Connect with us

LABARAI

2019: ‘Yan Gombe Mun Amince Da Takarar Buhari — Habu Mu’azu

Published

on


Dan takarar Gwamna a Jihar Gombe a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Abubakar Habu Mu’azu Yariman Kashere, ya ci albasa da bakin al’ummar Jihar, inda ya ce, al’ummar  Gombe sun amince da takarar Buhari a zaben 2019.

Alhaji Abubakar Habu Mu’azu, ya bayyana hakan jiya a Gombe a wajen taron motsa Jam’iyyar da suka gudanar a Gombe .

Ya ce, ayyukan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi a Najeriya su suka sa suke ganin babu wani Wanda zai zo ya zamowa Buhari kishiya wajen yin takara.

Dan takarar, ya kuma ce a shekarun baya Boko Haram, sun addabi al’ummar Najeriya musamman yankin Arewa maso Gabas, amma zuwan Buhari ya kawar da ita har ma ya kafa kwamitin sake farfado da shiyyar ta Arewa maso gabas din.

Baya ga wannan ya ce, yanzu hakan aikin hako Man Fetur a wannan shiyya ta Arewa maso gabas din ya yi nisa, don ciyar da yankin gaba.

Habu Mu’azu, ya kuma ce ba su yarda Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi takara da Buhari ba domin bai cancanta ba saboda bai iya biyan kudaden fansho da gratuti ba, balle bashin ‘yan kwangila duk da irin kudaden faris kulob da Shugaban kasar ya bai wa gwamnonin.

Ya kara da cewa, ba shi kadai yake takara ba, kuma duk wanda ya zama Gwamna a cikin su ya kamata su hadu su marawa wanda Allah Ya baiwa goyon baya.

“Idan na zama Gwamna, ba zan nada kowa mukami ba sai wanda Jam’iyya take so, don Jam’iyya ce ta san wanda ya sha mata wahala da kuma ya fi da cewa a nada,” in ji Yeriman Kashere.

Har ila yau, ya yi alkawarin cewa, ko da lokacin yin takarar ya yi ba zai sa mutum ya rantsa da Alkur’ani ko Littafi mai tsarki na Bible kafin ya yarda mutum zai zabe shi ba.

Daga nan, sai ya kara da cewa, kamar maganar da Rabaren Nbaka ya yi kan cewa Dankwambo, cewa shi ya dace da takara, ya zo Gombe ya ga yadda mutanen Gombe suke rayuwa ne cikin ukuba ba rashin yanayin rayuwa mai kyau, Don haka ya bar ‘yan Gombe su zabi wanda suke so ba shi zai musu zabi ba.

Da yake jawabi tun farko Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ta yankin Gombe ta kudu, Mista Juliis Ishaya, jinjinawa Shugabanin Jam’iyyar tasu ya yi da kuma wakilci na mutane biyar-biyar da aka zabo su wakilci sauran.

Mista Julius Ishaya, ya ce, kuma a ce Jam’iyyarsu ta kira wannan taron ne don fara shirye-shirye na tunkarar zabubbukan da ke tafe, kama daga kan Shugaban kasa zuwa kan sauran mukamai.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai