Connect with us

RAHOTANNI

An Jinjina Wa Gwamna Gaidam Kan Ayyukan Raya Kasa

Published

on


Daya daga cikin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gurugusku,  ya bayyana matukar jin dadinsa bisa ga ayyukan ci gaban kasa da Gwamnan Jihar ke shimfidawa al’ummar Jihar ta Yobe, wanda ya bayyna hakan, tamkar shimfida ne ga samun nasarar cin zabe ga Jam’iyya mai jagorancin Jihar da kasa bakidaya shekarar zabe ta 2019.

Alhaji Ibrahim ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da wakilinmu a garin Potiskum, dangane da yadda gwamna Gaidam ke aiwatar da ayyukan raya kasa da suka shafi gina babban filin jirgin saman saukar da kaya na kasa-da-kasa da a yanzu haka ake kokarin ginawa a babban birnin Jihar.

Kusa a Jam’iyyar ta APC, ya kuma nemi matasa da su zama masu son zaman lafiya da junansu musamman ma ganin cewar shekarar siyasa ta kama, kamar yadda a kullum gwamna Gaidam ke gargadin Matasan.

Alhaji Ibrahim ya kara da cewar, Matasa a matsayinsu na kashin bayan al’umma ya zama wajibi su yi karatun ta nuna, wajen ganin wasu ba su yi amfani da su ba don cimma muradunsu na siyasa a karshe su watsar da su ba tare da hassala masu komai ba.

Ya kuma hakkake cewar, cikin hukuncin Allah, Jam’iyyar APC za ta ci gaba da kare kambunta a Jihar, musamman ganin hakan ya ta’allaka da irin ayyukan ci gaban kasa da ya ke aiwatar wa.

Gurugusku ya kuma roki ‘yan Jam’iyyar adawa ta PDP da kar su ci gaba da yaudarar kansu, dangane da tunanin cin zabe a matakin kasa da Jiha, su dawo ga Jam’iyya mai mulki ta APC don su ma su dandana romon dimokuradiyya don kar a bar su a baya.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai