Connect with us

LABARAI

MUKALA: Hattara Dai Inyamurai (16)

Published

on


Daganan ne kuma Ogundipe ya fara neman hanyar sulhu amma kuma duk hanyar da ya bi na samun sulhu sai ta kiya don sojojin arewa sun ce in dai ana son sulhu sai dai a dawo da mulkin ga wadanda aka kwacewa watau lokacin da aka kashe Tafawa balewa watau Alhaji Dipcherima ya zama Fira-minista. Da sauran sojoji kudancin Najeriya suka ga abin babu dama suka nunawa Odundipe gaskiya cewa in har yana son ransa to ya rufawa kansa asiri ya bi, in ko ba haka ba zai zama marigayi. Suna fada masa haka kowannesu ya zuke, su ka yi kauyukansu suka yarda kwallon mangwaro suka huta da kuda. Ganin wannan ya sanya shi ma ya bayar da kai bori ya hau.

Daganan sojojin ‘yan asalin arewa suka yi shawara suka baiwa Yakubu Gowon shugaban kasa don shine mafi girman mukami cikin sojojin arewacin Najeriya a ranar asabar 30 ga watan Yuli 1966. A ranar 1 ga Agusta 1966 Yakubu Gowon ya yi wa kasa jawabi na farko inda ya fadi dalilan da ya sanya aka yi wannan juyin mulki sa’annan kuma ya yi kira da kowane soja ya yi wa Allah ya baiwa kansa magana a daina zubar da jini hakanan don zubar da jinin da aka yi ya isa, sa’annan kuma ya yi alkawarin mayar da mulki a hannu farar hula ba da dadewa ba.

Washegari kuma Gowon ya yafewa Chief Obafemni Awolowo da Chief Anthony Enahoro da sauransu wadanda aka daure saboda laifin cin amanar kasa. Awolowo  yana fitowa kuma sai ya yi kira ga Yarabawa da su manta da duk abin da ya faru su goyawa Gwamnatin Yakubu Gowon baya. Shi ma Dabid Ejoor na yankin Benin ya yi caffa ga sabuwar Gwamnati a ranar 3 ga watan Agusta haka shi ma gwamnan yamma ta tsakiya watau na Benin Kanar Adeyinka Adebayo ya yi tasa mubayi’a a ranar 4 ga watan Agusta yanzu abin da ya rage shine Ojukwu na kasar Inyamurai.

Yanzu kuma labari ya taru kacokam ya koma kasar Inyamurai, sai kuma mu je can mu ga yadda abubuwa suka kaya. Ita ma Enugu kumandan Bataliya ta farko Lt Kanar Dabid Baba Ogunewe ya samu labarin abin da ke faruwa a Abeokuta don Kyaftin Ogbonna ya sanar da shi, kuma kaddara ce kawai ta sanya ya sani don wanda ke karbar signa din dan arewa ne kuma bisa kaddara sai ya tashi ya je yin wani abu. A wannan lokacin sakon ya iso sai wanda ya karba ya kaiwa kumanda. Wannan ya sanya ya shiga cikin sojoji a ranar 30 ga watan Yuli tun da asubahin farko inda ya iske Shehu Musa ‘Yar aduwa da Daudu Sulaiman da Muhammadu Jega da sauransu suna tare amma su ba su yi niyyar kaiwa kowa hari ba don suna tsakiyar Inyamurai ne. Saboda haka suka yanke shawarar kada su kai hari illa su yi kokarin kare kansu. Shi kansa ‘Yar aduwa ya san abin da ke faruwa don Kyaftin Remawa ya fada masa abin da ya faru a Abeokuta. Wannan ya sanya ya tashi ya kuma tayar da dukkan sojojin ‘yan asalin arewa. Daganan aka tara sojojin inda aka yi gamin gambiza na sojoji ‘yan asalin yankin arewa da na kudu suka shiga gadin runbun makamai don kada a samu mamuwa.

Gama wannan sai Ogunewe ya fada wa Ojukwu abin da ake ciki sa’annan aka tayar da sojoji aka ce musu don Allah su bari a zauna lafiya aka kuma ayyanawa kowane soja inda zai zauna ba tare da kula daga inda ya fito ba. Wannan zai hana wani bangare ya shammaci wani bangaren. Daganan kuma aka shawarta cewa in ban da shi Ogunewe kada a samu wani soja dauke da makami.

Da karfe 11 na safe Ojukwu ya kara yin taro inda ya fada wa mahalarta taron abin da ake fama da shi a sauran sassan kasar. Kafin wannan Ojukwu na can yana faman yin waya don sanin abin da ake ciki daga Inyamurai ‘yan uwansa inda duk ya ji bayanin sai ya ji abin babu dadi, jin abubuwan da ke faruwa suka sanya ya samu ‘yan sanda ‘yan  asalin kabilar Inyamurai ya sanya su su kare masa iyalinsa. Ana cikin wannan sai kuma ga sarakunan Inyamurai wadanda suka je taron birnin Badun sun dawo da mummunan labarin ga kabilar Ibo suka ce musu an sace shugaban kasa Ironsi da kuma gwamnan jihar yamma Fajuyi kuma ban da Allah babu wanda ya san inda suke sai wadanda suka sace su.

Wannan bayanai ya kara rudar da Ojukwu wanda ya sanya ranar lahadi 31 ga watan Yuli ya sake kiran wani taron inda ya fada musu cewar Ogundipe daga Ikko ya fada masa cewar abin ya fi karfinsa kuma tun daganan da ya buga wayar Ogundipe sai ya ji babu wanda ya dauka daganan ya gane cewa lallai abin ya yi matukar baci. Daganan bai kara jin abin da ke faruwa a Ikko ba sai da Janar Gowon ya yi jawabi a cikin rediyo inda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

Da jin haka shi kuma Ojukwu ya ce sam wannan ba ta sabuwa don daga Ironsi babu wani wanda ya kamata ya karbi mulki illa Ogundipe watau ya manta da abin da Inyamurai suka yi wa Alhaji Dipcherima bayan kashe su Tafawa balewa. Kuma ya ce ya ji a lokacin da ana ta wannan dauki ba dadi sojojin arewa na cewa babu yadda za su yarda da tsagaita wuta sai an yanyanka Najeriya gunduwa-gunduwa sa’annan a kyale duk ‘yan kudu mazauna arewa su koma gida, haka su ma ‘yan arewa mazauna kudu. To amma kuma yadda aka yi ta yiwa mutanensu kisan kiyashi a kwanaki biyun da suka gabata ya nuna cewa babu yadda za mu iya zama a matsayin ‘yan kasa daya. Nan ma ya manta ba kisan gillar da Inyamurai suka yi wa su Sardauna. Wannan ya sanya ya fadawa shugaban soja cewar ya kamata a yi yarjejeniyar yadda kowa ya ke so ya zauna.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai