Connect with us

RAHOTANNI

Gobarar Bututun Gas: Mata Da Yara Sun Bace A Delta

Published

on


Al’ummar garin Ugbokodo da ke yankin Karamar Hukumar Okpe ta Jihar Delta sun shiga dimuwa a sakamakon fashewar bututun gas da ya ratsa ta yankinsu a jiya Alhamis.

Al’amarin ya auku ne a kusa da matatar mai ta Warri da ke Jihar Delta.

Majiyarmu ta bayyana cewa tunda misalin karfe hudu na asuba bututn ya fashe inda mutanen kauyen suka rika tserewa domin neman tsira da rayukansu.

Rahotanni sun nunar da cewa wutar da ta tashi ta rudar da mutane kowa ya yi ta kansa zuwa cikin daji inda har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton akwai mutane da dama ciki har da mata da yara dab a a san inda suke ba.

An gano cewa fashewar ta auku ce a sakamakon hujicewar bututun gas din da ya ratsa garin wanda mutanen garin suka ce sun shaida wa mahukuntan Kamfanin Gas na Nijeriya amma ba a dauki matakin da ya kamata ba.

Da kyar da jibing goshi jami’an kasha gobara na hukumomi daban-daban suka yi taron dangi suka kasha wutar da ta tashi, inda daga bisani mutanen garin na Ugbokodo suka yi zanga-zangar nuna bacin rai kan yadda aka yi sakaci da rayukansu.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai