Connect with us

RAHOTANNI

Jawabi: Jawabin Shugaba Di Jinping Na Kasar Sin Kan Murnar Sabuwar Shekarar 2018

Published

on


A jajiberin sabuwar shekara ta 2018, shugaba Di Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabi don murnar sabuwar shekara, ta gidajen rediyon kasar Sin CRI, da gidan rediyon jama’ar kasar Sin CNR, da gidan talibijin na CCTB, da gidan talibijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN da ma yanar gizo ta Internet.

Yanzu ga cikakken jawabin da shugb Di ya gabatar:

Jama’a masu karatu da masu kallo da ma masu sauraro, maza da mata:

 

Barka da yamma! lokaci na wucewa cikin sauri. Yanzu muna maraba da sabuwar shekara ta 2018. A nan ne nake yi wa ‘yan kabilu daban daban na kasarmu, da ‘yan uwanmu na yankunan musamman na Hong Kong da Macao, da lardin Taiwan da ma Sinawa ‘yan kaka gida murnar sabuwar shekara. Kana kuma ina fatan abokanmu da ke sassa daban daban na duniya za su cika burinsu a shekara mai zuwa.

Allah yana yabawa wadanda suke kokarin yin aiki, sannan kome na samun sauye-sauye a kullum. A shekarar 2017, mun gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 19, wanda ya fara sabon aikinmu na raya kasarmu ta gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni. Jimillar GDP da kasarmu ta samu ta wuce kudin Sin yuan biliyan dubu 80. Karin mutane fiye da miliyan 13 sun samu aikin yi a duk fadin kasar. Sannan mutane fiye da miliyan 900 suna cin gajiyar inshorar tsoffi. Haka kuma, mutane kimanin biliyan 1.35 suna cin gajiyar inshorar lafiya, yayin da wasu fiye da miliyan 10 suka fitar da kansu daga kangin talauci a yankunan karkara. A cikin wata tsohuwar waka, an ce, “Idan an samar da gidaje masu tarin yawa, wadanda suke fama da talauci za su yi farin ciki sosai.” Yanzu, masu fama da talauci kimanin miliyan 3 da dubu 400 sun fara sabon zaman rayuwarsu a sabbin wurare, inda suka samu sabbin gidaje, sun fita daga talauci. Sa’an nan kuma, an kammala yin kwaskwarima kan gidaje marasa inganci miliyan 6 kafin lokacin da aka tsai da. Kasar Sin ta gaggauta raya ayyukan jin dadin jama’a iri daban daban, yayin da yanayin muhalli yake ta samun kyautatuwa. Jama’ar Sin sun kara jin dadin zamansu cikin tsaro. A hakika dai, Kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen raya zaman al’umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni.

Kasar Sin ta kuma samu nasarori da dama a fannonin kimiyya da fasaha, yin kirkire-kirkire, da manyan ayyuka. Tauraron dan Adam na Huiyan yana zagayawa cikin sararin samaniya. An samu nasarar yin gwajin babban jirgin sama kirar C919. Sannan an samu nasarar fitar da na’ura mai kwakwalwa ta zamani. An kammala gwajin shuka shinkafa a cikin ruwan teku. An soma gwajin babban jirgin ruwan yaki mai dauke da jiragen saman yaki cikin ruwa. Injin bincike na musamman mai suna Haiyi ya kammala aikin binciken cikin ruwan teku mai matukar zurfi. A karo na farko kasar Sin ta hako wani nau’in kankarar da ake iya konawa. Tashar jiragen ruwa ta Yangshan da take sarrafa kanta ta bude kofarta. An gama gina babbar gada data hade Hong Kong, da Zhuhai da Macao baki daya. Jirgin kasa mai saurin tafiya kirar Fuding ya fara tafiya a duk fadin kasar ta Sin. Ina jinjinawa da kuma yabawa kwarewar jama’ar Sin ta yin kirkire-kirkire!

A sansanin soja na yin rawar daji na Zhurihe, mun gudanar da atisayen soja domin tunawa da cika shekaru 90 da kafuwar rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin PLA. A yayin da aka cika shekaru 20 da komowar Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin, na kai ziyara a Hong Kong. Na ganewa a idona cewa, sakamakon cikakken goyon baya daga gwamnatin tsakiyar kasar, Hong Kong ta ci gaba da samun dadaddiyar wadata da kwanciyar hankali. Tabbas ne Hong Kong zata kara samun makoma mai kyau! Har ila yau, mun gudanar da taron tunawa da cika shekaru 80 da kaddamar da yaki da mahara Japanawa, da taron tunawa da wadanda suka rasa rayukansu cikin kisan kiyashi da mahara Japanawa suka yi a birnin Nanjing na kasar Sin, a kokarin tunawa da tarihi da nuna fatan samun zaman lafiya nan gaba.

Haka zalika, mun shirya wasu tarurrukan diplomasiyya a nan kasar Sin, kamar taron dandalin tattaunawa na koli kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, taron shugabannin kasashen BRICS na Diamen, da taron tattaunawa tsakanin kusoshin JKS da na jam’iyyun siyasa na kasa da kasa. Ban da haka kuma, na halarci wasu muhimman tarurrukan kasa da kasa. A farkon wannan shekara, na halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na Dabos. Sannan na yi jawabi a babban zauren MDD dake birnin Geneba. Bugu da kari na halarci taron koli na kasashe mambobin kungiyar G20, da kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC. A yayin wadannan tarurruka, na yi musayar ra’ayoyi da sassa daban daban masu ruwa da tsaki, wadanda suka amince da kara azama kan raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama, a kokarin kawo wa al’ummomin kasa da kasa alheri.

A shekarar 2017, na samu wasiku masu yawa daga al’ummar kasar, kamar wadanda suke zaune a garin Yumai da ke gundumar Longzi a jihar Dizang, da makiyayya daga yankin Suniteyou a jihar Mongolia ta Gida, da kuma shehun malami wanda ya taba shiga aikin kaurar da jami’a ta Di’an zuwa yammacin kasar a shekaru 1950. Sannan akwai wasikar dana samu daga daliban jami’ar Nankai wadanda suka zama sabbin sojoji. Labarunsu sun burge ni matuka. Al’ummomin Sinawa na tsayawa kan kishin kasa, bautawa kasarmu ba tare da yin da-na-sani ba. A ganina, al’mmomin fararen hula, su ne manyan mutane. Kana kuma, ba za a iya jin dadin zaman rayuwa ba, dole sai an yi iyakacin kokarin yin aiki.

Masu karatu da masu kallo da kuma masu sauraro, maza da mata!

Shekarar 2018 shekara ce ta farko wajen aiwatar da manufofin da aka tsara a yayin babban taron wakilan JKS karo na 19 daga dukkan fannoni. A yayin wannan muhimmin taro, an tsara babbar manufar raya kasarmu nan da shekaru 30 masu zuwa. Idan ana son gina wani gini mai tsayi, dole ne a kafa tushensa mai inganci. Idan muna fatan mayar da manufar da ta zama abin gaskiya, dole ne mu gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, a maimakon yin mafarki ko kuma tsara shiri kawai.

A shekarar 2018, za a cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje. Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, manufa ce da dole ne kasar Sin take bi domin samun ci gaba da cimma burin kasar. Za mu yi amfani da zarafin yin murnar cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, wajen warware matsalolin da muke fuskanta, zamu zurfafa gyare-gyaren da muke yi kamar yadda ya kamata.

Ya zuwa shekarar 2020, za mu kubutar da dukkan masu fama da talauci daga kangin talauci bisa ma’aunin da muke bi yanzu, wanda shine alkawarin da muka dauka a tsanake. Yanzu ya rage shekaru 3 kawai. Dole ne dukkan al’ummar kasar su dauki matakan da ake bukata bisa hakikanin halin da ake ciki, ta yadda za a iya rika samun sabbin nasarori kamar yadda ake fata. Samun nasarar kawar da talauci gaba daya cikin lokaci bayan shekaru 3, shine karo na farko da za a fitar da dukkan al’ummar Sin daga kangin talauci a tarihin Sin cikin dubban shekarun da suka gabata. Bari mu hada kanmu wajen kammala wannan babban aiki, wanda yake da matukar muhimmanci ga al’ummar Sin dama dukkan ‘yan Adam baki daya.

A halin yanzu, ana nuna kyakkyawan fata kan makomar dan Adam ta fuskar zaman lafiya da bunkasuwa, yayin da wasu suke nuna damuwa. Dukkansu suna fatan kasar Sin zata bayyana matsayinta da ra’ayinta a bayyane kuma a fili. Dukkan ‘yan Adam na kasancewa kamar wani babban iyali ne. A matsayinmu na wata babbar kasa wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, kasar Sin tana da nata ra’ayi. Kasar Sin tana tsayawa kan kiyaye marbatar MDD da matsayinta. Tana kuma nuna kwazo wajen sauke nauyinta a al’amurran kasa da kasa. Tana cika alkawarinta dangane da daidaita sauyin yanayi a duniya. Sannan tana kara azama kan aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Tun a da can da har zuwa yanzu, kasar Sin tana himmantuwa wajen shimfida zaman lafiya a duniya, tana ba da gudummawa wajen raya duniya, tana kuma kiyaye oda da tsarin kasa da kasa. Jama’ar kasar ta Sin suna son hada kai da jama’ar kasa da kasa wajen samun makoma mai wadata da kwanciyar hankali.

Masu sauraro, da masu kallo da masu karatu, maza da mata!

Jama’a ne ke kokarin kirkiro babban ci gaban da muka samu. Don haka dole ne jama’ar kasar su ci gajiyar nasarorin. Na gane cewa, jama’armu sun fi mai da hankali kan samun ilmi, da aikin yi, da kudin shiga, da inshorar zaman al’umma, da kiwon lafiya, da kulawa da tsoffi, da samun wurin kwana, da yanayin duniyarmu da dai sauransu. Wasu suna jin dadin zamansu, yayin da wasu suke nuna damuwa, ba su ji dadi sosai. Muna bukatar ci gaba da kokarinmu a wasu ayyukan jin dadin jama’a, hakan da ya bukace mu kara sauke nauyin dake bisa wuyanmu, mu gudanar da ayyukan jin dadin jama’a yadda ya kamata. Har ila yau tilas ne kwamitocin JKS a matakai daban daban, hukumomin wurare daban daban da jami’ai su mayar da moriyar fararen hula a cikin zukatansu a kullum. Wajibi ne su mayar da kawo wa jama’a alheri a matsayin aikinsu mafi muhimmanci, su warware dukkan matsalolin da jama’a suke fuskanta, su fitar da su daga wahalar da suka sha, a kokarin ganin jama’ar Sin sun kara jin dadin zamansu.

 

Na gode!

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai