Connect with us

LABARAI

Kagaggun Labarai: Ragon Foliyo

Published

on


Wani Shugaban ‘yan sintiri ne mai suna Baballe, mazaunin Unguwar Mai’aduwa, lokuta da dama  yakan faki idon makwabcinsa Mutari, yana yi masa dauki-daidai cikin garken tumakinsa. Duk da cewa Baballen ne Kwamandan ‘yan Sintiri na Unguwar ta Mai’aduwa.

Ba a gidan Mutari ne kawai beraye ke shiga sace dabbobi ba, mugunyar ta’adar tuni ta riga ta zamo ruwan-dare game duniya a daukacin Unguwar ta Mai’aduwa tsawon lokaci, ba tare da iya lalubo bakin zaren ba. Takai-ta-kawo a Unguwar, makwabta na zargin junansu game da salwantar dabbobin a kai-a kai. Da yawan masu sukuni a Unguwar  na ta dannawa kungiyar ‘yan sintiri ta Unguwar  makudan Nairori don ba su kwarin gwiwar bankado barayin dabbobin.

Bera Baballe da aka sani da jagorantar waccan kungiya ta ‘yan sintiri kam ya cika cikakken makiri, daga ‘yan kudaden da kungiyar ke tarawa, yakan kamfaci wasu adadi masu kauri akai-akai da sunan yana kai wa ne ana sauke Alkur’ani don Allah Ya gaggauta bayyanar da barayin dabbobin. Ashe a duk sa’adda Baballe ya kamfaci wadancan kudaden bisa da’awar za a yi sauka, yakan kewaye ne zuwa Layin ‘yan kaji na kasuwar Kurmi ya kwashi kajinsa rabin dozin gami da yin zazzafan cefane ya kai gida.

Cikin dabbobi goma da Mutari ke kiwatawa, za a iske Baballe Kwamandan ‘yan sintiri tuni ya yi awon-gaba da kimanin shida. Haka cikin garken dabbobin akwai wani santalelen rago mai zubi daya da na-uda, wanda Baballen ya jima da kafawa arwa amma yana tsallakewa.

Wata rana kwatsam ne, Mutari ya saci-jiki daga kasuwa ya zo gida ya yi likimo, a yunkurinsa na daukar matakin rana-dubu-ta-barawo…Can dab da karfe daya na rana, sai Mutari ya rika jin wani kusur-kusur da ya gaza kwanta masa a rai can wajejen zauren gidansa, wanda a can ne garken dabbobin nasa yake.

Cikin wata sanda Mutari ya rungumi wata dirarriyar gora mulmulalla da ya jima da gadar ta wajen Abbansa, kana ya biyo bango cikin yanayi na dauke numfashi. Ko da ya kai ga zauren, sai ya yi kwalli da Kwamandan ‘yan sintiri tsugune zuru-zuru ashe ma tuni ya kwanto wannan barkeken rago daga turkensa ya dafe abinsa.

“Innalillaahi Wa’inna Ilaihi Raaji’un!” Shi ne sallallamin da Mutari ya yi cike da mamaki. Bayan ajiyar zuciya ne, sai Mutari ya dubi Baballe Kwamanda ya ce da shi;

“Shin wai wa nake gani ne kamar Shugaban ‘yan Sintiri? Ashe da ma wannan shi ne sintirin da ka jima kana yi cikin dabbobin al’umar Unguwa? Karyarka ta sha karya, don kuwa yau dubunka ta cika makiyin Allah mujirimi!”

Cikin karfin hali na mugun-iri, sai Kwamanda ya amsa da;

“Malam Mutari, ina ga bai kamata a tashin farko ka munana mini zato ba, ya kyautu ne ka tambaye ni abinda ke faruwa”

Cikin matsanancin fushi Mutari ya ce;

“To na tambaye ka, bisa wane dalili ne ya sanya ka shigo gidana babu izini, sannan har kake da karfin halin kwance min uban-garke?”.

Kwamandan ‘yan sintiri ya amsa da;

“Masu allurar foliyo ne na zo wucewa, sai na gamu da su a kofar gidanka suna neman yaron da za su aiko cikin gidanka a yi musu izini, su shigo su yiwa dabbobinka allurar foliyo. Saboda ka san wannan hunturun sanyi da muke ciki a yanzu, shi ke rikidewa ya zamewa dabbobi shan-inna muddin ba a yi musu allurar foliyon ba. Sannan, rashin yin allurar ne za ka ga dabba ta samu tawayar da hatta a addinance ma ba a son yin layya da ita. Ka ga ke nan yi musu allurar wani abu ne da za a kira shi da waajibun! Ina nufin, wajibi ne”

Sai Mutari ya ce;

“Af!! Ba ya ga goyon bayan kiwon lafiyar dabbobin, har ma ka rikide ka zama Ustazu, to karbi! (Ji kake wani tiiimmm!!! Ya shirga masa sandar dake rike a hannunsa a gadon baya).”

Bayan Kwamandan ‘yan sintirin ya fadi somamme sakamakon bugun sanda, sai Mutari ya fito waje ya samo wasu Samari su uku, kana ya ce da su;

“Don Allah ku dauke shi ku kai shi har cikin gidansa. Ku fadawa Matarsa Jummala cewa, an yi masa allurar foliyo ne kuma sai aka ga ya kasa tashi, amma kada ta damu zai farfado”

Nan da nan wadannan Matasa suka shigar da Baballe har cikin kwaryar gidansa suka shimfidar da shi. Sannan suka sanar da Matar gidan cewa an yi masa allurar foliyo ne sai ya shide ya kasa tashi. Amma Malam Mutari ya fada cewa zai dawo cikin hayyacinsa.

Nan fa Jummala ta sukwana ta debo ruwan sanyi a Firji, ta zo ta antayawa mijin a fuskarsa. Mhhhhh!!!!! Ya yi ajiyar zuciya. Jummala dai ta kara zabura ta samo mafici, ta zo ta gurfana a gabansa tana yi masa fifita.

Bayan Baballe ya farfado ne, sai ya kyallaro idanu ya yi wani kasake yana son jin yaya ake ciki ne, shin an fadi dalilin suman nasa ne ko kuwa ba a fadi ba?.

Jummala na ganin Maigida ya dawo hayyacinsa, sai ta dora fadin;

“Alhamdu Lillahi Kabiraa! Sannu baban Huwaila, ashe dai akwai sauran shan ruwanka a Duniya. Sannu, Sannu. Baban Nauwara ne ya ce da wasu Samari su shigo da kai, sannan su fada min cewa, wai allurar foliyo aka yi maka ka kasa tashi”.

Ko da Baballe ya ji cewa ashe ma asirinsa bai bankadu ba, nan da nan sai ya tashi ya ce da matar tasa;

“Hakika allurar foliyo aka yi min. Idan mutum yana yaro ne ake diga masa allurar, amma yayin da ya manyanta ba a yi masa ba, idan an zo yi masa sai dai a kantara masa ita ko a jibga masa maimakon digawa”.

Sai matar ta ce;

“Kamar yaya ne a kantara masa ko a jibga masa Maigida?”

Baballe ya dube ta ya ce;

“Yanzu fa ba lokacin wani wassafe-wassafe ne ba, ki tashi ki dora min ruwan dumi. Haba! Ai kamata ya yi mu godewa Allah Rabbana, tun da dai wannan mugunyar cutar da ta jima tana gudana a jinin jikina yanzu mun yi hannun-riga da ita. Maasha Allah! Khalassss!!!!!”

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai