Connect with us

RAHOTANNI

Duk Da Akwai Wasu Matsaloli, Nijeriya Na Samun Ci Gaba

Published

on


A tsakanin ranaikun 19 da 22, na samu damar sake kai ziyara a Abuja, hedkwatar mulkin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya. Wannan ne karo na biyar da na kai ziyara a Nijeriya.

Tun da na fara koyon harshen Hausa a jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing a shekarar 1985, tun daga shekarar 1994 zuwa yanzu, na riga na kai ziyara Nijeriya har sau 5. A cikin wadannan shekaru fiye da 20 da suka gabata, a ganina, ko da yake har yanzu ya kasance wasu matsaloli, kamar ma’aikatai wadanda suke aiki a filin jirgin sama har yanzu suna neman kudi daga hannun fasinjoji, amma a hakika dai, kasar Nijeriya ta samu ci gaba sosai.

Da farko dai, ana tafiyar da harkokin siyasa bisa doka.  Kowa ya sani, bayan Nijeriya ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, ta kan gamu da juyin juya hali.  A tsakanin shekara ta 1963 zuwa ta 1998, gwamnatocin soja sun yi mulkin kasar har na tsawon shekaru 30.  Amma, bayan an komar da tsarin dimokuradiyya a kasar a shekarar ta 1999, ya zuwa yanzu, an riga an shirya manyan zabuka har sau biyar cikin lumana. Al’ummomin Nijeriya sun san muhimmancin zaman lafiya da ‘yanci.  Wannan ne wani babban ci gaba.

Sannan tattalin arzikin Nijeriya yana ta samun ci gaba a cikin shekaru 20 da suka gabata, har ma GDP nata ya wuce kasar Afirka ta kudu ya kai matsayin farko a nahiyar Afirka a shekarar 2013.  Ko da yake, wasu ‘yan Nijeriya sun ce, tattalin arzikin Nijeriya ba shi da kyau.  Amma, idan wani ya dade yana zaune a wani wuri guda, mai yiyuwa ne, ba zai iya ganin sauyin wurin ba.  A idona, wato wani bakon da ya kan kai ziyarar Nijeriya lokaci-lokaci, tattalin arzikin Nijeriya ta samu ci gaba sosai cikin shekaru 20 da suka gabata.

A tsakanin watan Mayun shekarar 1994 da watan Mayun shekarar 1995, wato a lokacin da kasar Nijeriya take karkashin mulkin soja na Sani Abacha, na samu damar kara koyon harshen Hausa a jami’ar Ahmadu Bello dake samara, Zaria bisa kwangilar hadin gwiwa da aka kulla tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Nijeriya. A lokacin da nake karatu a Jami’ar ABU, Zaria, babu masana’antu da yawa a kasar, balle yankin raya tattalin arziki.  Idan ina son buga waya daga Zaria zuwa Legas, wannan ba abu ne mai sauki ba.  Amma, yanzu, kowace jiha ta kasar tana kokarin kafa yankin raya tattalin arziki, ban da shugabanni da kuma ministocin hukumomin tarayyar Nijeriya, gwamnonin jihohi ma su kan tafi kasashen waje suna kokarin jawo jarin waje domin bunkasa masana’antun samar da kayayyakin masarufi, da sauran more rayuwar al’umma.  Alal misali, ga layin dogo da aka shimfida tsakanin Abuja da Kaduna. Ga layin dogo maras nauyi da sabuwar hanyar mota mai fadi sosai dake hade cikin garin Abuja da filin saukar jiragen saman Abuja.  Bugu da kari, yanzu kusan kowa yana da wayar salula, yana buga waya ga duk wanda yake son bugawa cikin sauki da rahusa.

Bugu da kari, yanzu ‘yan Nijeriya wadanda suke cike da imani ga makomarsu sun karu.  A lokacin da nake karatu a jami’ar ABU, Zaria, abokan ajinmu da sauran ‘yan Nijeriya da na sani su kan zargi shugabannin kasarsu.  Ko da yake kasar Nijeriya wata babbar kasa ce a Afirka, musamman ta fi muhimmanci a yankin yammacin Afirka, kuma tana da al’ummomi mafi yawa a duk fadin Afirka, ya kamata kowane dan Nijeriya ya yi alfahari da wannan.  Amma a ganin wasu ‘yan kasar, Nijeriya ba ta da makoma mai haske, sabo da a wancan lokaci, ana cikin mulkin soja.  Yanzu, ko da yake wasu ‘yan Nijeriya, ciki har da wasu manyan mutane su kan yi kuka kan kasarsu, amma ana iya ganin murmushi dake fuskokin galibin ‘yan Nijeriya. A lokacin da muke yin hira da su, su kan gaya mana cewa, a duk duniya, kasashen Amurka da Sin suna kan gaba, kasarsu Nijeriya tana kan matsayi na uku tana biyo bayansu biyu kawai.

Dadin dadawa, Nijeriya na kokarin kara yin mu’mala da sauran kasashen duniya bayan da aka komar da tsarin dimokuradiyya a kasar, ta yadda suaran kasashen duniya za su iya kara fahimce ta. A lokacin da na yi aiki a ofishin CRI dake Legas tsakanin shekarar 2002 da 2004, mai martaba tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya kan kai ziyara a kasashen duniya domin kokarin kyautata sunan kasarsa, da kuma jawo jarin kasashen duniya. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, kusan kowane ranaku uku, cif Olusegun Obasanjo ya tashi daga kasarsa zuwa kasashen waje. A wancan lokaci, kafofin yada labaru na kasar Nijeriya sun kira shi “Flying President”. Sauran shugabannin kasar bayan shi ma su kan kai ziyara a sauran kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa domin kara yin mu’amala da su. Yanzu, sunan Nijeriya ya samu kyautatuwa sosai bisa kokarin shugabannin kasar, da kuma na al’ummomin kasar. Haka kuma, ta jawo jarin waje mai tarin yawa.  Alal misali, yanzu kamfanin CCECC ya yi suna sosai a kasar Nijeriya, amma a lokacin da nake karatu a ABU, Zaria, babu ‘yan Nijeriya da yawa da su san kamfanin. Bugu da kari, a wancan lokaci, babu Sinawa da yawa da suke kasuwanci ko suke da zama a kasar Nijeriya. A nan kasar Sin ma, ban da ‘yan Nijeriya wadanda suke yin aikin diflomasiyya a kasar Sin, kusan babu sauran ‘yan Nijeriya da suka yi aiki ko suka yi kasuwanci a kasar Sin. A lokacin da na yi aiki a Legas, kamfanin CCECC ya fara samun suna a kasar.  Yawan Sinawa ma ya fara karuwa cikin sauri.  Galibinsu sun yi kasuwanci a Legas. ‘Yan kasuwa daga Nijeriya ma sun soma zuwa nan kasar Sin, musamman birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin. Kawo yanzu, na ga kusan kowane dan Nijeriya ya san wannan kamfanin kasar Sin na CCECC. Wannan kamfanin kasar Sin ya shimfida, ko yana shirin shimfida layukan dogo da yawa a duk fadin kasar Nijeriya.  Yawan Sinawan da suka yi kasuwanci ko aiki a kasar Nijeriya ma ya karu cikin sauri.  Na ji an ce, yanzu yawan Sinawan da suke da zama a sassa daban daban na kasar Nijeriya ya kai kusan dubu 60.  Galibinsu suna sayar da kayayyaki kirar kasar Sin. Sannan yawan ’yan kasuwa daga kasar Nijeriya ya kai fiye da dubu 10 a nan kasar Sin.

A matsayin wani tsohon abokin Nijeriya, ina fatan kasar Nijeriya za ta kara samun ci gaba kamar yadda ake fata. Ina kuma fatan al’ummomin Nijeriya wadanda suke bin addinai daban daban, kuma suka fito daga kabulu daban daban za su kara fahimtar juna, kuma za su zauna cikin jituwa.

Sanusi Chen, shi ne shugaban Sashen Hausa na Gidan Radiyon China (CRI), ya rubuto ne daga Birnin Beijing na Kasar Sin


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai