Connect with us

MAKALAR YAU

Alkalami: Fina-finan Hausa: Kowag-gyara ya sani!

Published

on


Dr. Ibrahim Shehu Liman 08023703718 (TES Kawai )   [email protected]

Muna matukar godiya ga Allah madaukaki da ya bamu dama muna tofa albarkacin bakinmu da kuma yin hannunka-mai-sanda ga duka masu ruwa da tsaki kan harkar rubutawa, shiryawa da aiwatar da wasannin kwaikwayo da fina-finai, musamman ma a yanzu da harkar fina-finai na Hausa ke kara habaka. A makon jiya mun yi nazari kan abubuwan da suka jibanci marubuta da masu shirya wasan kwaikwayo ko fim, a wannan karo zamu waiwayi ‘yanwasa ne, ko kuma ‘yanfim.

Duka gudunmawar da marubuta da masu tsarawa da shirya fim ko wasan kwaikwayo suka bayar, to ‘yanwasa ne ke iya aiwatar da abin da aka rubuta ko aka shirya. Ta wannan hanyar aiwatarwa ne kuma ake iya tantancewa da more dandano na kowane fim. A dalilin haka ne ma ake ganin cewa idan an kwatanta duka rassan adabi, wato waka da zube da kuma wasan kwaikwayo, wasan kwaikwayo ko fim ne kawai ke iya isar da sako da kuma gamsar da jama’a sosai nan take, ko kai tsaye.

Shin shi wane ne danwasa, ko danfim? Za a iya bayyana shi da cewa shi ne, wani haziki, mai basira, mai juriya da kuma dabarar iya kwaikwayo wanda ke kwaikwayon yanayin rayuwar al’umma a aikace da kuma magance, kuma ya aiwatar da abin da ya ke kwaikwayo ta hanyar nishadantarwa.

Wajibi ne ga kowane danwasan kwaikwayo ko danfim ya zama ya tare wasu muhimman abubuwa guda uku da suka hada da lokacin da aka kayyade masa, da wuri ko bigiren da ake so ya kasance da kuma aiki, ko zancen da aka tsara masa. Bari mu bibiyi wadannan muhimman batutuwa daya-bayan-daya.

Lokaci abu ne mai matukar muhimmanci da ‘yanwasan kwaikwayo ‘yanfim ya kamata su kula da shi sosai. Duk wasa ko fim da za a aiwatar, a kan tsara shi ne gwargwadon tsawon lokaci, kamar mintoci gama shabiyar, ko rabin awa, ko kuma awa guda. Domin haka ne marubucin wasa ke tsara wasu kayyadaddun zantuka ko ayyuka ga ‘yanwasa domin su dace da tsawon lokacin da aka ware. Da zarar danwasa ya fadi ko aiwatar da abin da aka tsara mishi, ana bukata ya bayar da dama ga abokin fadi-in-fadarsa, ko abokin wasansa shi ma ya gabatar da nasa. Anan ba a so danwasa ya kankane kome yace shi kadai yake so a yi ta jin muryarsa, ko a yi ta kallon aikin da yake yi. Haka kuma wajibi ne ya kula da salon da yake amfani da shi, na shidantarwa ne, ko mai sosa rai ne, ko na bayar da tausayi ne, ko kuma wasun wadannan.

Dangane da wuri ko bigire, ana so a ga danwasa ko danfim a wurin da ya dace da matsayinsa, misali wajibi ne a ga dattijo a wurin da ya dace da shi, haka nan malami, ko saraki, ko kuma yara. Daidaita bigiren da ya dace da kowane danwasa zai taimaka a tarar da fim ko wasan da aka shirya ya zama ya na kan turba.

Sai kuma aiki, wanda a ba ya kadan, an ga cewa a mafi yawan lokuta, aiki na tafiya tare ne da zance. A nan ana bukatar kada danwasa ya kuskura ya rika wuce makadi da rawa, ko wuce gona da iri. Misali duk inda aka ayyana wani danwasa a matsayin Sarki, to akwai bukatar ya rika kamewa wajen zancensa, da yin takama wajen tafiya, da sarrafa fuskarsa ta kasance mai kwarjini da kuma yin wasu abubuwa da ke nuna kasaita da karimci. Haka abin yake ga duk wani matsayi da aka ba danwasa, lallai ne ya kasance kamar Kumbo-kamar kayanta.

A nan bai dace danwasa ko danfim ya rika yasassun zantuka da ba sa cikin abin da aka tsara ba, kada kuma ya yi wani zance ko aiki da bai dace da matsayinsa ba domin mai makon ya burge masu kallonsa, sai ya bata rawarsa da tsalle.

A wajen ‘yanwasan da akan tanada a wasan kwaikwayo ko fim, akwai danwasan da akan ware a matsayin babban tauraro da kananan taurari da kuma wadanda akan kira bi-yarima-ku-sha-kida. Don haka ana bukatar kowane danfim ya tsaya matsayinsa.

Idan an yi la’akari da tanade-tanaden da aka yi don ‘yanfim ko ‘yanwasan kwaikwaikwayo, a nan sai mai karatu da su ‘yanfim ko masu kallon fina-finai da ma masu yin tsokaci su yi nazarin wadannan tambayoyi:

  1. a) Shin ‘yanfim da ke fitowa a fina-finan Hausa su kan tsaya matsayinsu dangane da zantukan da aka tsara musu? Ko suna shiga fagen da bai dace ba.
  2. b) Shin wajen ayyukan da aka tanada ga su ‘yanfim, ko sun dace da matsayin da aka ba kowannensu?
  3. c) Shin bigire, ko wuraren da ‘yanwasa suke fitowa sun dace da su?

Dalilin bukatar amsa wadannan tambayoyi shi ne muddin ana samun zakewa ko gazawa dangane da wadannan batutuwa, akwai yiwuwar samun nakasa a wasa. Wajibi ne ‘yanwasa ko ‘yanfim su san cewa suna wakiltar yanayin rayuwar al’ummarsu ne. A baya an bayyana cewa aikin duk masu ruwa da tsaki ne a harkar wasan kwaikwayo ko fim, tun daga masu rubutawa, da tsarawa, da shiryawa, da aiwatarwa da ma masu yin tsokaaci, wato mawara da su san da zaman cewa makasudin wasan kwaikwayo ko fim shi ne bayyanawa da kare martaba da kuma bunkasa harshe da al’adu da yanayin rayuwar al’umma da kuma fasahohi da basirorinta. Domin haka ido ba mudu ba, amma ya san kima.

Duk inda aka san ana bukatar gyara, musamman ma wajen ‘yanwasa ko kuma ‘yanfim, wajibi ne a rika la’akari da haka, kasancewar su wadannan nan ‘yan wasa ne duniya ke kallo, kuma da abubuwan da suke aikatawa, ko fada, ko kuma irin shigar da suke yi ke suranta al’ummar Hausawa da ake magana a kai. Marigayi makadin kotso, Alhaji Musa Dankwairo Maradun na cewa cikin wakarsa ta Shirya Kayan Hwada Mai Gida Tsahe: “Ko wag-gyara ya sani, kowab-bata ya sani.

 

Mu kwana a nan. A tari alkalami a makon gobe, idan Allah ya yarda.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai