Connect with us

AL'AJABI

Kabilar Ashaingin: Ga Tsiraici Ba Zina

Published

on


ALLAH DAYA GARI BAMBAN

Kabilar Ashingin ko Kambari, (kamar yadda aka fi sanin su), daya ne daga cikin kabilun da suke rayuwa a jihohin Neja da Kebbi. Bincike ya nuna cewa  Kabilar Kambari da suke zama a jihar Neja, suna zaune ne a kananan hukumomin Agwara, da Magama, da Mariga, da Rijau, da Wushishi da kuma Borgu. Yayin da wadanda suke a jihar Kebbi suna zaune ne a kananan hukumomin Ngaski da Yauri.

Kabilar Kambari manoma ne, abubuwan da suke nomawa sun kunshi;  gero, dawa gyada da doya. Ita wannan kabila ta Kambari kashi uku take dangani  da karin harshensu. Wadanan kare-karen harshe su ne: Tsishingini, Tsikimba, da Cishingi.

Da yawan ‘yan kabilar Kambari ba su da wayewa ta zamanini. ‘Yan kadan daga cikin masu wayewar suna gani shuwagabannin ba su isa ba. Yayin da su kuma shuwagabannin ke zargin ’yan kabilar da rashin ba da hadin kai gare su.            Hukumomin kasa sun yi ta kokari ta hanyar kyautatawa da kafa doka ga Kabilar Kambarin don su bi al’adar kasa su rabu da miyagun al’adunsu. Wannan ya haddasa masu rashin fahimta da zargi tsakaninsu da hukumomin.

Yawancin garuruwan da Kambari suke ba su ne ke sarautar a wuraren ba. Wannan ya sa suna adawa da Hakan. Da yawan iyaye basu aminta da makarantun boko ba, wanda suke ganin ta a matsayi bata wa yaro lokaci kawai, maimakonta gara yaro in ya isa zuwa gona ya je ya yi noma. Masu ilim daga cikinsu basu wuce kashi uku cikin dari ba.

Ga baki daya dai kabilar Kambari mutane ne masu saurin yarda da baki indai ba sun nanu isgilanci ga al’adarsu ko addininsu ba. Abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da asibitoci akwai karancinsu a garuruwan Kambari, musamman na kudancin jihar Neja.

Tarukan yau da kullun irin su, taron suna da na daurin are ko zuwa kasuwa duk ba a bar su baya ba. Sannan da yawansu suna murna a ranakun bukukuwan salla karama da sallah babba. Kambari ba su aminta da duk wata mummunar al’adaba a cikin al’ummarsu, kamar shaye-shaye da zinace-zinace.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai