda yakoma Arsenal a shekara ta 2008 ya buga wasanni 150 a kungiyar cikin shekaru goma da yayi yana buga wasa a kungiyar kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin kalubale na FA guda biyu.

A karshe Wenger yayiwa dan wasan fatan alheri inda yace yana fatan zai samu buga wasanni a kungiyarsa daya koma.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai