Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Wani Mutum Ya Arce Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane Bayan Ya Ya Kwashe Mako Biyu Hannunsu

Published

on


Wani dan shekara 47 Philips Emekudu, mazauni a yankin Okpanam dake kusa da Asaba a jihar Delta ranar Alhamis data wuce, Allah ya tarfawa garin sa nono, sakamakon arcewar da ya yi da yammar ranar daga ma’ajiyar gungun masu yin garkuwa da mutane bayan sunyi garkuwa dashi

har tsawon sati biyu.

Philips anyi garkuwa dashi ne lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa gidansa a yayin da yake tuka motarsa kirar Ledus 350 SUB a daidai titin Okpanam, inda gungun masu garkuwar su shida suka auka masa a kusa da wani sanannen otel, suka tilasata masa shiga cikin motar tasa, sannan suka arce dashi zuwa wurin da ba wanda ya sani.

Da yake shedawa manema labarai yadda lamarin ya auku, Philiphs yace “sun dauke ni zuwa wani daji, inda suka ajiye ni har sati biyu ba tare da bani abinci mai kyau ba, kafin daya daga cikin su ya taimaka min in arce daga gurinsu,inda acewar wanda ya taimaka min din, na taba taimaka masa a wasu shekaru da suka shige.”

Idan za’a iya tunawa, rundunar ta jihar Delta ta kaddamar da neman philips tun kafin masu garkuwar su fara tuntubar iyalansa neman kudin fansa.

A wata sabuwar kuma, jami’an ‘yansanda sun cafke mutane biyu da ake zargin masu yin garkuwa da mutane a gari Ibusa kusa da  Asaba.

An cafke sune lokacin da suke yunkurin yin garkuwa da ta hanyar yin amfani da kafar shafin zumunta na facebook.

Mutumin wanda aka sakaya sunansa, masu garkuwar sun gayyace shine daga warri dake jihar Imo zuwa garin Ibusa ta hanyar Facebook, inda suka dauke shi zuwa cikin wani daji suka bukaci kudin fansar sa naira dubu N200,000 daga danginsa kafin a kamasu.

Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Mista Andrew Aniamaka, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace wadanda ake zargin a yanzu haka suna gudanar da binceke akansu in an kammala binciken za’a gurfanar dasu a gaban Kotu.

Har ila yau, jami’an ‘yansanda masu yaki da ‘yan fashi da makami (SARS) dake gudanar da aiki a rundunar ‘yansandan jihar sun cafke ‘yan fashi da makami uku  da ake zargin sunje yin fashi a gidan wata mata bazawara ‘yar shekara 52  dake kantitin Infant Jesus a cikin Asaba.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Aniamaka, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace jami’an ‘yansanda sun samu nasarar cafke sune sakamakon bayanan sirri da suka samu, kuma wadanda ake zargin bayan da aka gudanar da bincike akansu, sun amsa laifinsu sannan kuma an dauke su zuwa anguwar Agbor, inda aka dauko motoci har guda sha uku da suka sace.

Kakakin ya zayyana sunyen wadanda ake zargin kamar haka;  Kayode Fredrick da Nnamdi Kenneth da da kuma Boniface Iwuobi, kuma rundunar tana gudanar da baicike akansu.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai