Connect with us

AL'AJABI

ALLAH DAYA GARI BAMBAN: Abin Da Ya Tilasta Wa Kabilar Eloyi Barin Tsauni A 1918

Published

on


Asalin Kabilar Eloyi na zaune ne a tsakiyar Nijeriya a yankunan jihohin Binuwai da Filato. Taswirar mazauninsu ta kai tsawo mil goma sha biyar a cikin tsaunuka, inda ’yan kabilar ta Eloyi ke zaune tun shekarar 1918.

Tarihi ya nuna cewa, a shekarar ta 1918 rikici ya wakana a tsakanin ’yan kabilar, wanda ya tilasta wa mafi yawan ‘yan kabilar kaura suka sauka daga kan tsaunukan zuwa karkashin tsaunukan. Sannan daga baya wasu suka sake komawa a kan tsaunukan suka bar dangi da ‘yan uwansu a kasa.

Ita wannan kabila ta Eloyi, a shekar 1932, Turawan mulkin sun karkasa su zuwa tungaye da kauyuka har guda goma. Wanda kowane kauye ya kasance karkashin hakiminsa. Koda yake ‘yan kabilar Eloyin sun dage a kan dabi’arsu da ganin sun zamo masu ‘yanci, wannan ya sa suka bijire wa hakiman da Turawa suka nada masu. Dan suna gani wannan nadi katsalandan ne a cikin al’adarsu da addininsu. Duk da kasancewar canjin zamanni, wannan bai sa ‘yan kabilar watsi da al’adarsu ta asali ba, amma kuma da damansu a yau sun shiga aiki a cikin gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu. Kasantuwar suna yin karatu zamani, hakan ya sa suna ba da gudummawa ta bangarori dabn-daban na tattalin arziki.

 

  • Tsarin Rayuwarsu

Idan an kwatanta su da sauran kabilun da suke zaune a jihar Binuwai, ‘yan kabilar Eloyi mutane ne masu himma ga neman na kansu. Ma’ana, su ba cima zaune ne ba. Dan haka suna samun ci gaba a fagen tattalin arziki. Duk da yake suna zaune ne a kan tsaunuka amma kuma suna noman abubuwa daban-daban, kama daga dawa, da auduga, da doya da kuma ganyen taba.

Yanwancin matan kabilar Eloyi suna yin ‘yan kanan sa’o’i kamar saida manja da busasshen kifi. Sun kware wajen kitso, da rini, na sakar tufafin gargajiya. Suna tafi–taye da nisa domin tallata hajojinsu.

Mazansu kuwa manoma ne sannan suna farauta, suna kuma share manyan gonaki domin noma, suna kuma hadawa da wasu sana’o’i manya. Duk da matansu suna yin wadan can sana’o’in, wannan bai hana su kula da mai gida da ayyukan gida ba, kamar kula da yara da kuma girka abincin gida.

Yanzu zamani ya kawo cewa, kabilar Eloyi suna zaune a garuruwa ne, wadanda suke da ginin bangaye. Manyan garuruwansu ana rarraba su unguwa –unguwa, kuma kowace unguwa tana da mai unguwarta. Ga wadanda suke a kan tsaunuka kuwa suna yin zagayayyun bukkoki ne wadanda ake rufe su da ciyayi. Wadannan bukkoki suna yin su rukuni-rukuni. Sannan su saki fili a tsakiyar rukuknan gidajen, wanda yake zama kamar wajen tarurruka da shakatawarsu.

A tarihi, ‘yan kabilar Eloyi ba su da wasu kungiyoyi na kabilu, a bin sani kawai su sun dauka cewa, al’ummar kauye su ne komai, ba wani abu ba. Kowane kauye yana cin gashin kansa ne ba ruwanshi da wani kauyen.

Kazalika kowane kauye yana da sarkinsa wanda yake da fadawa da masu ba shi shawara. Sukan hadu gaba daya don tattaunawa da warware matsalolin da suka shafi kauyen. A al’adar Eloyi, Gadon shi ne uban al’umma kuma shi ne mai yanke hunkunci na karshe ga duk wata magana da ta taso. Shi ne mai cewa amfanin gona ya nuna kuma shi zai ba da damar a girbe shi. Kuma shi ke kafa dokoki da hukunce-hukunce. Wannan al’ada suna biye da ita kaka da kakanni.

 

  • Addininsu

Mafi yawan ‘yan kabilar Eloyi suna bin addininsu na gargajiya, amma yanzu akwai masu bin addinin Musulunci. Eloyi suna bautar ubangijinsu ne, mai suna Owo. Bautar Owo ana yin ta a daidaiku ne ba a kungiyance ba. Shi wannan abin bauta nasu ba a ganinn sa sai dai a alamta shi, ko dai da farin siliki na auduga ko kuma da wani itacen kayan marmari. Ya danganta da wurin da mai bautar yake.

Bautar Owo na da matukar muhimmanci a rayuwar kabilar Eloyi. Yin fatalwa da maita da surkulle su ne kashin bayan imann wannan bauta.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai