Connect with us

SIYASA

Jadawalin Zabukan 2019: Wankin Hula Na Iya Kai Jam’iyyu Ga Dare

Published

on


Tun bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana jadawalin ranakun zaben shekara ta 2019, al’umma ke ta tofa albarkacin bakinsu game da ranakun da kuma halin da jam’iyyun kasar ke ciki musamman jam’iyya mai mulki ta APC da kuma babbar ‘yar adawa ta PDP.

Ya yin da wasu ke ganin jam’iyyun ba su shirya shiga zaben ba musamman yadda lokaci ke kurewa, don haka suke ganin da alama wankin hula zai kai jam’iyyiun ga dare. Wasu kuwa na kallon abin a matsayin hannunka mai sanda Hukumar zaben ta yi wa jam’iyyun don su fara shiri yanzu kar lokaci ya kure musu.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC), da ta fitar da ranakun zaben ta nuna cewa a ranar 16 ga watan Fabrairun shekara ta 2019 mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya. Wato Sanatoci da kuma ‘yan malajisar wakilai na tarayya.

Sabon salon da hukumar ta bullo da shi shi ne cewa daga yanzu wadannan ranaku sun zauna daram, ba sai kowane wa’adin mulki an yi wahalar batun tsaida ranaku na zabe ba don ya kasance daidai da tsari.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Mista Nick Dazang Daraktan yada labarai na hukumar zaben Nijeriyar ya sanar da hakan.

Tuni dai ‘yan siyasa suka fara sharhi da maida martani a kan wannan sabon babi na ranakun zaben a Nijeriya, inda wasu ke cewa hukumar ta yi riga Malam Masalacci. Amma ga wasu manyan ‘yan siyasar na Nijeriya na masu hangen alfanu da ma muhimmancin yin hakan ga daukacin tsarin dimukradiyyar Nijeriya.

INEC ta ce fitar da jadawalin na cikin tsari. Ta ce tsaida lokacin zaben da wuri zai ba da damar kammala shiri kafin lokaci ya kure.

Sanin cewa a baya dai sanar da ranakun zaben na nuni da kada kugen siyasa ne na fara yakin neman zabe, abin da ke katse hanzarin gudanar da ayyukan gwamnatin da ke kan mulki. To sai dai daraktan hukumar zaben ta Nijeriya ya ce akwai bukatar a fahimci lamarin. Domin ba wai sun buda kofa a fara kamfen da yakin neman zabe ba ne.

Tuni dai aka fara ganin alama ta fafatawar da za a yi a tsakanin jam’iyyu da ma ‘yan takara da suka fara kunno kai da yawansu ya kai mutum 15 da za su fafata a zaben shugaban kasar Nijeriyar a 2019. Zaben da masana harkokin siyasa ke ganin cewa zai kasance mai ban sha’awa saboda kara wayewar da kan mage ya yi a tsakanin ‘yan Nijeriya a fuskar zabe.

Hukumar ta ci gaba da cewa za ta gabatar da zabe a kujeru 1,558 a fadin kasar wanda suka hada da kujerar shugaban kasa, gwamnoni 29 cikin 36 da ake da su. Sai kuma kujerun Sanatoci 109, kurerun majalisun wakilai na tarayya 360, kujerun ‘yan majalisun jihohi 991. Sai kuma shugabannin Kananan Hukumomi na birnin tarayya guda 6 da kansilolinsu guda 62.

Hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta ta ci gaba da bayyana cewa za a fara zaben ne da Shugaban kasa da ‘yan majalisar Dattawa da na Wakilai. Sai kuma na Gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi. Sai a kammala da zaben shugabannin Kananan Hukumomin Birnin tarayya Abuja da kansilolinsu, kamar yadda kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da aka yi garanbawul da kuma dokokin zabe suka tanadar.

Za a fara yakin neman zabe na shugaban kasa da ‘yan majalisar wakilai a ranar 18 ga watan Nuwamba 2018. Su kuwa masu takarar Gwamna da ‘yan majalisun jihohi za su fara na su yakin neman zaben ne a ranar 1 ga watan Disambar 2018. Su kuma masu takarar kujerun Kananan Hukumomin Birnin Tarayya Abuja za su fara na su yakin nema zaben ne a ranar 2 ga watan Disambar 2018.

Ranar karshe ta mika sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da ‘yan majalisar Dattawa da na Wakilai ga Hukumar zabe ita ce ranar 3 ga watan Disamba na 2018. Ya yin da mika sunayen masu yin takarar Gwamna da majalisun jihohi zai kasance ranar 17 ga Disamba. Sai kuma na masu yin takarar Shugabancin Kananan Hukumonin Birnin Tarayya da kansilolonsu zai kasance ranar 14 ga watan na Disambar 2018.

Ita kuma ranar kamfe ta karshe ga ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisar Dattawa da malajisar wakilai zai kasance ranar 14 ga watan Fabrairun 2019. Shi kuma na Gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi da kuma masu takarar shugabannin Kananan Hukumomin Birnin Tarayya zai kasance ranar 28 ga Fabrairun 2019, dan haka hukumar ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryenta don tunkarara wannan zabe. Sai dai ta nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki don ganin wannan shiri na ta ya sami nasara. Sai dai kuma bisa dukkan alamu akwai sauran aiki a gaban jam’iyyun da ke neman shiga wadannan zabubbuka da za a yi a shekarar 2019.

Jam’iyyar PDP da ta yi fatan ganin ta sake dawowa kan mulki na fama da matsalolin rikicin cikin gida da ya ki ci, ya ki cinyewa.

Tun bayan kammala babban taronta da ta gudanar, in da aka zabi sabbin shugabannin jam’iyyar, wanda aka yi fatan zai kawo karshen rikicin jam’iyyar, sai kuma ga wata sabuwar jam’iyyar ta PDP ta bayyana, wadanda suke bayyana cewa sune cikakkun kuma halastatun jam’iyyar ta PDP.

Wannan ba karamin kalubale bane a jam’iyyar musamman a irin wannan lokaci da ake dab da fara yakin neman zabe. Baya ga wannan kuma da alama komawar tsohon ma’atimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar jam’iyyar ta PDP daga APC bai yi wa wasu ‘yan jam’iyyar dadi ba, musamman wasu Gwamnonin jam’iyyar da kuwa wasu daga cikin iyayen jam’iyyar. Suna kallon dawowar Atikun a matsayin wanda ya dawo jam’iyyar don yin takarar shugaban kasa, bayan sun sha wahalar gyara jam’iyyar da shi Atiku din ya kware wa baya a shekarar 2014, dab da yin zaben da suka ka da PDP din.

Wannan da kuma wasu matsalolin na daga cikin abin da PDP ya ke ci mata tuwo a kwarya kuma idan ba ta mayar da hankali wajen magance su ba to akwai yiyuwar wankin hula zai kai ta ga dare.

Ita ma jam’iyyar da ke mulki ta APC cike take da na ta matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa, wanda ya kamata tun wuri ta tunkare su don kar ta sha kasa a zaben da ke tafe.

Daga cikin matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta har da na rashin shugabanci na gari da wasu ‘ya’yan jam’iyyar ke zargin shugaban na kasa Cif Odigi Oyegun da shi. Sai dai kuma wasu na kallon halin da jam’iyyar ke ciki na rashin kudi ne babbar matsalar da ta ake fama da shi. Domin ko ma’aikatanta na kasa biyansu albashinsu na nema ya gagara.

Wasu kuwa na kallon gazawar APC din ne na kasa gudanar da babbara taron jam’iyya. Domin tun da aka kafa Gwamnati jam’iyyar ta kasa kiran wani taro da za ta tattauna matsalolinta don magance su.

Baya ga wannan, jam’iyyar na ta fama da rikice-rikice a jihohi da dama da take da karfi a cikinsu. Kamar jihohin Kaduna, Katsina da aka kasa yin zaben shugabannin jam’iyyar na wadannan jihohi tun bayan da aka nada shugabannin a wasu mukamai. Inda shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna ya zama mataimakin Gwamnan jihar, shi kuma na Katsina ya zama sakataren Gwamnatin jihar. Wasu ‘yan jam’iyyar na ganin Gwamnonin na da wata manufa ne shi ya sa ba sa son a yi zaben wadannan kujeru. Haka ma a jihar Kano tuni jam’iyyar ke fama da rikici wanda har ta kai ga bayyanar rarrabuwar kawuna a tsakanin magoya bayan Gwamna Ganduje da na Sanata Kwankwaso.

Hausawa dai na cewa duk wanda ya kona rumbunsa, to ya san in da toka ke tsada ne. Don haka wadannan jam’iyyu sun fi kowa sanin halin da suke ciki kuma sun fi kowa son cinye zabe, amma babban abin tambaya shi ne bisa tarin matsalolinsu da kuma jadawalin zaben da INEC ta sa, anya wankin hula ba zai kais u dare ba kuwa?


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai