Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Filato Ta Janye Dokar Hana Daukar Nauyin Mahajjata

Published

on


Gwamnan Jihar Filato, Barista Simon Bako Lalong, ya bayyana cewa gwamnatin Jihar ta janye dokar da ta gindaya wa Musulmai da Kiristoci masu zuwa kasar Saudiya da Isra’Ila, don yin ayyukan Haji  da  aikin Ibada.

Gwamna Lalong ne ya yi wannan albishirin wa Kiristoci da Musulman Jihar  a lokacin da yake jawabin bankwana wa Kiristocin da za su je Kasar Isra’ila, don yin aikin ibada na wannan shekara ta 2017, da aka gudanar a harabar COCIN Church Jos, a makon da ya gabata. Ya ce yanzu gwamnati ta dawo da tallafawan da take baiwa Musulmi da Kirostoci masu karamin karfi daga Jihar zuwa kasashen Saudi Arabiya da Isra’ila don yin ayyukan ibada kamar yadda aka shar’anta masu.

Ya taya Kiristoci daga Jihar  da suka sami zarafin tafiya kasar Isra’ila,don yin ibada  murna, kuma ya hore su da su zama jakadu na gari a lokacin da suke kasar Isra’ila, kuma ya bukace su da su yi wa jihar da kasar addu’o’in samun zaman lafiya da yalwatar arziki a lokacin da suke ayyukan ibadarsu.

Tun da fari a jawabinsa Mataimakin Babban Sakataren Hukumar Jindadin Kiristoci na Jihar CPWB, Mista.Wilfred S. Sohatyep, ya ce, shirye-shiryen tafiya zuwa kasar Isra’ila,ya gudana cikin nasara, kuma ya yaba wa gwamnati mai ci yanzu a Jihar bisa kyakkyawar taimakon da take baiwa hukumar, musamman a lokaci irin wannan na tafiya ziyarar ibada. Jimillar Kirostoci 579, ne za su yi aikin ibada a kasar Isra’ila a wannan shekara daga Jihar, wanda 200, daga cikinsu Gwamnatin Jihar da Kananan Hukumomin Jihar suka dauki nauyin tafiyarsu.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai