Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Filato Ta Kasafta Kashe Naira Biliyan 132.7 A 2018 – Gwamna Lalong

Published

on


Gwamnatin Jihar Filato, ta kasafta kashe kudi Naira bilyan dari daya da Talatin da biyu, da milyan dari bakwai da biyu, da dubu dari biyu da casa’in da shida da dari biyu da casa’in da biyar, (N132,702,296,295.00)  a wannan shekara ta 2018.

Gwamnan Jihar, Barista Simon Bako Lalong, ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika kasafin kudin ga ‘yan Majalisar Dokokin  Jihar don amincewa, a kwanakin da su ka  gabata, ya ce, kasafin kudin wannan shekara ya kasa wanda gwamnati ta kasafta a bara,  yin la’akari da faduwar darajar mai da kuma cikas din da ake samu wajen tono mai din a sanadiyar ta da kayar baya da ‘yan tsagerun Neja- Delta, ke yi wa gwamnatin Tarayya, wanda ya tilasta gwamnatin rage yawan kudin kaso da take baiwa jihohi.

Ya ce, a wannan shekara gwamnatin Jihar ta kasafta tara kudin shiga na Naira bilyan Saba’in da biyar da Naira Miliyan Dari biyar da goma sha biyar da dari bakwai da sittin da Naira dari tare da hamsin da daya (N75,515,760,951.00) ne kawai, sai kuma kason da za ta samu daga gwamnatin Tarayya na Naira Biliyan Hamsin da Bakwai da Miliyan Dari Bakwai (N47,700,000.000.00) wanda ya nuna raguwar kimanin Naira Biliyan goma sha uku, N13, a kan na shekarar da ta gabata.

Gwamna Lalong, ya ce, daga cikin kasafin kudin da ya mika wa Majalisan, Naira Biliyan Sittin da Hudu da Naira Miliyan Dari Biyu wanda ya nuna kashi arba’in da takwas da digo arba’in da hudu,48.44 na jimillar kudin da za a kasha, zai je ne wajen manyan ayyuka, sai kuma Naira Bilyan Sittin da takwas da Miliyan Dari Hudu da Ashirin da biyu, da dubu dari shida da bakwai da dari biyu da tamanin da takwas, (N68,422,607,288), wanda ya nuna kashi Hamsin da Daya da digo Hamsin da shida,51.56. zai je ne wajen ayyukan yau da kullum.

Gwamnan ya godewa al’ummar Jihar bisa kyakkyawan hadin kai da goyan baya da suke ba shi, wanda ya ce hakan yana kara ba shi karfin guiwar gudanar da ayyukansa, ya kuma neme su da su ci gaba da yin addu’o’in fatan alheri wa Jihar.

Da yake karbar kasafin kudin Kakakin Majalisar, Ritaya Honarabul Peter Azi, ya tabbatar wa Gwamnan cewa, ‘Yan Majalisun za su yi duk abin da za su iya,  su ga sun yi nazarin kasafin kudin a cikin karamin lokaci, don mayarwa Gwamnan ya amince.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai